11/05/2026
🕋 INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI’UN
Hukumar National Hajj Commission of Nigeria ta tabbatar da rasuwar wata mahajjaciya ‘yar Najeriya a ƙasar Saudi Arabia yayin gudanar da aikin Hajjin bana.
Marigayiyar, Malamma Aishatu Muhammadu, mai shekaru 73 daga jihar Adamawa State, ta rasu ne a yayin aikin Hajji kamar yadda jami’ai s**a tabbatar.
Rahotanni sun ce marigayiyar ta fito ne daga ƙaramar hukumar Gombi, kuma hukumomi sun bayyana cewa ana ci gaba da kula da sauran mahajjatan Najeriya domin tabbatar da lafiyarsu.
Allah ya jiƙanta da rahama, ya gafarta mata kura-kuranta, ya sanya Aljannatul Firdausi ce makomarta. Allah kuma ya bai wa iyalanta da al’ummar jihar Adamawa haƙurin jure wannan rashi. 🤲