07/11/2025
Zan gwada yiwa kaina wani discipline. Na ware $100 a Bitget, kullum zan shiga trade da ita tsakanin 6am zuwa 10am. A wannan tsakanin zanyi analysis, na nemi signal na shiga.
Target dina shine 10%, wato $10. Ba dole bane saina samu abinda nakeso. Kawai zan nemi signal din, kuma zan shiga a tsakanin 6am zuwa 10am. Kona samu 10%, ko samada 10%, ko kasa da 10%, ko asara nayi idan 10am tayi zan fita daga wannan trade din.
Saidai idan naga alamar bearish a kasuwar k**ar yanda muka gani last week, zan haqura da shiga trade har sai kasuwar ta dawo normal.
Wata yarinya yar India ce ta bani wannan shawarar a jiya, tace na fara gwadawa na tsawon wata daya. Hakan zai taimaka mini wajen samun discipline, rage greediness da kuma taimakawa wajen risk management a kasuwar crypto.
Kuma ku gwada, domin tabbas hakan zai taimaka muku sosai. Ba lallai sai a Bitget ba, zaku iyayi aduk kasuwar da kuke ra’ayi. Ba lallai sai ribar 10% ba, amma ku dauki karamar riba (5%-15%). Ba lallai sai 6am-10am ba, zaku iya zabar duk lokachin da yayi muku, amma dai ya kasance komai zakuyi shi chikin 4 hours, tun daga nemo signal, shiga trade da kuma fita. Tabbas yin hakan zai taimaka muku sosai wajen samun discipline, rage hadama (greediness) da kuma karfafa risk management.