22/08/2025
Baitocin da SAYYIDA FATIMATUZ ZAHRA(S.A) Takeyi yayin da take zuwa Ziyarar Mahaifinta
"Idan na buqaci ganinka sai in zo kabarinka, in yi kuka kuma in yi qorafin rashinka. Amma ba za ka amsa min ba. Ya kai wanda ke cikin kabarin nan! Kai ne ka koya min kuka. Sannan kuma tunaninka yana dauke dukkan baqin ciki. Duk da cewa an binne ka a cikin qasa, amma ba a binne tunaninka a zuciyata mai cike da baqin ciki ba."