Arewa Vision Media AVM

Arewa Vision Media AVM Zamu kawo muku labarai masu inganci daga Najeriya da ko'ina cikin duniya. Ku kasance masu samun labarai da Ɗumi-Ɗuminta tare da Arewa Vision Media AVM.

01/09/2026

Ɗan shiyar Arewacin Najeriya baida dalilin zaɓar Mr Peter Obi a matsayin shugaban kasa, ko shin menene dalili?
Saurari zantawa da mukayi da Alhaji Hussaini Gambo Bello Na Kura....

01/09/2026

Ko shin wani irin cikas masu sana'ar saye da sayar da man fetur ke fiskanta a jihar Adamawa?
Saurari wannan zantawa da mukayi da Isa Bapetel (Isa Ataimaka)...

AUN Schools Faces Concerns Over Rising Fees, Teaching Quality and Student WelfareYOLA - AUN Schools is facing growing co...
28/08/2026

AUN Schools Faces Concerns Over Rising Fees, Teaching Quality and Student Welfare

YOLA - AUN Schools is facing growing concerns over its increasing school fees and alleged decline in educational standards, infrastructure and student welfare.

The concerns include the continuous increase in annual fees, which are reported to exceed *₦2 million* per child, despite persistent challenges affecting students and parents.

Issues reported include unreliable electricity and air conditioning in classrooms and the school clinic, shortage of experienced teachers, frequent teacher absenteeism, inadequate textbooks, unmarked assignments, declining academic performance, concerns over food and access to drinking water, poor toilet facilities and inadequate response to students complaints.

There are also concerns over reports of *weak* performance in Mathematics among SS3 students during mock examinations, raising questions about their preparedness for WAEC, JAMB and other external examinations.

The school’s recently introduced fee payment policy has also generated concerns, particularly the requirement for fees to be paid one month before resumption, a ₦1,000 daily late payment penalty, and restrictions on students resumption until outstanding fees and penalties are fully settled.

Other issues include the reported departure of experienced teachers, additional administrative responsibilities assigned to some teaching staff, limited participation in external academic competitions, discontinuation of student teacher evaluation forms and concerns surrounding prize money reportedly won by students at a competition in Abuja.

Concerns have further been raised over additional charges for school activities and graduation events, with parents questioning why such expenses are not incorporated into the main school fees.

Several of the issues reportedly date back to concerns raised during a parents meeting in 2022, including teaching quality, textbooks, school fees, transport services, security, communication and student welfare.

Further findings by newsmen also indicate that, despite the more than ₦2 million in annual fees reportedly paid by parents for each child, the school management has no significant humanitarian or community support activities targeted at the surrounding community.

The concerns are said to be contributing to declining confidence among some long standing parents, with reports that some families have withdrawn their children while others have decided against enrolling their younger children.

The situation has raised questions about accountability, value for money and whether the current level of educational and welfare services is commensurate with the financial obligations placed on parents.

All efforts by newsmen to obtain the reaction of the school management proved abortive, as the Interim Director of the school was absent when journalists visited. Her deputy, however, through the school security guard indicated that the management would be able to comment on the matter after the school resumes.

28/08/2026

Yadda gangamin sauya sheka da tsohon gomnan jihar Adamawa Senator Bindow Umaru Jibirilla da magoya bayansa mutum dubu goma ya kasance daga jam'iyyar ADC zuwa APC a birnin Yola.

DAMARE YA BA MASU GOYON BAYAN BABA TEN SU BIYAR ƘARIN JARIN MILIYAN ₦2.5A wani mataki na ƙarfafawa, nuna godiya da talla...
21/08/2026

DAMARE YA BA MASU GOYON BAYAN BABA TEN SU BIYAR ƘARIN JARIN MILIYAN ₦2.5

A wani mataki na ƙarfafawa, nuna godiya da tallafa wa matasan da s**a ci gaba da kasancewa masu aminci da jajircewa wajen tafiyar siyasar Hon. Ibrahim Babayola Mustapha (Baba Ten), an bai wa mutane biyar tallafin kuɗi na jimillar ₦2.5 miliyan.

Ga sunayen waɗanda s**a amfana:

Abdulrasheed Babale — ₦500,000
Bashiru Mohammed — ₦500,000
Mauludu Abbajo — ₦500,000
Kabiru Turaki — ₦500,000
Sahabo PTF — ₦500,000

Alhaji Ahmed Usman Damare, Manajan Top 10 Plaza da ke Yola, kuma Mataimaki na Musamman ga Hon. Ibrahim Babayola Mustapha, ɗan takarar jam’iyyar ADC na kujerar Sanatan Adamawa ta Tsakiya, ne ya jagoranci wannan tallafi.

Manufar wannan tallafi ita ce nuna godiya ga waɗanda s**a kasance masu jajircewa da aminci, ƙarfafa musu gwiwa su ci gaba da kasancewa cikin tafiyar, tare da taimaka musu wajen bunƙasa sana’o’insu da ƙara jarin gudanar da harkokinsu.

Alhaji Damare ya ci gaba da nuna cewa shugabanci ba magana kawai ba ce, illa kuma gano mutanen da ke buƙatar tallafi da kuma miƙa musu hannu domin taimaka musu. Irin waɗannan ayyukansa, musamman wajen tallafa wa ƙoƙarin jinƙai da shirye shiryen ƙarfafa al’umma na jagoransa, sun ci gaba da sanya matasa da magoya baya ganin darajarsa.

A ɓangaren Hon. Baba Ten kuwa, wannan tallafi ya ƙara nuna ruhin gina mutane, ƙarfafa al’umma da kuma saka hannun jari wajen bunƙasa rayuwar waɗanda s**a yi imani da manufofin siyasar ɗan takarar Sanatan Adamawa ta Tsakiya.

Yayin da shekarar 2027 ke ƙara matsowa, irin waɗannan matakai na ci gaba da nuna muhimmancin hulɗa da jama’a a matakin ƙasa, ƙarfafa matasa da kuma bayar da tallafi na gaskiya ga mutanen da s**a ci gaba da kasancewa masu aminci ga burin siyasar da s**a yi imani da shi.

21/08/2026

Alhaji Babayola Mustafa Baba 10 yana ci gaba da samun karɓuwa tsakanin matasas Adamawa ta tsakiya.

KU KYALE ABDULRAHMAN HASKE. Cewar Hussaini Ahmadu HarWanda ya kafa ƙungiyar Fight to Finish Forum 2027, kuma Tafidan Dau...
20/08/2026

KU KYALE ABDULRAHMAN HASKE.

Cewar Hussaini Ahmadu Har

Wanda ya kafa ƙungiyar Fight to Finish Forum 2027, kuma Tafidan Daulan Adamawa, Hon. Hussaini Ahmadu Har, ya yi kira ga mutanen da ke s**ar matakin siyasar Abdulrahman Haske da su daina ba shi shawarwarin da bai nema ba, su bar shi ya yi amfani da haƙƙinsa na kundin tsarin mulki wajen yanke shawarar siyasar da ya ga ta dace da shi.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Hon. Hussaini ya ce hankalinsa ya karkata kan wasu jerin kalamai da wasu matasa ke yi dangane da rahotannin cewa Abdulrahman Haske na shirin ficewa daga jam’iyyar APC.

Ya bayyana irin waɗannan s**ar a matsayin abin da ba dole ba, yana mai cewa Haske, a matsayinsa na ɗan Najeriya, yana da cikakken haƙƙin yin zaɓe da kuma tsayawa takarar wani muƙamin siyasa a ƙarƙashin kowace jam’iyyar siyasa da ya zaɓa.

A cewarsa, Abdulrahman ya shiga APC ne domin ya yi amfani da wannan haƙƙi tare da bayar da gudunmawa wajen ci gaban jam’iyyar, amma tsarin, musamman zaɓen fidda gwani na jam’iyyar, ya gaza samar masa da abin da ya kira dama mai inganci ta lashe tikitin jam’iyyar gabanin babban zaɓen 2027.

Hon. Hussaini ya ƙara da cewa Abdulrahman Haske baligi ne, mai ilimi, kuma wanda ya samu gogewa da sanin ya kamata ta hanyar tafiye tafiye da hulɗa da al’umma, don haka yana da cikakkiyar damar yanke shawarar siyasa bisa fahimtarsa da abin da ya yi imani da shi.

Ya ce duk da abin da ya bayyana a matsayin gazawar APC wajen bai wa Haske damar siyasa ta gaskiya, tsohon ɗan takarar na ci gaba da samun gagarumin goyon bayan siyasa daga sassa daban-daban na al’umma.

Hussaini ya danganta tasirin siyasar Haske da irin goyon bayan da yake samu daga mutane masu bambancin jam’iyyun siyasa, shekaru, ƙabilu da kuma rukunin al’umma daban daban.

Haka kuma, ya yi watsi da zargin cewa mutanen da ke goyon bayan burin siyasar Haske suna yin hakan ne kawai saboda suna fatan samun wata moriya daga gare shi.

Ya ƙalubalanci masu yin irin waɗannan zarge zarge da su yi amfani da ma’auni guda wajen kallon nasu zaɓin siyasa, yana tambayar ko mutanen da ke goyon bayan wasu ƴan takara da ake zargin an ɗora su daga manyan jami’an jam’iyya ba sa yin hakan ne saboda wani buri ko tsammanin wata moriyar siyasa ko ta kashin kai.

Hussaini ya kuma yi kira ga shugabannin APC a jihar Adamawa da su mai da hankali wajen magance matsalolin da ya bayyana a matsayin rashin demokradiyyar cikin gida, zargin ɗora ƴan takara da kuma rashin ingantaccen jagoranci, yana gargadin cewa irin waɗannan matsaloli na iya yin illa ga jam’iyyar gabanin zaɓen 2027.

Saboda haka, ya roƙi masu s**ar Abdulrahman Haske da su karkatar da hankalinsu wajen magance matsalolin da ke cikin APC maimakon ƙoƙarin tilasta masa irin matakin siyasar da ya kamata ya ɗauka.

Ya ce: “A Kyale Abdulrahman ya tsaya takara a ƙarƙashin kowace jam’iyyar siyasa da ya zaɓa.”

Hussaini ya jaddada cewa Haske ya kamata ya samu ƴancin bin burinsa na siyasa ba tare da la’akari da sakamakon da zai iya samu ba.

Ya kuma yi tsokaci kan ƙuri’u 65,424 da aka ce an bai wa Haske a lokacin zaɓen fidda gwani na APC, yana mai zargin cewa tsarin zaɓen bai kasance cikin gaskiya da sahihanci ba.

Hon. Hussaini Ahmadu Har, wanda ya sanya hannu kan sanarwar a matsayin shi na Tafidan Daulan Adamawa kuma wanda ya kafa Fight to Finish Forum 2027, ya ce abin da ya kamata a fi mayar da hankali a kai shi ne ƙarfafa tsarin dimokuraɗiyya da kuma mutunta zaɓin siyasar kowane ɗan takara gabanin babban zaɓen 2027.

19/08/2026

Sakon Hon. Hussaini Ahmadu Har akan Abdullahi Bashir Haske sabon Sarkin Fulani Adamawa.

THE MAKING OF THE FIRST SARKIN FULANI ADAMAWA FOMBINA KINGDOM!Abdullahi Bashir-Haske is a Nigerian businessman who is de...
18/08/2026

THE MAKING OF THE FIRST SARKIN FULANI ADAMAWA FOMBINA KINGDOM!

Abdullahi Bashir-Haske is a Nigerian businessman who is determined, respectful, and forward-thinking individual who values personal growth, integrity, and meaningful relationships.

He is someone who strives to approach life with a positive mindset and a strong sense of responsibility.

He is passionate about learning, developing his abilities, and creating opportunities for a successful future, not only for himself but everyone around him.

He believes that dedication, discipline, and perseverance are important qualities for achieving both personal and professional goals.

He is also committed to treating others with kindness and respect and values honesty and good character.

With a willingness to learn from experience and face challenges with confidence, Abdullahi Chiroman Ganye continues to work toward becoming a better version of himself.

His ambition, commitment, and desire for continuous improvement are qualities that can help him make a positive contribution to his community and to the people around him.

Abdullahi Bashir Haske is the founder and group managing director of AA&R Investment Group, a conglomerate with interests in oil and gas, agriculture, information and communication technology, aviation, marine services and logistics.

His company, Etihad Oilfield Services is credited for discovering oil in the Kolmani River area in Bauchi State. Haske holds the traditional title of "Ciroma-Ganye of Adamawa" in recognition of his business and social impact in his home state of Adamawa.

BUSINESS CAREER

Haske began his business career in 2005 offering general contracting services to private and public organizations and trading in agro-commodities and petroleum products. He later established AA&R Investment Group – a conglomerate with several subsidiaries in diversified industries including agriculture, oil and gas, logistics, aviation, marine services and ICT. His company, Manomi Support Services Limited, a community based agricultural production firm manages 15,000 hectares of land across several Nigerian states with over 2,000 employees.

His H & W Rice Company Limited, an integrated rice miller is one of the largest millers in northern Nigeria with an annual production of 48,000 tons of paddy.

Haske is known mainly in the Nigeria oil and gas industry with diversified investments in upstream and downstream sectors with several companies including Mars Exploration and Production Limited, an indigenous exploration and production, and Etihad Oilfield Services Limited. Etihad Oilfield Services is known for its role in the discovery of oil and gas in commercial quantity in the Kolmani River area around Bauchi and Gombe states in the north east of Nigeria.

Haske is reported to own 51% stakes in four oil blocks which include OML 123, OML 124, OML 126, and OML 137.

With this background, I believe the Adamawa Emirate Council have hit the bullseye by giving honours to whom it is due by conferring the traditional title of SARKIN FULANI ADAMAWA to Abdullahi Bashir Haske, a gesture which received a commendation from all and sundry thereby cementing the robust relationship between Adamawa Emirate and Ganye Chiefdom where he currently hold the title of Chiroma.

Hon. Hussaini Ahmadu Har

Tafidan Daulan Yola.
Director Media & Publicity Adamawa APC UNITY FORUM.
Coordinator City Boy Movement Yola South.
Founder Fight To Finish 2027.

Jam'iyyar ADC a jihar Adamawa ta dakatar da Barrister Sadiq Ɗasin a matsayin shugaban ta inda nan take ta maye gurbin sh...
17/08/2026

Jam'iyyar ADC a jihar Adamawa ta dakatar da Barrister Sadiq Ɗasin a matsayin shugaban ta inda nan take ta maye gurbin shi da Alhaji Sa'idu Naira a matsayin shugaban riko.

Address

Yola

Telephone

+2347061658047

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Arewa Vision Media AVM posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Arewa Vision Media AVM:

Shortcuts

Share