
14/07/2025
Gwamna Dikko Radda ya iso Birnin Katsina don shirin jana’izar marigayi tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya dawo gida Katsina domin jagorantar shirye-shiryen jana’izar tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, wanda ya rasu jiya a wani asibiti a ƙasar Birtaniya.
An tarbi Gwamnan ta hannun manyan jami’an gwamnati na jihar, ciki har da Sakatare na Musamman a Ofishin Gwamna, Hon. Abdullahi Aliyu Turaji.
Ana ci gaba da gudanar da shirye-shiryen jana’izar marigayin da kuma tsare-tsaren taron girmamawa.