English to Hausa

English to Hausa This page is for learning English and Hausa language.

28/10/2025

Darasinmu na yau - Personal pronoun Part 4

28/10/2025

Darasinmu na yau - Personal pronoun Part 3

28/10/2025

Darasinmu na yau - Personal pronoun Part 2

12/12/2023

Darasinmu na yau - Personal pronoun Part 1

Darasinmu na yau shine rabe-raben wakilin suna.Zaku iya ziyartan shafinmu na TikTok
06/12/2023

Darasinmu na yau shine rabe-raben wakilin suna.
Zaku iya ziyartan shafinmu na TikTok

Check out English to Hausa's video.

13/10/2023

- 1

Prepositions are most commonly followed by a noun, phrase or pronoun. Prepositions relate words or elements in a sentence.
There are over 200 prepositions in English, the most common single prepositions are:

About, before, down, into, through, above, behind, during, to, across, below, except, of, toward, after, beneath, for, off, under, among, beside, from, on, up, around, between, over, with, at, by, instead of, since, without, near, beyond, underneath, against, despite, onto, unlike, along, down, opposite, until, among, out, around, except, down, opposite, until, among, out, around, outside, upon, as, via, past, within, inside, than, beneath,

Galibi "noun", "phrase" ko "pronoun" sune suke kasancewa a gaban "prepositions". "Prepositions" yana nuna alaƙa ne tsakanin kalmomi ko wasu abubuwa. Akwai sama da prepositions 200 a turanci. Amma waɗanda s**a fi shahara sune kamar haka:
About, before, down, into, through, above, behind, during, to, across, below, except, of, toward, after, beneath, for, off, under, among, beside, from, on, up, around, between, over, with, at, by, instead of, since, without, near, beyond, underneath, against, despite, onto, unlike, along, down, opposite, until, among, out, around, except, down, opposite, until, among, out, around, outside, upon, as, via, past, within, inside, than, beneath.

Muhaɗu a darasi na gaba🙏🏻

21/05/2023

DARASIN MU NA 👇

UNIT OF TIME

We measure time mainly with :

Seconds,
minutes,
Hours,
Days,
Weeks,
Months
Years :

NAU'IKAN LOKACI

Muna auna lokaci musamman da :

Sakan,
Mintuna,
Awanni,
Kwanaki,
Makonni,
Watanni,
Shekaru :

1. 1000 milliseconds = 1 Mili sakan dubu yake sakan ɗaya.

2. 60 seconds = 1 minute
Sakan sittin yake minti ɗaya.

3. 60 minutes = 1 hour
Mintuna sittin suke awa ɗaya.

4. 24 hours = 1 day
Awanni ashirin da huɗu suke kwana ɗaya.

5. 7 days = 1 week - Kwana bakwai, sati ɗaya.

6. 28, 29, 30 or 31 days = 1 month - 28, 29, 30 ko 31, wata ɗaya.

7. 365 or 366 days = 1 year, kwana 365 ko 366, shekara ɗaya.

8. 12 months = 1 year - Wata sha biyu, shekara ɗaya.

9. 10 years = 1 decade - Deked ɗaya, shekara goma.

10. 100 years = 1 century - ƙarni ɗaya, shekara ɗari.

11. 1000 years = 1 millennium - Mileniyam ɗaya, shekara dubu.



Badamasi Mairecord Vander Sar

24/09/2021

Preposition part.1

Gatabatarwa :

Masu fassara sun fassara kalmar preposition da 'Bigire' a yaren Hausa.

Ataƙaice ma'anar kalmar tana nufin wasu gajerun kalmomi ne da ake haɗawa tsakanin suna da wakilin suna da noun-phrase domin su bada jimla.

Misalan kalmomin preposition suna da yawa amma zamu ɗau wasu guda uku masu kamaimainiya da juna muyi darasi akan su.

SUNAN DARASIN :

PREPOSITIONS OF TIME

1. IN

2. ON

3. AT

Kalmar "IN" tana nufin ciki, amma yawancin kalmomin turanci ana juyasu su canza wata ma'ana daban musamman a cikin jimla, sai dai ana iya juya kalmar ne ta hanyar amfani da muhalli na kalma, misali kalmar in :

1. IN ==> periods of time

Anan kalmar "IN" tana magana ne akan lokuta uku

i. In the future - a kacin da ba'a shiga ba.

ii. In the present - a lokacin da ake ciki.

iii. In the past - a lokacin da ya wuce.

Misali :

i. I'd like to get married - Ina so inyi aure.

ii.We were in time - Mun zo da wuri.

iii. He's in a good mood today - Yau yana cikin ƙoshin lafiya.

iv. He made a study of history in the school - ya koyo karatun tarihi a makaranta.

v. I studied hard in school - Nayi karatu sosai a makaranta.

2. We use "IN" To talk about years - Muna amfani da kalmar "IN" dan yin magana akan shekaru misali :

In 2000 - a shekarar 2000.

In 1990s - a shekarar 1990s.

In 1988 - a shekarar 1988.

In 1980s - a shekarar 1980s.

In 2020 - a shekarar 2020.

In the 19th century - a ƙarni na 19.

In 1988. I was born - A shekarar 1988. Aka haifan.

I was born in the 1980s - An haifan a shekarar 1980s.

My great grandfather was born in the 19th century - An haifi kakan-kaka na a ƙarni na 19.

3. We also use "IN" To talk about months/weeks - Muna amfani da kalmar "IN" wajen yin magana akan watanni/Sati misali :

In June - a watan Yuni

In November - a watan Nuwamba

In five weeks time - Nan da sati biyar

In a few weeks - Nan da ƴan makonni

In October, i will be 34 - a watan Oktoba zan cika ɗan shekara 34.

4. We use "IN" To talk about parts of days - Muna amfani da kalmar "IN" don yin magana akan ɓangarorin ranaku misali :

In the morning - Da safe

In the evening - Da marece

In the night - Da dare

In the afternoon - da rana

Early in the morning - Da Asuba/ da duku-duku

In the night i like to relax and watch the television - Ina son shaƙatawa da kallon talabijin da dare.

In the morning i like to drink a tea - Ina son shan shayi da safe.

10/03/2021

POSSESSIVE PRONOUN LESSON - 2

Possessive pronouns are used in English to avoid repeating of information that is already clear in the sentence

Ana amfani da (wakilin suna) mai nuna mallaki a cikin turanci don kawar da maimaita bayanin da ya riga ya bayyana a cikin jumla

Ga misalai nan cikin jimla, daga cikin jimlolin akwai Common errors in English incorrect sentence da correct sentence

1. I didn't have my cap so Habibu lent me his cap❌
Ba ni da hular kaina sai Habibu ya ara min hular sa❌

1. I didn't have my cap so Habibu lent me his☑️
Ba ni da hular kaina don haka Habibu ya ba ni aron tashi☑️

2. Her phone its more expensive than my phone❌
2. Wayarta ta fi wayata tsada❌

2. Her phone its more expensive than mine☑️
2. Wayarta ta fi tawa tsada☑️

3. This food is our food and not their food ❌
3. Wannan abincin namu ne ba abincin su bane ❌

3. This food is ours and not theirs ☑️
3. Wannan abincin namu ne ba nasu bane ☑️

4. The book is my book not your book❌
4. Littafin nawa ne ba littafinka bane❌

4. The book is mine not yours☑️
4. Littafin nawa ne ba naka bane☑️

ƙarin bayani wannan darasi yana hani ga maimaita kalmar da an riga an faɗeta a cikin jumla,
Idan ka faɗi kalma acikin jimla musamman sunan mutum ko wani abu to baka da damar da zaka ƙara ambatarta sai dai kayi musaya da wakilin suna don ganin ka kawar da maimaita suna acikin jimla, idan ka ambaci suna sama da sau ɗaya acikin jimla mutane zasu fahimcka sannan zasu gane amma a tsarin koyarwar nahawu kuskure ne yin hakan, ba sai a turanci ba a kowani yare ma kuskure ne maimaita suna acikin jimla, da fatan kun gane.

Darasin mu na gaba shine :
Possessive pronoun lesson - 3

Address

Opposite Abdullahi Makama House Zango Rogogo Road
Zango

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when English to Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to English to Hausa:

Share