28/05/2025
                                            Wasu Daga Cikin Falalar Goman Farko Na Watan Zulhijja
..jama'a mu yada (sharing) wannan sako domin amfanar sauran jama'a
1) Allah Ya yi rantsuwa da su a cikin alQurani. Qur'an 89:2.
2) Sune Ayyamun Ma'alumat da Allah ya umurci ayi ambaton sa a ciki a suratul Hajj Qur'an 22:  28.
3) Aiki a cikin su yafi falala da lada da soyuwa ga Allah akan duk sauran kwanakin shekara. Bukhari no.926.
4) Ana so a yawaita Subhanallah, Walhamdulilllah, wallahu Akbar wa Lailaha illallah da karatun al-Qurani. Bukhari ya ruwaito.
5) Ana so a bayyana ambaton Allah a ciki domin a tunawa wanda yamanta. Abdullahi Ibn Umar da Abu-Hurairah sun kasance suna shiga kasuwa suna kabbara jamaa na kabbara da kabbarar su. Bukhari ya ruwaito .
6) Aikin Hajji yana cikin Ayukka mafi falala a cikin wadanna kwanaki.
7) Annabi S.A.W ya kasance yana azumin kwanaki tara na farkon Zulhijja. Ahmad da Abu-Dawud da Nasai s**a ruwaito . Albani ya inganta a Sahihi Sunani Abi-Dawud 2106.
8) Azumin ranar Arafah yana kankare zunuban shekarar da ta wuce da wadda za ta zo. Muslim 1162.
9) Idan kwanakin goma s**a shigo wanda keda niyyar layya ba zai cire gashi ko kumba a jikin sa ba. Muslim ya ruwaito.