02/09/2026
GWAMNA FINTIRI YA JAGORANCI TARON MAJALISAR ZARTARWA TA JIHAR ADAMAWA KARO 13, YA AMINCE DA MUHIMMAN AIYUKA DA KUMA MANUFOFI MASU KYAU.
Gwamnan Jihar Adamawa, Rt. Hon. Ahmadu Umaru Fintiri, a yau ya jagoranci taron Majalisar Zartarwa ta Jihar Adamawa (EXCO) karo na 13, inda aka tattauna tare da amincewa da muhimman ayyuka da manufofi da dama.
Daga cikin ababen da aka amince dasu akai Waɗannan:
An amince da kwangilar gina sabbin gine-ginen ofisoshi na Hukumar Kula da Makarantun Sakandare ta Jihar Adamawa (Post Primary Management Board) kan jimillar kuɗi Naira biliyan 1.752.
An amince da kwangilar gina hanyoyin cikin makaranta, magudanan ruwa, kwalbatoci da sauran ayyukan more rayuwa a Babbar Makarantar Kimiyya da Fasaha (Mega Science and Technical Secondary School) da ke Hong, a Ƙaramar Hukumar Hong, kan kuɗi Naira miliyan 627,695,000.
Domin bunƙasa noma da noman rani, Majalisar ta amince da sayen buhuna 36,300 na takin zamani iri-iri domin noman rani, kan jimillar kuɗi Naira biliyan 2.198.
Haka kuma, Majalisar ta amince da ɗaukar wani kamfanin bada shawara domin gudanar da ayyukan shawarwari kafin da bayan gina Sansanin Yaƙi da Ta’addanci (Counter-Terrorism Base) da ake shirin ginawa a Gulak, Ƙaramar Hukumar Madagali, kan kuɗi Naira 381,655,781.24.
An kuma amince da sayen magungunan kashe ciyawa da kwari domin tallafa wa ayyukan noma a faɗin jihar, kan kuɗi Naira miliyan 759,280,000.
Bugu da ƙari, Majalisar ta tattauna tare da amincewa da takardar Ma’aikatar Albarkatun Ma’adinai ta jihar game da lasisin haƙar ma’adinai.
Waɗannan amincewar suna nuna ci gaba da jajircewar gwamnatin Gwamna Fintiri wajen inganta ababen more rayuwa, ilimi, noma, tsaro da kuma ɓangaren albarkatun ma’adinai, domin tabbatar da ci gaba mai ɗorewa a Jihar Adamawa.
📸 Thomas Terry
📍 Vandi Yusuf Mai Ba Gwamna Shawara na Musamman kan Yaɗa Labarai.
Fassara: Muhammad Mahdi Hamisu
02/09/2026