
18/09/2025
Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da shirin gaggawa na kula da lafiyar jarirai a Jihar Kano
Hukumar Inshorar Lafiya ta Ƙasa (NHIA) ta kaddamar da wani sabon shiri na gaggawa domin rage mace-macen jarirai da ƙara samun damar kula da lafiyar jarirai a asibitocin gwamnati a faɗin ƙasar nan.
An kaddamar da wannan shirin ne a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano da ke jihar Kano, inda shugaban NHIA, Dr Kelechi Ohiri, ta ce shirin zai mayar da hankali kan jarirai da ke fuskantar matsalolin gaggawa bayan haihuwa.
Dr Ohiri, wadda Dr Salawudeen Sikiru ya wakilta, ya bayyana cewa shirin ya samo asali daga wani tsari na kulawa da lafiyar iyaye mata da aka fara fiye da shekara guda da ta gabata.
“Mun fara wannan shiri ne don rage mace-macen iyaye mata da jarirai. Matakin farko ya shafi uwa, yanzu kuma mun kaddamar da bangaren jarirai domin magance matsalolin gaggawa bayan haihuwa,” in ji shi.
Ya ce yanzu haka NHIA tana ɗaukar nauyin kuɗin magani ga jarirai a asibitocin gwamnati, inda asibitoci ke karɓar kudaden da s**a kashe a kowane mako bayan an tabbatar da bayanan jinya.
“Ayyukan da shirin ya ƙunsa sun haɗa da kula da jariran da aka haifa ba su gama girma ba, matsalolin rashin numfashi bayan haihuwa, rawayar ido da fata (jaundice), cutar jini (sepsis) da matsalolin tiyata ga jarirai,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa shirin ba zai tsaya kawai kan kulawar gaggawa ba, domin bayan an ceto jaririn za a yi masa rajista a kan inshorar lafiya ta ƙasa domin ya ci gaba da samun kulawa.
Shirin zai shafi iyalai marasa galihu ne kawai, tare da buƙatar lambar NIN domin tabbatar da sahihancin rajista.
A cewarsa, wannan matakin na farko zai gudana har zuwa shekarar 2027, tare da burin ganin kowane jariri mai buƙata ya samu kulawa a asibitocin da s**a shiga cikin shirin.
Shugaban Asibitin Koyarwa na Aminu Kano, Farfesa Abdulrahman Sheshe, ya yaba wa Gwamnatin Tarayya da NHIA bisa wannan mataki, yana mai cewa zai taimaka wajen rage mace-macen jarirai da kuma ƙara inganta ayyukan lafiya a manyan asibitoci.
Ya kuma yi kira ga gwamnati da ta ci gaba da ɗaukar nauyin irin waɗannan shirye-shirye na dogon lokaci, yana mai cewa su ne ginshikin tabbatar da tsarin kiwon lafiya da ya dace da bukatun ’yan ƙasa.