Sir Wisdom II

Sir Wisdom II I carry the past, respect the present, and engineer the future.
(2)

Takaitaccen Tarihin Annabi Muhammadu (S.A.W)1. HAIHUWAR SA DA ASALINSA Annabi Muhammadu (S.A.W) an haife shi ne a garin ...
19/05/2026

Takaitaccen Tarihin Annabi Muhammadu (S.A.W)

1. HAIHUWAR SA DA ASALINSA

Annabi Muhammadu (S.A.W) an haife shi ne a garin Makka a shekara ta 570 Miladiyya, shekarar da ake kira shekarar giwaye – a shekarar da sarki Abrahata yazo da rundunar giwaye domin rusa ka'aba, amma Allah ya halaka su da tsuntsaye masu jifa da duwatsu na wuta.

Sunansa Muhammadu ɗan Abdullahi ɗan Abdul-Muṭṭalib, daga zuriyar Annabi Isma’il ɗan Annabi Ibrahim (AS). Mahaifinsa ya rasu tun kafin a haife shi, mahaifiyarsa kuma, Aminatu ta rasu tun yana ƙarami.

2. ƘURUCIYAR SA DA HALAYENSA

Yayin da yake ƙarami ya girma ne a wajen wata mace mai suna Halimatu sa’adiyya wadda ta reneshi a karkara

ya kasance mai k**ala gaskiya da amana har ma mutanen makkah suna kiransa da "Al-Amin" (Amintacce).

3. AUREN SHI DA SAYYADA KHADIJAH

Yana da shekara 25, ya yi aure da Sayyida Khadijah bint Khuwaylid, wata babbar mace mai arziki kuma mai daraja, Ita ce mace ta farko da ta karɓi Musulunci kuma ta kasance garkuwa gare shi (s.a.w)

4. FARKON WAHAYI

Yana da shekara 40, a yayin da yake zaune a (dutsen hira) sai Mala’ika Jibrilu ya zo da saƙo daga Allah:
"Karanta!" (Iqraa’)
Wannan shine farkon saƙon Annabci – wanda ya kai shekaru 23 yana yada shi.

5. GWAJI DA ƘOƘARIN YAƊA SAƘO

A Makka, mutane da yawa sun ƙi karɓar saƙonsa, musamman ‘yan ƙabilar Quraysh, sun tsananta masa da sahabbansa, sun ƙuntata musu, har aka tilasta wasu yin hijira zuwa Habasha..👌

6. HIJIRARSA ZUWA MADINA 🌴🌴

Daga ƙarshe, Allah (s.w.a) ya umarce shi da yayi hijirah daga makkah zuwa garin madina, Ya bar Makka tare da abokinsa Abubakar As-siddiq (RA)
Wannan hijirah itace ta wanzar da sabuwar rayuwa ga musulmi baki ɗaya..🫵👌

7. JIHADI

A madina ne Annabi (S.A.W) ya kafa al'umma ta musulunci bisa gaskiya, adalci da zumunta tsakanin mabiya, an yi wasu yaƙe-yaƙe don kare Musulunci k**ar 1-Badr
2-Uhud
3-Khandaq

Annabi bai taɓa zaluntar kowa ba–hatta da maƙiyansa ma idan sunyi masa abu na cutarwa yakan yafe musu (s.a.w)

8. KARƁAR MAKKAH:

Bayan shekara 8 da hijira, Annabi (SAW) ya koma Makka cikin nasara da ladabi, baiyi ramuwa game da azabar da kafiran makkah s**ayi masa ba, yakan ce dasu:
"Ku tafi, kun ƴanta, babu laifi a kanku."
Wannan ya nuna tausayi da yake dashi a zuciyarsa da rahama

9. WAFATIN SA

A shekara ta 11 bayan hijira (632 Miladiyya), Annabi (SAW) ya rasu yana da shekara 63. Ya rasu a cikin ɗakin matarsa da yafi ƙauna A’isha (RA), kuma aka binne shi a can.

Annabi Muhammadu (SAW) rahama ne ga duniya baki ɗaya, saƙonsa da yazo dashi babu komi a ciki face gaskiya da adalci...❤️❤️💞

Allah kayi salati maras adadi ga shugaban mu Annabi Muhammad s.a.w

A cikin Kruger National Park a ƙasar South Africawani gogaggen mai kula da namun daji mai suna Sipho Nkosi ya sami bugaw...
18/05/2026

A cikin Kruger National Park a ƙasar South Africa

wani gogaggen mai kula da namun daji mai suna Sipho Nkosi ya sami bugawar zuciya (heart attack) yayin da yake sintiri shi kaɗai.

An gano motarsa babu kowa a ciki, lamarin da ya sa aka fara neman sa.

Abin da kyamarorin sa ido da ke cikin dajin s**a nuna ya taɓa zuciyar duk wanda ya kalli bidiyon.

Wani tsohon toron giwa wanda masu kula da dajin ke kira “Mnumzane” (kalma ce ta harshen Zulu wadda ke nufin “Yallabai”), shi ne ya gano gawar Sipho.

Na tsawon kwanaki uku da dare uku, giwar ta ƙi barin wajen, yayi tsaye tare da gadin gawar, tana shafa Sipho a hankali da hancinta (trunk), tana korar kuraye da sauran dabbobin da s**a kusanci gawar, har ma tana rufe wasu sassan gawar da rassan itatuwa da ganyaye.

Har a daren rana ta uku giwar tana wurin, tana nuna alamar baƙin ciki, tana karkada jikinta a hankali kusa da mai kula dasu da ya rasu.

Sai bayan tawagar ceto ta iso da motoci ne Mnumzane ta ja baya, tana kallo cikin nutsuwa yayin da ake ɗaukar gawar Sipho...😭

Daga baya, jami’an gandun dajin sun tabbatar da cewa Sipho ne ya ceci wannan giwa tun tana ƙaramar jaririya, bayan mafarauta sun kashe mahaifiyarta shekaru da s**a wuce, Giwar ba ta manta da wannan alheri ba... 🐘

Ɗaya daga cikin abokan aikinsa da ya kalli bidiyon ya ce;
“Ba ta zo domin yin bankwana ba, tazo ne domin tabbatar da cewa babu wanda zai wulaƙanta gawar wanda ya ceci rayuwar ta tun tana ƙarama

Har yanzu Mnumzane yana yawan dawowa wannan wuri, wanda yasa masu kula da gandun dajin suke ajiye ruwa da ‘ya’yan itatuwa a wurin domin girmama su duka biyun.

Sir Wisdom II

Shin ka taɓa tunanin yaya halittar raƙumi take?yaya al'amarin dake ɓoye a tattare dashi yake ?Amma ka taɓa karanta aya t...
17/05/2026

Shin ka taɓa tunanin yaya halittar raƙumi take?
yaya al'amarin dake ɓoye a tattare dashi yake ?

Amma ka taɓa karanta aya ta (17) cikin suratul Gashiya inda Allah madaukakin sarki yake cewa:

﴿أَفَلَا يَنظُرُونَ إِلَى الْإِبِلِ كَيْفَ خُلِقَتْ﴾
[ الغاشية: 17]

"Shin basu duban raƙumi 🐫 yadda aka halitta shi"

Muje zuwa binciken masana domin sanin sirrin dake tare dashi👇

Wani abun burgewa dangane da halittar raƙumi 🐫 da Ubangiji Madaukakin Sarki yayi;

Raƙumi 🐫 yana iya shan ruwan teku mai gishiri da kuma ruwan kogi ko kuma ruwa maras gishiri: Ubangiji ya halitta ƙoda (kidney) na raƙumi 🐫 yadda zai iya tace gishiri mai yawa daga ruwan teku, yadda zai zamto daidai domin amfani a jikinsa, sauran gishiri kuma zai zamto ya fita ne ta hanyar fitsari

Raƙumi 🐫 yana iya cin ƙaya ba tare da ta cutar dashi ba dalili: yawun raƙumi 🐫 yana da kauri, hakan yana bashi daman sanya ƙaya tayi laushi ba tare da ta cutar dashi ba.

Leɓɓan shi da kuma da kuma cikin bakin shi suna da tauri sosai, hakan yasa yake iya tauna ƙaya cikin sauƙi.

Raƙumi yana da fatan idanu guda 2 masu bawa idanun shi kariya: 1 bashi da kauri siriri ne kuma ana ganin shi, 1 kuma yana da kauri kuma yana da tsoka. Lokacin da ƙura ta tashi a cikin sahara, Raƙumi 🐫 yana rufe fatan idanun shi mara kaurin domin hana ƙasa shiga, amma kuma duk da a rufe ne yana gani, fatar tana zama mishi k**ar wani gilashin kariya kenan, Hakannan yana da dogon gashin idanu wanda suke hana ƙasa shiga cikin idanunshi.

Raƙumi yana da Ƙwarewar ƙwaƙwalwa wajen tantance nesa
Kwakwalwar raƙumi ta saba da binciken hoton da idon sa ya gani, don haka yana iya gane tsayin abu da tazara cikin sauri.

Wannan yana taimaka masa wajen gane tafarkin ruwa ko abinci a cikin hamada mai nisa.

Idanun raƙumi suna da ƙwayoyin gani (rods da cones) masu yawa wanda suke taimaka masa gani da kyau a lokacin dare wanda tamkar da rana yake gani.

Raƙumi yana iya kwanaki 7 zuwa 15 ba tare da yasha ruwa ba, sannan idan ya samu ruwa yakan sha sama da lita 100

Haka kuma Raƙumi 🐫 yana iya lura da yanayin zafi ko sanyi na jikin shi wato (body temperature)..

Tsarki su ƙara tabbata ga Ubangiji, Allahu Maƙagin Ɗan Adam, Aljan, Dabba, Tsuntsaye, Shine wanda Bashi da farko b***e ƙarshe.

Wannan fa kaɗan ne daga cikin baiwa da Ubangiji ya tara a jikin wannan dabba ta raƙumi 💪💯

Allah yasa mu wanye lafiya.

Sir Wisdom II pen.. 🖊️

Wata rana wani ƙaramin yaro ya taho da gudu zuwa ga Mahaifiyarsa yana kuka yana ƙiran sunanta yana cewa: "Ummanah Jarir ...
17/05/2026

Wata rana wani ƙaramin yaro ya taho da gudu zuwa ga Mahaifiyarsa yana kuka yana ƙiran sunanta yana cewa: "Ummanah Jarir da Mughiz duk sun saka kayan sallarsu nima za'a a sakamin nawa?”

Uwar ta ɗauke shi ta share mishi hawayen dake kwaranya a fuskarashi, Uwar ba wata bace illa Fatima bint Abdul Malik Radiyallahu anhu, Ubanta, Kakanta, da dukkan Ƴan'uwanta 4 sunyi Kalifanci ko jagorancin al'ummar musulmai.

A wannan lokacin ma mijinta shike khalifanci wato Umar ibn Abdul-Azeez wanda ya mulki daular da tafi kowacce girma a duniya.

Uwar sai tayiwa yaron alƙawarin cewa ya bari babanshi ya dawo zasu duba suga ko yanada sabbin kayan da zai saka.

Yayinda babanshi wato Khalifa Umar ibn Abdul Aziz ya dawo gida, sai matarshi ta faɗa mishi abinda ɗan shi yake buƙata.

Idanun Khalifa s**a canja ya kalleta yace: “Ya Fatima, kinsan yadda nake son ƴaƴa nah, amman dukkan kuɗin da nake dasu kinsan suna wajen ki, bazasu kai mu saya mishi kayan sallah ba.

Khalifa Umar ya kasance mai tsantseni da rayuwa tare da son yin adalci ga jama'arshi.


Fatima ta amince da maganar mijinta, amma tace inaga wataƙila s**ai mu sayamar koda wasu irin kaya masu arhane domin yayi farin cikin yasa sabbin kayan sallah.

Nan take hawaye s**a fara kwaranya daga fuskar Khalifa Umar sai yayi shawarar ya tuntuɓi ma'ajinsa take yayiwa treasurernsa wasiƙa yana neman a bashi rance kuɗi acikin albashin sa kafin wata ya ƙare domin ya samu ya sayawa ɗan shi kayan sallah.

Khalifa yayi sa'ar treasurer na gari mai adalci, wanda take shima yayi masa wasiƙa a matsayin amsa.

Bayan an kaiwa khalifa ya karɓi saƙon wasiƙar ya fara karantawa nan take hawaye ya fara kwaranya a idonshi, Ga yadda wasiƙar tazo mishi:

“Ya Amirul Mumineen, ina matuƙar baka girma, na yarda da kai kuma ina mai matuƙar biyayya a gareka, Amma duk da haka, idan zaka jaddadamin cewa zaka rayu har zuwa wani watan ka aiwatar da aikin ka ga talakawa (wanda shi zaisa a biyaka), toh tabbas zan saka hannu a baka kuɗin ka na wani watan

Idan kuma baka da tabbaci akan cewa zaka rayu har zuwa wani watan, to meye zai sa treasury ta biyaka? kuma meyasa kake ɗaukan haƙƙin talakawa, marayu da zawarawa a kafaɗar ka?”

Nan take Khalifa Umar ibn Abdul Aziz ya gane kurenshi, sai matarshi Fatima bint Abdul Malik ta wanke tsofin kayan yaron.

Ranar bikin Idi yayi, garin yacika maƙil da jama'ah kusan kowa sanye yake da sabbin kayanshi na sallah, Khalifa Umar ibn Abdul Aziz shima ya fito domin sallar Idi riƙe da hannun Ɗan shi inda dukkansu suke sanye da tsofin kayansu.

Take fuskar yaron ta cika da annashuwa yayin da suke takawa da babanshi, ya ƙara yadda da cewa daɗin dake lahira yafi duniya yawa nesa ba kusa ba.

Yan'uwa masu daraja mu duba fa k**ar ba daga yumɓu guda aka haliccemu da suba. Shin haka shugabannin mu suke a yau?

Ubangiji muke roƙo ya gyara mana halayen mu da na shugabannin mu baki ɗaya

Allah yasa mu wanye lafiya...🙏🙏

Akwai ustazi da aka k**a a ƙofar gida yana kwanciyar zafi don shan iska aka tafi dashi station.. bayan da Ƙanin shi yaje...
16/05/2026

Akwai ustazi da aka k**a a ƙofar gida yana kwanciyar zafi don shan iska aka tafi dashi station.. bayan da Ƙanin shi yaje bail, ya kwatanta musu shi sai kuwa s**a ce wanda aka k**a a a gidan Karuwai ko?? 😳 ƙanin cike da mamaki_bayan an fito da yayan daga cell yana bayan kanta kafin a sallame shi sai ɗan sandan ya kalle shi yace "kaine wanda muka k**a a gidan karuwa ko??" nanfa ran ustazu ya ɓaci yace "shi sam ba anan aka kamo shi ba".. nanfa ƙanin yaci gaba da roƙon su cika ya'yan nashi_yan sanda s**a ce "sam! sai ya amsa laifin sa" akayi-akayi ustazu yaƙi yadda! Ashe Oga yana office yana jin yadda ake fama da Ustazi. Da Oga ya fito sai yace: "Oh wannan shine ɓarawon handcuff ɗin mu ko?" 😅. Ustazi da kanshi yace: "Yallaboi a gidan matan banza aka k**ani" Ustazi yaji wuya da kanshi ya amsa 😀😀😀..

Alherin Allah Ya kai ga hukumomin ƙasar mu, Allah Ubangiji Ya gyara mana masu sharrin cikin su Ya kuma kare mana su Ya basu ikon aikin adalci wajen tsaron ƙasa.

Sir Wisdom II...sashin raha da nishaɗi...🖊️

Wata mata ta farka daga bacci sai ta samu Mijinta baya Kan gado 🛏....Saita tashi ta fito tana dube_dube tana neman shi, ...
12/05/2026

Wata mata ta farka daga bacci sai ta samu Mijinta baya Kan gado 🛏....

Saita tashi ta fito tana dube_dube tana neman shi, Tana dubawa saita same shi a kitchen yana zaune ga kofin tea a gaban shi...☕

Sai ta lura taga k**ar yana cikin yanayin tunani mai zurfi, domin taga yana kallon gini..

Tana kallon shi yana share ƙwalla 😢 yana kurɓan tea☕...

Sai tace dashi: "dear meke faruwa ne?"

Sai mijin ya kalli sama yace da ita: "kawai ina tuna lokacin da muka fara soyayya ne shekaru 20 da s**a wuce, zaki iya tunawa ko?"

Hakan sai ya taɓa zuciyar matar domin tana tunanin mijin nata is so caring and sensitive ne...🥰

Sai tace dashi: "yes I do darling"😍

Mijin sai ya ɗan yi zugum.....🥹

Sai yaci gaba da cewa: "kin tuna lokacin da Babanki ya k**a mu a lungun gidan ku muna zance?"

Tace: "eh na tuna" tana mai sunkuyar da kanta ga kujerar dake kusa dashi saboda kunya...😁

Mijin nata sai yaci gaba da cewa...🗣️

"kin tuna lokacin daya nuna mini bindiga yace dani: "Ko ka auri ya' ta, ko kuma na turaka gidan yari na shekaru 20?"...🥸

Matar tace: "na tuna wannan ma sweetheart"

Sai mijin ya share hawayen shi ya ƙara kurɓan tea ɗin shi sannan yace: "Da lokacin na ɗauki zaɓin daya dace dani da yau zan fito daga gidan yari" 😅 😅 😅

Anan fa fada ya kaure......
😂😂😂😂😂🏃‍♂🏃‍♂🏃‍♂🏃‍♂

Sir Wisdom II pen...🖊️

Anyi wani Sarki a wata masarauta wanda yake da ido ɗaya da ƙafa ɗaya amma kuma ya kasance mai basira da tausayin talakaw...
07/05/2026

Anyi wani Sarki a wata masarauta wanda yake da ido ɗaya da ƙafa ɗaya amma kuma ya kasance mai basira da tausayin talakawa..👌

Kowa a masarautar yana rayuwa ta jin daɗi saboda yadda sarkin ke kyautata musu.

Wata rana, sarkin yana wucewa a cikin fadar tashi sai yaga zanen hotunan Iyayen shi da kakanin shi a parlour, sai yayi tunanin shima ya k**ata yasamu ayi zanen shi domin shima ƴaƴan shi da jikokin shi suna tuna shi da wannan zanen.

Sai Sarkin yasa aka gayyato dukkanin masu zane na garin hadda maƙwabta domin suzo su zana hoton shi

Sarki ya bada shelar cewa duk wanda ya zana hoton shi mai kyau, zai samu wasu kyaututtuka na musamman daga fada

Duk masu zanen sai s**a fara tunanin ae sarki idanun shi ɗaya ne kuma ƙafar shi ɗaya ce, yaya za'a yi ace an zana shi Hoto yayi kyau kuma? 🤔. Hakan bazai yiyu ba, kuma idan akayi zanen baiyi kyau ba kowa yana tsoron hukunci daga fadawan sarki.

A sabo da haka ɗaya bayan ɗaya duk sai s**a fara bada uzuri suna ɓacewa domin kada suyi zanen.

Ana cikin hakan, sai wani mai zane ya ɗaga hannun shi yace: "Ranka shi daɗe zan jaraba zana hoton ka yayi kyau sosai in Allah Ya yadda". Sarki sai yayi farin ciki da hakan.

Mutumin ya k**a zane har ya gama, sannan ya lulluɓe zanen sai ya sanar da cewa ya kammala.

Dukkanin masu zanen Garin dana maƙwabta kowa yazo yana jira yaga yaya akayi aka zana Sarki mai ido ɗaya da ƙafa ɗaya kuma yayi kyau? 🤔

Yanzu idan sarkin baiyi kyau ba yaya kenan zaiyi? 🤔.

Lokacin da mutuminnan ya buɗe zanen, ae kuwa fada sai ta cika da mamaki da murna.

Abinda yayi shine:

Ya zana Sarkin a zaune akan doki (ƙafar shi ɗaya za'a gani), yana riƙe da 🏹 kwari da baka yayi saitin abinda zai harba yana leƙawa da ido ɗaya a kulle.

Sarkin kuwa sai ya kamu da farin ciki yadda yaga mutuminnan yayi zanen da kyau sosai ya kuma qayatar, sarkin sai yabashi kyauta masu yawan gaske.

Yan'uwa masu hankali da tunani, abun lura anan shine:

Wajibi ne garemu mu kasance masu nufin wasu da alhkhayri da kuma ɓoye aibun wasun mu.

Yak**ata muna ɓoye inda s**a gaza muna maida hankali akan inda s**ayi daidai.

Maimakon kuma ɓoye aibun nasu kawai, sai mu samu mu ɓollowa aibun ta gefe mai kyau domin gyara shi.

Allah Ya sa mu wanye lafiya.
Alƙalamin Sir Wisdom II ....🖊️🖊️

TARIHI YA NUNA CEWA;A lokacin da Suratul Nasr ( إِذَا جَآءَ نَصۡرُ ٱللَّهِ ) ta sauka, Sahabban Ma'aiki sallallahu alai...
06/05/2026

TARIHI YA NUNA CEWA;

A lokacin da Suratul Nasr ( إِذَا جَآءَ نَصۡرُ ٱللَّهِ ) ta sauka, Sahabban Ma'aiki sallallahu alaihi wasallam 💞 duk sai s**a k**a murna saboda tunanin cewa ai sunyi nasara tunda musulunci ya shiga kowani saƙo.

Sai Sayyadi Abubakar (Radiyallahu anhu) kaɗai a cikin su yake ƙwalla 😭 😭 , saboda fahimtar da yayi wa wannan surah, sai wasu daga cikin sahabban s**a tambaye shi menene yasa yake kukan?

Sai yace dasu: "ina kuka domin yadda na fahimci wannan surah, Rasoulullah sallallahu alaihi wasallam 💞 zai koma ga Allah tunda ya idar da saƙo"

Sayyadi Abubakar yafi kowa fahimtar Qur'ani cikin sahabban Ma'aiki sallallahu alaihi wasallam 💞.

Sai Ma'aiki sallallahu alaihi wasallam 💞 yace dasu tabbass hakane abinda Abubakar ya fahimta.

Daga wannan lokaci ne ba a jima ba Ma'aiki sallallahu alaihi wasallam 💞 ya fara jinya.

Anzo za'ayi sallah lokaci yayi, Ma'aiki sallallahu alaihi wasallam 💞 bai samu fitowa ba, sai yace da Ummunah Aisha Radiyallahu anha taje tace ma Abubakar yayi wa mutane sallah, Ita kuma sai taje ga Ummanah Hafsa, tace taje ta faɗawa Umar yayi sallah ga mutane, sau 3 ana hakan, saboda ita Aisha ta san mahaifin ta zaiyi wuya yayi sallar ba tare da yana cikin damuwa ba saboda jikin Ma'aiki sallallahu alaihi wasallam 💞 ya tsananta, Kusan sai da Ma'aiki sallallahu alaihi wasallam 💞 ya ce dasu: "Shin kuna son ku fitinu ne k**ar yadda matan zamanin Annabi Yusuf s**a fitine shi?", sannan aka sanar da Abubakar ya fara bada sallah..👌

Ana cikin sallah, sai ga Ma'aiki sallallahu alaihi wasallam 💞 ya dafo mutane 2 sun shigo dashi cikin masallacin, Sahabban da s**a hango shi sai s**a fara kabbara, nan Abubakar ya gane cewa Ma'aiki sallallahu alaihi wasallam 💞 ya shigo masallacin. Sai ya ja baya Ma'aiki sallallahu alaihi wasallam 💞 ya shiga ya ci gaba da bada sallah, Abubakar kuma yana koyi dashi, sauran mamu na koyi da Abubakar.

Daga bisani Ma'aiki sallallahu alaihi wasallam 💞 ya yi wafati a ɗakin ummunah Aisha.

Lokacin sayyadi Abubakar baya nan, sayyadi Umar ɗan khaɗab ya zare takobi yace; "duk wanda yace ma'aiki sallallahu alaihi wasallam 💞 ya mutu zai fille kan shi"

Jimawa kaɗan sai ga sayyadi Abubakar yazo, da ya shiga ya tabbatar da wafatin Ma'aiki sallallahu alaihi wasallam 💞, shine ya fito ya karanta wannan ayar a gaban sahabbai.

﴿وَمَا مُحَمَّدٌ إِلَّا رَسُولٌ قَدْ خَلَتْ مِن قَبْلِهِ الرُّسُلُ ۚ أَفَإِن مَّاتَ أَوْ قُتِلَ انقَلَبْتُمْ عَلَىٰ أَعْقَابِكُمْ ۚ وَمَن يَنقَلِبْ عَلَىٰ عَقِبَيْهِ فَلَن يَضُرَّ اللَّهَ شَيْئًا ۗ وَسَيَجْزِي اللَّهُ الشَّاكِرِينَ﴾
[ آل عمران: 144]

Nan ne mutane s**a k**a kuka na rashin Ma'aiki sallallahu alaihi wasallam 💞.

Ranar wafatin manzo (s.a.w) itace babbar fitina data taɓa samun Sahabban Ma'aiki sallallahu alaihi wasallam a tsawon rayuwar su 💞

Ya ubangiji kayi daɗin tsira da aminci da salati ga Annabi Muhammadu sallallahu alaihi wasallam 💞

Alƙalamin Sir Wisdom II ...🖊️🖊️

UBANGIJINKA YANA DA ADALCI KUWA???Wata mata ta je gurin Annabi Dauda (AS) cikin fushi, ta ce masa: "Ya Annabin Allah! Ub...
05/05/2026

UBANGIJINKA YANA DA ADALCI KUWA???

Wata mata ta je gurin Annabi Dauda (AS) cikin fushi, ta ce masa: "Ya Annabin Allah! Ubangijinka yana da adalci kuwa?

Sai ya ce: "Kwarai kuwa, mai adalci ne, ba ya zalunci.

Menene labarin ki? Sai ta ce: "Ni bazawara ce, ba ni da mai taimaka min, ga 'ya'ya mata guda 3 marayu. Ina ciyar da su ne da sana'anar saƙa da nake yi.

Jiya na yi sakata mai yawa, na daure a wani jan tsumma, zan tafi kasuwa na sayar, na sami abin da zanciyar da kaina da 'ya'yana, sai wani tsuntsu ya zo ya wafce daga hannuna, kuma ba ni da komai, ga marayu...😭

Kafin Annabi Dauda (AS) ya ce komai ga wannan mata, sai ga wasu mutane su 10 sun shigo, kowannen su da Dinare 100 a hannunsa, s**a ce:

"Ya Annabin Allah! Muna son za mu yi sadaka da wannan kudi, Sai Annabi Dauda (AS) ya ce da su: "Me ya faru?" Sai s**a ce:
"Muna cikin jirgin ruwa, sai iska mai karfi ta taso, jirgin namu ya bule, sai muka dinga ambaton Allah, kuma muka yi bakancen idan Allah Ya tseratar da mu, za mu yi sadaka da Dinare dari-dari.

Muna cikin wannan hali, sai wani tsuntsu ya jeho mana wani jan tsumma, a cikin tsumman akwai wata saƙa.
Sai muka toshe bular da wannan saƙar, Allah Ya tseratar da mu.

Sai Annabi Dauda (AS) ya yi godiya ga Allah, ya fuskanci wannan mata ya ce mata: "Ubangijinki mai adalci ne... Idan kin yi saƙar nawa k**e siyarwa?"

Sai ta ce: "Dirhami daya".
Sai ya ce: "Ga Dinare 1000, Allah Ya sayi saƙarki, karbi ki je ki ciyar da 'ya'yanki".

ya ubangiji ka warware mana matsalolin mu, ka yalwata arzikin mu 🙏🙏

Sir Wisdom II pen...🖊️

NISA'U BAYIN ALLAH...💃🕺Ya dawo daga wajen neman abinci ya tarar da matar sa a palour tana kallon shirin MBCyayi sallama ...
04/05/2026

NISA'U BAYIN ALLAH...💃🕺

Ya dawo daga wajen neman abinci ya tarar da matar sa a palour tana kallon shirin MBC
yayi sallama ya shigo, ta amsa masa ciki-ciki taci gaba da kallo abinta..😏

Murmushi yayi kawai ya nemi waje ya zauna da alamun gajiya a tare dashi ya kalli dining table ga abinci nan an shirya masa k**ar yadda aka saba!, amma abinda yau ya rasa shine tarairaya da kulawa da aka saba yi masa...🥺

ya ɗanyi jim yana satar kallonta, ita kuwa kallo take abinta, ya buɗe baki a hankali k**ar mai shirin yin raɗa ya kira sunan da ya saba kiranta dashi "my treasure" 🥰

Cikin fushi ta juyo "ka neme ta a wani wajen dai! can inda ka tsaya har dare yayi muku tare, sannan harda kashe wayarka! 🔥

Taci gaba da maganganu cikin fushi da faɗa, ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, wani abun ma bata san tana faɗa ba

Yasan halin kayarsa sarai kawai kallonta yake cike da murmushi, baice uffan ba har tayi ta gaji tayi shiru.😔

Ya tashi tsam daga inda yake ya wuce dakin shi, ya shiga toilet bayan ya kammala wankan shi ya fito ya sako jallabiyan shi tare da feso night perfume, sannan ya fito palour inda ya tarar madam tana ta faman kumbura

Yana zuwa ya zuba ruwa mai sanyi a cup ya miƙa mata cikin fara'a domin yasan bata cin abinci sai ya dawo daga aiki suke ci tare, da fari taso tayi gardama amma da taga ya haɗe fuska, saita ta karɓa tare da kurɓa kaɗan ta ajje cup ɗin

Sir wisdom ina gefe da birona ina ci gaba da rubutu..🖊️

Wayar sa ya ɗakko ya miƙa mata tare da cewa riƙe, bayan ta amsa sai taga wayan gaba ɗaya a farfashe, caraf tace masa garin yaya!??🙆😳

Ya ɗora da cewar "nayi crossing t**i ne wayan ya faɗi a kan kwalta before in dawo dauka, mota ya take shi, and nayi ƙoƙari na neman ƙaramin waya na siya don ɗora sim card ɗina ashe shima sim ɗin ya samu issue ya karye, shine kawai na wuce wajen swapping, acan na daɗe haka, amma kinsan hankali na ai yana wajenki my treasure..🥰

Yana maganar tare da kai hannu ya shafi gefen fuskanta, tayi ajiyar zuciya tare da faɗin "Allah sarki babe Allah ya maida alkhayri ga tawa wayan kasa sim ɗinka sai ka bani ƙaramar daka siyo" 🤗

murmushi kawai yayi ya buɗe flask don zuba abinci, wuff tayi ta karɓi spoon ɗin ta haɗa musu, ta fara bashi a baki.

sun ciyar da kansu k**ar yadda s**a saba, nikuma ina gefe ina haɗiyar yawu..🙄🥴

Bayan sun kammala ta kwashe kayan ta dawo ta durƙusa a gabansa k**ar yadda ta saba idan tayi masa laifi zata bashi haƙuri tace (abban ilham) don Allah kayi haƙuri ka yafe min wlh ban sani bane, kasan rashin ka a kusa dani hana min sukuni yake yi, kai kaɗai nake kallo in samu sanyin zuciya, don All...

caraf ! taji ya riƙe ta, tare da ɗago ta daga tsuguno da tayi yana dariya yace "babe babu komi fa is okay matso kiji wata magana"🤗, aikuwa ta miƙa kunne domin ya faɗa mata, kawai sai ji tayi ya sumbaci kumatun ta 😘, tayi wata yar kara tare da siririyar dariya, tana faɗin "saina rama" aikuwa wuf ya tashi ya zagaya bayan kujera, nan s**a fara zagaye zagaye a palour.....!!!🥰💯

Ni kam dake gefe ina rubutun duk abinda yake faruwa, na zabga wata doguwar hamma, wadda take min ishara da cewa tumbina empty yake fah, babu wani ɓata lokaci na rufe takardun rubutun, tare da sanya alƙalami na a cikin aljihu na miƙe na fice abina 🖊️

HIKIMAR LABARIN..👌

Su mata wato duk girman su kuma duk ƙankantar su yan haƙuri ne, idan s**a tashi sama kai saika sauka ka jira su gama, sai ka lallashe su, babu abinda mace take buƙata sama da kulawa da rarrashi domin su tsarin halittar su a haka Allah ya halitta su idan ka iya haƙuri da ƙaramin laifinsu tabbas zasu ƙaunace k**ar ba gobe!💯

Ya Allah ka haɗa kowa da mai sonshi, ka zaunar da iyalai lapia a gidan mazajensu ka basu ikon sauke nauyin dake kawunansu🙏

Sir Wisdom II

04/05/2026

The revenge...😂🐂🐂

Address

Zaria

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Sir Wisdom II posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Sir Wisdom II:

Share