True Love never end.

True Love never end. I talk about what's love,but no hurry in life&everythings has own time!!!

03/09/2026

TIRKASHI: Kai da ka kasa rage farashin ruwan FARO ne kake alkawarin rage farashin man fetur? — Dr. Sani Ahmad Zangina ya caccaki Atiku

Dr. Sani Ahmad Zangina ya ƙalubalanci Atiku Abubakar kan alkawarin rage farashin man fetur, yana mai cewa ya kamata ya fara da rage farashin ruwan FARO da kamfaninsa ke samarwa.

Dr. Sani Ahmad Zangina ya caccaki tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, kan alkawuran da yake yi wa ’yan Najeriya na rage farashin man fetur da kuma batun tallafin mai gabanin zaɓen 2027.

Zangina ya ce idan har Atiku na son tallafa wa talakawa da rage musu radadin tsadar rayuwa, ya kamata ya fara daga kamfaninsa ta hanyar rage farashin ruwan sha na FARO da sauran kayayyakin da kamfanin ke samarwa.

A cewar Zangina, ruwan FARO da talakawa ke amfani da shi a kullum ya yi tsada, duk da cewa kamfanin na cikin harkokin kasuwancin Atiku.

Ya ce abin mamaki ne mutum ya kasa rage farashin ruwan sha da talakawa ke saya a kullum, amma a lokaci guda yana yi wa ’yan Najeriya alkawarin rage farashin man fetur daga N145 zuwa N90.

“Kai da ka kasa rage farashin ruwan FARO ne kake alkawarin rage farashin man fetur ga sama da ’yan Najeriya miliyan 200?” in ji Zangina.

Zangina ya kuma ce ya kamata ’yan Najeriya su tuna da irin alkawuran da ’yan siyasa ke yi a lokacin neman zaɓe, yana mai kira ga Atiku da ya daina, a cewarsa, yaudarar ’yan Najeriya da alkawuran da ba za su cika ba domin samun nasara a zaɓen 2027.

Ya ƙara da cewa “alheri yana farawa ne daga gida”, yana mai cewa idan ba a iya sauƙaƙa wa talakawa farashin abin da ake samarwa a kamfani ba, to akwai tambaya kan yadda za a iya aiwatar da irin wannan tsari a faɗin ƙasa.

02/09/2026
02/09/2026

Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) ta ce tattalin arzikin Najeriya ya samu ci gaba da kashi 4.43 cikin 100 daga watan Afrilu zuwa Yuni na shekarar 2026.

Shin a matsayinka na ɗan Najeriya, ka ga alamar wannan ci-gaban a rayuwarka ta yau da kullum?

02/09/2026

Kafito Kayimana Bayani akan karatun ka, Muna da Shakku akai -Piter Oba ya kalubalanci Tunibu.

02/09/2026

Duk wanda yake tunanin zamuci zabe cikin ruwan sanyi yaudarar kansa yake inji Gov Dikko Umar Radda

02/09/2026

FBI ta tabbatar da binciken Tinubu kan safarar miyagun ƙwayoyi

Hukumar Binciken Manyan Laifuka ta Amurka (FBI) ta tabbatar da cewa an taɓa gudanar da binciken laifi kan Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, dangane da zargin safarar miyagun ƙwayoyi a farkon shekarun 1990.

FBI ta bayyana hakan ne a wata rantsacciyar takarda da ta gabatar wa wata kotun tarayya a Amurka a ranar 28 ga Agusta, 2026, a wani shari’ar da ake yi ƙarƙashin dokar ’Yancin Samun Bayanai (FOIA), inda ake neman samun wasu takardun hukumar da s**a shafi Tinubu.

A cikin takardar, FBI ta ce bayanan da ake magana a kansu “an tattara su ne domin gudanar da binciken hukumar kan wasu mutane da dama dangane da laifukan safarar miyagun ƙwayoyi”.

Hukumar ta kuma ce kotun ta riga ta tabbatar da cewa an taɓa samun sahihin bayani a hukumance kan gudanar da bincike game da Bola Tinubu.

Matakin na baya-bayan nan ya biyo bayan hukuncin da Alƙaliyar Kotun Gundumar Amurka, Beryl Howell, ta yanke a watan Afrilun 2025, inda ta ce FBI da Hukumar Yaƙi da Miyagun Ƙwayoyi ta Amurka (DEA) ba za su ƙara amfani da tsarin da ake kira “Glomar response” wajen ƙin tabbatarwa ko musanta wanzuwar takardun binciken Tinubu ba.

Alƙaliyar ta ce hukumomin sun gaza gabatar da isassun dalilai na kare haƙƙin sirrin Tinubu da za su ba su damar ɓoye gaskiyar cewa an taɓa gudanar da binciken laifi a kansa.

Sai dai hukuncin kotun bai tabbatar da cewa Tinubu ya aikata laifin safarar miyagun ƙwayoyi ko kuma an taɓa yanke masa hukuncin wani laifi ba.

Binciken da ake magana a kai ya samo asali ne daga buƙatun bayanai da wani Ba’amurke mai fafutukar neman gaskiya, Aaron Greenspan, ya shigar ƙarƙashin dokar FOIA.

Daga cikin bayanan da Greenspan ke nema akwai “cikakken fayil ɗin FBI na Bola Ahmed Tinubu” da kuma bayanan tambayoyin da jami’an FBI s**a yi da Tinubu tsakanin shekarun 1992 da 1993, ƙarƙashin shari’ar mai lamba 245-IP-71386-UUUUUU.

Buƙatun Greenspan na daga cikin wani yunƙuri mai faɗi na samun takardun bincike da s**a shafi wata hanyar safarar hodar he**in da aka gudanar a Chicago a farkon shekarun 1990.

FBI ta ci gaba da hana fitar da wasu sassan takardun, tana mai dogaro da wasu tanade-tanaden dokar FOIA da s**a shafi kare sirrin mutum, majiyoyin bayanan sirri, dabarun jami’an tsaro wajen gudanar da bincike da kuma bayanan da fallasa su ka iya jefa wasu mutane cikin haɗari.

Hukumar ta ce ba za ta iya bayyana cikakken dalilin da ya sa ta dogara da wasu daga cikin waɗannan tanade-tanaden ba.

Kamfanin da Atiku ya ɗauka ya wallafa takardar FBI
Kamfanin Von Batten-Montague-York, wani kamfanin hulɗa da gwamnati da ke Washington, wanda tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya ɗauka gabanin zaɓen shugaban ƙasa na 2027, ne ya wallafa wasu sassan takardar FBI.

Kamfanin ya bayyana a shafinsa na X cewa yana nazarin dimbin takardun da ya karɓa daga FBI, tare da cire wasu sassan da ake ganin ya kamata a kiyaye.

Kamfanin ya ce ya wallafa takardar ne domin ƙaryara iƙirarin cewa ba a taɓa gudanar da binciken laifi kan Tinubu ba.

Ya ce takardar ta nuna cewa FBI ta tabbatar a bisa rantsuwa cewa kotu ta riga ta tabbatar da cewa an taɓa amincewa a hukumance da gudanar da binciken laifi kan shugaban na Najeriya.

Fadar Shugaban Ƙasa ta mayar da martani
Sai dai Mai ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Yaɗa Labarai da Sadarwa, Sunday Dare, ya yi watsi da iƙirarin da ake yaɗawa game da takardun FBI, yana mai cewa siyasa ce ta jawo batun.

Dare ya zargi Atiku da amfani da wani kamfanin hulɗa da gwamnati da ke Washington wajen ƙoƙarin haifar da ce-ce-ku-ce gabanin zaɓen 2027.

Ya bayyana yaɗa bayanan a matsayin wata kutungwilar siyasa, yana mai cewa takardun da ake yaɗawa ba su kasance wani sabon rahoton leƙen asiri ba.

Dare ya kuma yi tambaya kan sahihancin bayanan da kamfanin ke fitarwa, yana mai cewa bai kamata a ɗauki kalamansa a matsayin na gwamnatin Amurka ba.

Ya buƙaci masu yin zarge-zargen da su gabatar da hujjoji kan iƙirarin da suke yi, musamman waɗanda s**a shafi bayanan leƙen asiri na sirri.

Dare ya kuma ce bayanan da ake samu a fili daga takardun Ma’aikatar Shari’a ta Amurka da s**a shafi dokar rajistar wakilan ƙasashen waje (FARA) sun nuna cewa Atiku ya ɗauki kamfanin Von Batten-Montague-York kan kwangilar dala miliyan 1.2 na tsawon watanni 12.

A cewarsa, an ɗauki kamfanin ne domin ya taimaka wajen “daidaita” bayanan da gwamnatin Najeriya ke fitarwa tare da amfani da tsoffin bayanan kotunan Amurka wajen samun shiga a harkokin siyasa gabanin zaɓen 2027.

Dare ya kuma yi watsi da duk wata alaƙa tsakanin tafiyar Tinubu zuwa Turai da shari’ar FOIA, yana mai cewa shugaban yana hutun shekara-shekara ne da tun ba yanzu ba aka tsara.

Ya ce babu wata alaƙa tsakanin hutun shugaban a Turai da shari’ar da ake yi a kotun Amurka.

Dare ya kuma ambato lauyan Tinubu, Wole Afolabi, SAN, wanda ya yi bayani kan shari’ar a gidan talabijin na Channels, inda ya ce yunƙurin hana fitar da wasu sassan takardun yana da nasaba ne da dokokin Amurka da ke kare sirrin bayanan binciken jami’an tsaro.

A cewar Dare, Afolabi ya kuma ce da a ce Tinubu ya aikata wani laifi da ya sa ya zama abin hukunci a ƙarƙashin dokar Amurka, da hukumomin ƙasar sun gurfanar da shi a lokacin.

Dare ya zargi ’yan adawa da mayar da hankali kan tsoffin takardun Amurka maimakon gabatar wa ’yan Najeriya da cikakkun manufofin tattalin arziki da sauran shirye-shiryen da za su aiwatar idan s**a samu mulki a 2027.

Ya ce ya kamata zaɓen ya ta’allaƙa ne kan yadda ’yan siyasa s**a gudanar da mulki da kuma manufofinsu, ba wai ce-ce-ku-ce da ya shafi tsoffin bayanan binciken hukumomin ƙasar waje ba.

A halin yanzu, lauyoyin Tinubu na adawa da fitar da wasu ƙarin takardun, inda s**a ce sakin wasu bayanan sirri da ke cikin taskar gwamnati zai keta haƙƙin shugaban na sirri.

02/09/2026

Hukumar Binciken Laifuka ta Amurka FBI ta taba tuhumar Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan zanrgin safarar miyagun kwayoyi a shekarun baya.

Hello fans, Welcome to September month with hope and faithfulness,I pray God will guide us through this month, bless , g...
02/09/2026

Hello fans, Welcome to September month with hope and faithfulness,I pray God will guide us through this month, bless , grace, peacefully be successful says true love never end💞🥀🎉🥂🙏

Address

Michika L. G. A
Yola

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when True Love never end. posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share