06/09/2019
WAKAR DA MARIGAYI IBRAHIM NARAMBADA YA REREMA MARIGAYI SARKIN ZAZZAU MALAM JA'AFARU DAN'ISYAKU.
Jigo: Ai tafi Jekadiya
fado mashi bakonka ya zaka
Amshi: Ba taura bana Narambada Malamin kiddini, In ya ce maraba mun yi kidi Za mu Kwan bakwai, Dan Isyaku makaye Ja'afaru mai halin mazan jiya Zamna da lahiya.
Jgo: Ja'afaru Sarkin rikon amana ne baya walwalewa
Amshi: Sai ka walwale da kanka Yakan walwalewa Dan Isiyaku makaye, Ja'afaru mai halin mazan jiya Zamna da lahiya.
Jigo: Sarkin Gobir na Isa Ahmadu shi yak Kira ni, naji jawabin da yai mani, Ban zauna ba na shigo jirgi, sai fadin nikai jirgi Kai ni Zariya kai dai kai mu Zariya, Kai dai Kai mu lahiya Bisa yardan ubangiji,
Amshi: In mun shida mun ga Ja'afaru mun debe alkawal, Dan Isyaku makaye, Ja'afaru mai halin mazan jiya, Zamna da lahiya.
Jigo: Baban Jekadiya
Amshi: Ruwa da yawa maganin fari
Jigo: Tun ban zo nan ba naji labarin Abdu ya yi Sarki
Amshi: Ya kyauta duniya ×2
Jigo: Har Yero na ji yai Sarauta
Amshi: Ya kyauta duniya,
Jigo: Sarkin Yaki yai Sarauta
Amshi: Ya kyauta duniya
Jigo: Ibrahimu yai Sarauta
Amshi: Ya kyauta duniya,
Jigo: Ja'afaru Kai ag-gidanga, Kai ab babbansu kafi kowa,
Amshi: Wadda nit-taho kamar dai Yamusa ni ishe,
Dan Isiyaku makaye, Ja'afaru mai halin mazan jiya Zamna da lahiya
Jigo Baban Jekadiya
Amshi Ruwa da yawa maganin fari
Dan Isiyaku makaye, Ja'afaru mai halin mazan jiya Zamna da lahiya.
Jigo: Ai wata rana a sha Zuma wata rana a sha madaci, haka duniya take, yau in an ga an ci riba
Amshi Gaba faduwa akai Dan Isiyaku makaye Ja'afaru mai halin mazan jiya Zamna da lahiya
Jigo: Baban Jekadiya,
Amshi: Ruwa da yawa maganin fari ×2
Jigo: Kowai ce ya gane mu Zariya dominka yag-gamu
Amshi: In ba kai ba babu mai iya kawo mu Zariya ×2 Dan Isiyaku makaye Ja'afaru mai halin mazan jiya Zamna lahiya.
Jigo: Baban Jekadiya,
Amshi: Ruwa da yawa maganin fari ×2 Dan Isiyaku makaye Ja'afaru mai halin mazan jiya Zamna da lahiya
Kawowa Abdullahi Musa Badayi.