Tambura7

Tambura7 Labarai | Tallace -Tallace | Faɗakarwa | Nishaɗantarwa |

Daga Yanzu Najeriya Ta fita Daga Jerin Kasashen Da IMF Ke Bi Bashi!!! Mun Gode Baba  Asiwaju, Saura wani ya zo ya sake c...
08/05/2025

Daga Yanzu Najeriya Ta fita Daga Jerin Kasashen Da IMF Ke Bi Bashi!!! Mun Gode Baba Asiwaju, Saura wani ya zo ya sake ciyo mana kuma

R.A

LABARAI DAGA ANAMBRA....Yaro ɗan shekara goma sha takwas mai koyon sana'a ya dirkawa yan mata goma ciki har da ƴar ogans...
08/05/2025

LABARAI DAGA ANAMBRA....

Yaro ɗan shekara goma sha takwas mai koyon sana'a ya dirkawa yan mata goma ciki har da ƴar ogansa da yake koyon aiki a wajensa....

Cikin wata biyar kacal ya aikata hakan....

Na rubuta shi wannan labarin duk da kasancewarsa mummuna, saboda sanin cewa mafiyawan inyamurai suna nemo mummunan labari daga arewa su yaɗa a yankinsu don aga munin yan arewa...

Ayi hakuri da kalar labarin....

To Madallah...

Cewar Rabiu biyora

Na yi nadamar zama dan takarar mataimakin shugaban ƙasa ga Atiku a 2023 - OkowaIfeanyi Okowa, tsohon gwamnan jihar Delta...
30/04/2025

Na yi nadamar zama dan takarar mataimakin shugaban ƙasa ga Atiku a 2023 - Okowa

Ifeanyi Okowa, tsohon gwamnan jihar Delta, ya ce ya na nadamar amincewa da tsayawa takarar mataimakin shugaban kasa tare da Atiku Abubakar a zaben 2023.

Okowa ya bayyana cewa wannan matsaya da jam’iyyar PDP ta yanke a matakin tarayya ta saba da ra’ayoyin mutanensa.

Da yake magana a shirin Morning Show na Arise a ranar Litinin, tsohon gwamnan ya ce ya yi dogon tunani a kan illolin wannan zabi.

Ya amince cewa yankin kudu yana da muradin samar da wanda zai gaji Shugaba Muhammadu Buhari, amma shugabancin jam’iyyar PDP ya dauki wata hanya daban.

Okowa ya ce martanin jama’a game da wannan hukunci ne ya taimaka wajen rashin nasarar jam’iyyar a zaben shugaban kasa a jihar Delta.

Ya kara da cewa, duk da wannan koma baya, jam’iyyar PDP ta farfado ta lashe kananan hukumomi 21 daga cikin 25 a zaben gwamna da aka gudanar makonni uku bayan nan.

daga karshe yabar jam'iyyar ta PDP zuwa jam'iyya Mai mulki ta APC

Shugaban Kasa Rã-sha  ( Futin ) ya tura babbar tawagar manyan s0jojin shi domin kara bada kariya ta musamman ga Shugaban...
29/04/2025

Shugaban Kasa Rã-sha ( Futin ) ya tura babbar tawagar manyan s0jojin shi domin kara bada kariya ta musamman ga Shugaban Kasar BirkinaFaso.

Anata kokarin ganin ankwace mulkin Kasar ne daga IbrahimTaore dake kokarin samarwa kasar cigaba mai daurewa.

Menene Ra'ayinku?

Mutumin da ya datse al’aurars@ “domin kawar da sha’awar jim@’i a Benuwe, yace zai mayar da hankali kan bautar AllahTerhe...
29/04/2025

Mutumin da ya datse al’aurars@ “domin kawar da sha’awar jim@’i a Benuwe, yace zai mayar da hankali kan bautar Allah

Terhemen Anongo, mai shekaru 44 da haihuwa mazaunin Gboko a jihar Benue, ya cire al’aurars@ “domin kawar da sha’aw@r jim@’i”.

Anongo, wanda ya yi murabus a makarantar likitanci, ya yi ikirarin matakin zai ba shi damar bauta wa Allah yadda ya k**ata.

A shekarar da ta gabata, ya cire daya daga cikin ’ya’yan marainan sa da kansa, inda ya kusa rasa ransa a cikin wannan aikin.

Ya fara fitowa fili ne a cikin watan Maris bayan anyi masa tiyata, wanda ya yi sanadin zubar da jini.

Shigowar wadanda s**a san halin da yake ciki a kan lokaci ya ceto lamarin yayin da likitocin s**a yi ta zagayawa domin ba shi kulawa.

Anongo, wanda ya bar makarantar koyon aikin likitanci ta Jami’ar Ibadan bisa zargin rashin lafiya, ya ce ya yi hakan ne bisa imaninsa na addini cewa tun da bai yi aure ba, yana bukatar ya bauta wa Allah da aminci.

"Ina lafiya. Babu matsala, ina jira kawai lokacin da raunin zai warke don in cire dinkin. " Inji shi

Ana zargin cewa angon ya kira abokansa su uku domin su riƙe amaryar don ya yi tarayya da ita, lamarin da ya sa ta ɗimauc...
28/04/2025

Ana zargin cewa angon ya kira abokansa su uku domin su riƙe amaryar don ya yi tarayya da ita, lamarin da ya sa ta ɗimauce, har ta rasa ranta

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Jigawa, SP Lawal Sh*tu Adam ya ce an k**a angon da abokansa yayin da suke ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.

Ya kakeji in mai NAPEP ya dauke ka har kukaje inda zaka sauka bai samu passenger ko daya ba?
28/04/2025

Ya kakeji in mai NAPEP ya dauke ka har kukaje inda zaka sauka bai samu passenger ko daya ba?

Shima ana shi bangaren Sarkin Kano Alh Aminu Ado Bayero zai nada sabon Galadiman Kano ranar Juma'a.Me zaku ce?
27/04/2025

Shima ana shi bangaren Sarkin Kano Alh Aminu Ado Bayero zai nada sabon Galadiman Kano ranar Juma'a.
Me zaku ce?

Muhammad Shu'aibu, wanda aka fi sani da Baba Hasin ya rasu ranar Asabar a gidansa, bayan shafe tsawon lokaci yana jinya ...
27/04/2025

Muhammad Shu'aibu, wanda aka fi sani da Baba Hasin ya rasu ranar Asabar a gidansa, bayan shafe tsawon lokaci yana jinya a Asibitin Aminu Kano da ke jihar Kano.

Jarumin ya rasu yana da shekara 68 a duniya, kuma ya bar mata biyu da yara 17.

Gwamnan Zamfara ya ninka alawus din masu yi wa kasa hidima da kaso 100Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara ya umarci a ƙa...
27/04/2025

Gwamnan Zamfara ya ninka alawus din masu yi wa kasa hidima da kaso 100

Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara ya umarci a ƙara kuɗaɗen alawus na masu yiwa kasa hidima (NYSC) da aka tura jihar da kashi 100.

Lawal ya bayyana haka a ranar Juma'a a Gusau, yayin da yake ƙaddamar da buɗaɗɗen atisayen shirin horaswa na 2025 rukunin ‘A’, Stream I na masu yiwa kasa hidima da aka tura jihar.

Gwamnan ya samu wakilcin Sakataren Gwamnatin Jihar, Abubakar Nakwada, a wajen taron.

Ya sake jaddada cewa gwamnatin sa ta himmatu wajen tabbatar da tsaro da walwalar dukkan matasan na NYSC 550 da aka tura jihar.

"Ina farin cikin sanar da ku cewa na bayar da umarnin dawo da biyan alawus na jiha ga dukkan masu NYSC da ke cikin jihar.

"Haka kuma na bayar da umarnin ƙara yawan alawus ɗin da ake biya da kashi 100 cikin ɗari"

Wani jarumin TikTok ya mutu ya na tsaka da yin bidiyon kai-tsayeWani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta ya nuna lo...
26/04/2025

Wani jarumin TikTok ya mutu ya na tsaka da yin bidiyon kai-tsaye

Wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta ya nuna lokacin da wani ɗan TikTok mai suna Disturbing, wanda ke cikin gungun masu fafutukar 'JUSTICE FOR MOHBAD', ya mutu a yayin da ya ke tsaka da watsa bidiyo kai-tsaye.

Wannan labari ya samu tabbaci daga wani dan jarida mai binciken ƙwaƙwat, Temilola Sobola, wanda ya yada wannan bidiyo mai tayar da hankali tare da rubuta: “Wani shahararren ɗan TikTok da aka fi sani da Disturbing, wanda shima yana cikin masu fafutukar JUSTICE FOR MOHBAD, ya rasu wasu awanni da s**a wuce a yayin da yake watsa bidiyo kai tsaye…”

LEADERSHIP ta rawaito cewa, Disturbing, wanda ya yi fice saboda jajircewarsa a fafutukar “Justice for Mohbad”, ya bayyana kakar cikin damuwa sosai kafin ya ɓingire, inda daga bisani ya ce ga garin ku nan.

HOTUNA: An fara gudanar da jana'izar Fafaroma Francis a dandalin St. Peter, inda dubban al'umma s**a taru don yin ban kw...
26/04/2025

HOTUNA: An fara gudanar da jana'izar Fafaroma Francis a dandalin St. Peter, inda dubban al'umma s**a taru don yin ban kwana da shugaban ɗariƙar Katolika na duniya.

Shugaban Amurka Donald Trump da na Ukraine Volodymyr Zelensky da Yarima William na kasar Burtaniya da tsohon shugaban Amurka Joe Biden na daga cikin manyan shugabannin kasashen duniya da s**a halarci jana'izar.

Address

Zazzau Emirate Council
Zaria

Telephone

+2348144385327

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Tambura7 posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share