Real Luqman

Real Luqman I'm Facebook Technician | Content Creator
Helping you troubleshoot and resolve Facebook issues. Follow for tips, guides, and expert advice.
(363)

Today or tomorrow might be the last day of your life story in this worldly life. Are you ready for Dead? Have done a goo...
28/07/2025

Today or tomorrow might be the last day of your life story in this worldly life. Are you ready for Dead? Have done a good deed for meeting your Lord ?

It's not a bad things to rewrite your story ✈️💝
28/07/2025

It's not a bad things to rewrite your story ✈️💝

SHIN KA IYA SALLAH GAWA ?To bari in bayyana mataki-mataki yadda ake gudanar da Sallar Gawa (Salatul Janazah) a Musulunci...
29/06/2025

SHIN KA IYA SALLAH GAWA ?

To bari in bayyana mataki-mataki yadda ake gudanar da Sallar Gawa (Salatul Janazah) a Musulunci. Wannan salla tana da sauki amma tana bukatar fahimta da tsabta da niyya.



***YADDA AKE SALLAR GAWA (SALATUL JANAZAH)

✅ Sharuɗɗan Sallar Janaza:

1. Gawa ta zama Musulmi.

2. A wanke ta, a nade da likkafani.

3. A shimfiɗa gawa a gaban masu salla.

4. Jama’a su tsaya cikin layi (ba ruku’u, ba sujada).

5. A yi niyya.

**** Matakan Sallar Gawa:

1. Niyya (a zuciya):
“Zan yi sallar janaza ga wannan mamaci domin Allah.”
(Ba a furta niyya da baki).

2. Takbira na Farko:

Ka ce “Allahu Akbar”

Ka karanta Fatiha (Bismillah har zuwa Walad-daallin. Ameen ba dole ba)

3. Takbira na Biyu:

Ka ce “Allahu Akbar”

Ka karanta Salati ga Annabi (SAW):
“Allahumma salli ala Muhammadin wa ala aali Muhammadin...”

4. Takbira na Uku:

Ka ce “Allahu Akbar”

Ka yi addu’a ga mamaci, kamar:
“Allahummaghfir lahu warhamhu wa ‘aafihi wa’fu anhu...”
(In mamaci mace ne: laha maimakon lahu)

5. Takbira na Hudu:

Ka ce “Allahu Akbar”

Ka yi addu’ar karshe, kamar:
“Allahumma la tahrimna ajrahu wa la taftinna ba’dahu...”

6. Sallama:

Ka ce “Assalamu Alaikum wa Rahmatullah” (sau ɗaya, a dama kawai ko dama da hagu).

📝 Lura:

Ba a yin ruku’u ko sujada.

Ana yin sallar ne da tsaye idan mutum na da lafiya.

Za a iya yin sallar mutum ɗaya ko da jama’a ba su da yawa.

First batch of Adamawa State pilgrims arrived YOLA safely.
27/06/2025

First batch of Adamawa State pilgrims arrived YOLA safely.

24/06/2025
show one love for my beloved country
19/06/2025

show one love for my beloved country

Hudubar Bankwana Mai Ratsa Zuciya Da Annabi SAW Ya Yi A Irin Wannan Rana Ta Yau (Arfa):A irin wannan ranar ce ( 9 ga wat...
05/06/2025

Hudubar Bankwana Mai Ratsa Zuciya Da Annabi SAW Ya Yi A Irin Wannan Rana Ta Yau (Arfa):

A irin wannan ranar ce ( 9 ga watan Zul-Hijjah ) SHEKARA ta goma bayan Hijira a Dutsen Arafat (ranar Arfa kenan) Annabi Muhammad S.A.W ya yi wata huduba mai ratsa zuciya.

Fiyayyen Halitta (S.A.W) Ya fara da cewa:

“Ya ku mutane ku ba ni hankalinku, domin mai yiwuwa ba zan sake kasancewa da ku bayan wannan shekarar ba, saboda haka ku saurari abinda nake gaya maku da kyau, kuma (ku isar da abinda zan gaya maku) ga wadanda ba su a wannan wuri a yau.

1⃣

Ya ku mutane kamar yadda ku ka ri'ki wannan wata, (na Hajji) da wannan rana (ta Arfa) da kuma wannan gari (na Makka) da girma kuma abin tsarewa, to, haka kuma ku riki ran Musulmi da kuma dukiyoyinsu da girma abin kuma karewa, ku maida wa mutane kayan da s**a ba ku amana. Kar ku cuci kowa, saboda kar wasu su cuce ku.

2⃣

Ku tuna fa, hakika Allah zai yi sakayya akan ayukakanku. Allah (SWT) ya hana cin riba,(wato kudin ruwa) saboda haka, duk abin
da aka kulla ta kudin ruwa sai an warware shi. Ku yi hattara da shaidan, domin kiyaye addininku. Yanzu kan ya fidda ran batar da ku akan manyan abubuwa (na sabo) saboda haka ku guji binshi akan kanana.

3⃣

Ya ku jama'a hakika kuna da hakki bisa matayenku, amma su ma suna da hakki bisa kanku, to hakkin su ne akan ku da kuciyar da su,
Kuma ku tufatar da su akan jin kai. ku bi da su kyakkyawan biyarwa. Ku kuma tausasa musu domin su majibintan al'amurran ku ne, kuma mataimakan ku, Hakki ne akan su da kar su yi abota da duk wanda ba ku so, kuma su nisanci zina.

4⃣

Ya ku jama'a, ku yi kyakkyawar bauta ga Allah (SWT) ku tsaida salloli biyar (5) na farilla, Ku azumci watan Ramadan, kuma ku bada zakka. Ku aikata aikin Hajji idan har kun samu damar yi.

5⃣

Ku sani fa, kowane musulmi dan uwan musulmi ne. Dukkan ku daidai ku ke. Ba wanda yake da fifiko saman wani sai wajen tsoron Allah da aikata kyawawan ayyukka.

6⃣

Ku tuna fa (ya ku jama'a) wata rana za ku tsaya gaban Ubangijinku, domin sakamakon ayyukanku,saboda haka ku yi hattara kada ku yi sake da hanya madaidaiciya bayan na kau.

7⃣

Ya ku jama'a ba wani annabi ko manzo da zai zo bayana kuma babu wani addini da zai zo (bayan addinin musulunci), saboda haka ku yi
tunani sosai akan wannan magana da na gaya maku, kuma ku fahimce ta (sosai).

8⃣

Zan bar maku abubuwa guda biyu (2); (Alkurani) da kuma (Sunnah). Idan kun bi wannan ba za ku taba bata ba.

Duk wanda ya ji wannan sako to ya jiyar da wadansu, su ma su jiyar da wasunsu, kuma sau da yawa wadanda za su ji maganata daga karshe su fi masu ji na yanzu fahimtar abinda nake fada.

9⃣

Ya Allah... ka zamo shaida a gare ni, cewa na isar da aikenka zuwa ga bayinka.”

Allah yasa mudace Amin.

Sheikh Dr. Saleh bin Abdullah Bin Humaid, the Imam and Khateeb of Masjid Al Haram, will deliver the Arafah sermon for th...
30/05/2025

Sheikh Dr. Saleh bin Abdullah Bin Humaid, the Imam and Khateeb of Masjid Al Haram, will deliver the Arafah sermon for this year’s Hajj, 1446 AH at Masjid Nameira.

Address

Yola

Opening Hours

Monday 09:00 - 17:00
Tuesday 09:00 - 17:00
Wednesday 09:00 - 17:00
Thursday 09:00 - 17:00
Friday 09:00 - 17:00

Telephone

+2347067677403

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Real Luqman posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Real Luqman:

Share

Category