11/06/2026
MUNA BUKATAR SHUGABANNI CIKIN GAGGAWA – SAƘON GA MASU MULKI
Najeriya na fuskantar wani lokaci mai matukar wahala inda matsalolin tsaro, talauci da rashin tabbas s**a zama babban abin damuwa ga al’umma.
A yau, da dama daga cikin ’yan Najeriya na rayuwa cikin fargaba sakamakon hare-hare, garkuwa da mutane da kuma matsalolin tattalin arziki. Jama’a na ci gaba da tambayar: waye zai dauki alhakin wannan hali da ake ciki?
Masu bibiyar al’amura sun bayyana cewa shugabanci na gaskiya ba ya ginuwa kan bada uzuri ko dora laifi ga wasu, sai dai daukar alhaki tare da samar da mafita mai dorewa.
Sun jaddada cewa tsaro da jin dadin jama’a su ne ginshikin kowace gwamnati, kuma ya kamata a dauki matakan da s**a dace domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
A halin da ake ciki, iyalai na fuskantar bakin ciki, manoma na fuskantar matsaloli, kasuwanci na samun koma baya, yayin da matasa ke kara nuna damuwa kan makomar kasar.
Sakon da ake yadawa shi ne cewa Najeriya na bukatar shugabanni masu jajircewa, masu fuskantar gaskiya, masu daukar nauyi, kuma wadanda za su fifita rayuwar jama’a fiye da siyasa.
Ku saka mana Ra'ayin Ku a Kasa 👇👇
Voice Of Yola