05/08/2024
Da safiyar yau Litinin:
Zanga zanga yayi sanadin kawo karshen Gwamnatin Malama Hasina Sheikh ta kasar Bangladesh wacce ta shafe shekaru 15 tana mulkin kasar (daga 2009 zuwa yau 2024).
~ Asalin zanga zangar ta faro ne ranar Asabar data gabata daga wasu 'daliban Jami'o'i da s**a fito domin yin zanga zangar Lumana da yin korafi akan Gwamnatin Sheikh Hasina cewa lallai tayi gyara akan tsarin daukan aiki da gudanarwar gwamnatin kasar, inda s**a ce Prime Ministan din taki sauraren korafin su.
Masu korafin sun fusata ne tun bayan da kotun kolin kasar tayi hukunci cewa ba za'a gyara tsarin daukan aiki da salon gudanar da gwamnatin ba.
~ Matasan sunce tsarin yana favoring Prime Minister din ce da kuma jam'iyyar ta da wadanda suke a hannun daman PM. Sun ce arzikin kasar wasu tsiraru ne ke wadaka dashi.
Zanga zangar ta b***e daga Student Protest ta koma ta gama gari washegari (jiya) Lahadi, inda tayi zafi sosai, hakan yasa Hasina Sheikh ta fice daga kasar cikin gaggawa a cikin jirgi Mai saukar Ungulu na sojojin kasar.
~ A yanzu haka sojoji ke rike da kasar. Rundunar Sojin kasar tace ta kame iko da fadar shugaban kasar kuma za'a kafa Gwamnatin rikon kwarya (Interim Government) nan da watanni kadan masu zuwa.
Hasina Sheikh 'yar shugaban kasar Bangladesh na farko ne wato Sheikh Mujibur Rahman wanda shine shugaban kasa na farko a kasar.
Hasina Sheikh ta taba yin mulkin kasar daga 1996 zuwa 2001, sai kuma daga 2009 zuwa 2024 yau Litinin data ajiye mulkin kasar ko kuma Sojoji s**a kifar da gwamnatin nata bayan korafin matasan kasar yayi yawa kan salon mulkin ta. -Barr Abdulhadee Isa Ibraheem