22/08/2023
Ilimin Crypto da Blockchain a yanzu sun zama ko ka shiga a dama da kai, ko kuma a tafi a barka a baya.
Inada wani Aboki da yake Freelancer ne, yana aiki a ƙasashen waje, irin aikin Programming ɗin nan da mak**antan su, idan yayi aikin sa, suna biyansa in Dollar USD (Dollar ba irin tamu ba ta Crypto USDT) ko Euro a bankin sa na Transfer Wise.
Idan s**a biya shi, dole yana da buƙatar ya chanza kuɗin zuwa Nigerian Naira kafin ya samu yayi amfani dasu tunda daganan Nigeria yake yi musu aikin, duk sanda aka biya shi, dole yake turawa wani abokin sa yake chanza masa zuwa Naira, abokin nasa yace masa yana chajin Fee na 3%. Sau da yawan lokaci ya kan chanza kuɗi da yawa k**ar $3000. Kaga 3% na $3000 ya kai $90. Aƙalla N83K kenan.
Bari kaji, P2P da kake rainawa dai da mukeyi mu saka kuɗi ko mu cire a Binance, shi abokin nasa yakeyi a Binance ya cire masa kuɗin.
Ana haka sai yake cemin na koya masa yaya suke chanzawa, saboda ya taɓa lura abokin nasa k**ar ta Crypto yake cire kuɗin, cikin mintuna kaɗan na koya masa, ya fahimta, daga ranar yakeyi da kansa.
Wannan Freelancer ne, ba ɗan Crypto ba, amma sauƙi da kuma Solution ɗin da Crypto yazo dashi ya shigo dashi cikin ta. Kuma da yaƙi shiga cikin Crypto ɗin, haka zaici gaba da biyan 3% ana cire masa kuɗi ta hanyar Crypto ɗin da yake ganin bai yarda da ita ba.
Idan ka fahimci wannan labarin, wannan shine dalilin da yasa Satoshi Nakamoto ya ƙirƙiri BTC, don sauƙaƙa wa mutane cinikayya, da tura kuɗi tsakanin ƙasashe ba tare da wahalar da kai ba, ko jinkiri.
Zuwa gareka ɗan Crypto, wannan P2P ɗin da kake ganinsa ba'a bakin komai ba, dashi wasu suke riƙe kansu da al'amuran su na yau da kullum, idan wanda ya iya P2P zaiyi wannan, yaya kake gani idan ka faɗaɗa bincike da neman ilimi akan wannan sabgar?