Citizenship HAUSA

  • Home
  • Citizenship HAUSA

Citizenship HAUSA Takenmu: 'Yanci, Adalci, Cigaba...
(2)

Manufarmu ita ce wayar da kan jama’a kan hakkin ɗan ƙasa da nauyin da ke kansa, da kuma yadda za a rayu cikin zaman lafiya, adalci da haɗin kai a cikin al’umma tare da yadda zai samu cigaba da nasara a rayuwarsa.

15/07/2025

"Da ka karɓi haƙƙinka da ka yafe, wanne ne yafi? Kayi yafiya shi yafi har a wajen Allah"

Sheikh Dr. Ahmad Bamba

Tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, ya rasu jiya.A wannan lokaci na rabuwa da shi, muna roƙon al’umma da su yafe mas...
14/07/2025

Tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, ya rasu jiya.

A wannan lokaci na rabuwa da shi, muna roƙon al’umma da su yafe masa, su ɗauki kyawawan ayyukansa, su kuma yi masa addu’a. Duk wanda ya jagoranci mutane, ba ya rasa kura-kurai. Mu roƙi Allah Ya karɓi na alkhairi, Ya gafarta masa na kuskure, Ya sa kabarinsa ya kasance cikin haske da rahama.

Allah Ya ba iyalansa haƙuri da juriya. Ya karɓe Buhari da rahama. Ya jikansa da rahama.

Mace tagari ba ta neman PAKACITY 😃 tana neman amintacce da mai kula da ita da gaskiya.A takaice dai ita Tagari mai CAPAC...
12/07/2025

Mace tagari ba ta neman PAKACITY 😃 tana neman amintacce da mai kula da ita da gaskiya.

A takaice dai ita Tagari mai CAPACITY a Addini kawai take bukata.

In kana da sana'a da za ka ciyar da ita kullum, to, kana da PAKACITY. Sauran duka KARYA ce da TSORO.                    ...
12/07/2025

In kana da sana'a da za ka ciyar da ita kullum, to, kana da PAKACITY. Sauran duka KARYA ce da TSORO.

Ina masu 'CAPACITY' na tsayawa a layin shawarma - amma su ce aure sai sun gina gida? Shin shawarma tana da mortgage (Jin...
12/07/2025

Ina masu 'CAPACITY' na tsayawa a layin shawarma - amma su ce aure sai sun gina gida? Shin shawarma tana da mortgage (Jinginar gida) ne.?

Kar ka bari soyayya ta tsufa saboda kana jiran 'LOKQCI MAFI DACEWA' lokaci mafi dacewa shine yanzu...Aure akwai albarka ...
11/07/2025

Kar ka bari soyayya ta tsufa saboda kana jiran 'LOKQCI MAFI DACEWA' lokaci mafi dacewa shine yanzu.
..Aure akwai albarka

Babu aure mafi kyau da ya fara da kudi, duk suna farawa ne da niyya, kuma sai s**a sami komai daga baya...Auren wuri akw...
11/07/2025

Babu aure mafi kyau da ya fara da kudi, duk suna farawa ne da niyya, kuma sai s**a sami komai daga baya.
..Auren wuri akwai albarka aciki kuma mabudin arziki ce matukar an yi shi da kyakkyawar NIYYA kuma babu sabon Allah a ciki.

Wasu sunyi aure da tsintsiya da tukunya daya yau suna da gida uku, kawai kayi aure, Allah ne mai bayarwa da daukaka...Au...
11/07/2025

Wasu sunyi aure da tsintsiya da tukunya daya yau suna da gida uku, kawai kayi aure, Allah ne mai bayarwa da daukaka.
..Auren wuri yafi zinar wuri.

Shin waye ya gama shirye-shiryen aure ne? Ko ango ma yawanci yana aron takalma ne.Kaso daya ne 1% cikin dari ke kammalaw...
11/07/2025

Shin waye ya gama shirye-shiryen aure ne? Ko ango ma yawanci yana aron takalma ne.

Kaso daya ne 1% cikin dari ke kammalawa komai da komai, har da wasu masu CAPACITY ba sa kammala shirye-shiryen aure.

Kar dai a manta AUREN wuri tafi Zinar wuri...

Babu wanda ya gama gina gida da hada komai kafin aure mafi yawansu ma sun fara ne da daki da darduma da rufi da addu'a n...
11/07/2025

Babu wanda ya gama gina gida da hada komai kafin aure mafi yawansu ma sun fara ne da daki da darduma da rufi da addu'a ne.

AUREN wuri dai tafi Zinar wuri...

Wasu suna gudun aure ne saboda suna ji ana cece-kuce, amma a karshe sai su ji ana ce musu: "WAI SHI BAI YI AURE BA NE HA...
11/07/2025

Wasu suna gudun aure ne saboda suna ji ana cece-kuce, amma a karshe sai su ji ana ce musu: "WAI SHI BAI YI AURE BA NE HAR YANZU?". Gori kenan.

Don haka duk wanda ya samu damar yi yayi kawai kada yaji tsoro.

Yin AURE da wuri yana gyara zuciya kamar yadda sallah ke gyara hali - duka biyun ibada ne.AUREN wuri yafi ZINAR wuri... ...
11/07/2025

Yin AURE da wuri yana gyara zuciya kamar yadda sallah ke gyara hali - duka biyun ibada ne.

AUREN wuri yafi ZINAR wuri...

Address


Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Citizenship HAUSA posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Citizenship HAUSA:

Shortcuts

  • Address
  • Telephone
  • Alerts
  • Contact The Business
  • Claim ownership or report listing
  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share