04/04/2024
SALLAR FANSAR SALLOLI A JUMA'AR ƘARSHE NA WATAN RAMADAN
*Sayyid Abdullahi Ashura*
Yazo a ruwaya cewa "Duk wanda yayi wannan Sallar a wannan ranar ta Juma'ar ƙarshen watan Ramadan, To zata fanshi sallolinshi dabasu cikaba ta shekara dubu. Imam Ali (AS) shine ya ruwaito daga manzan Allah (S), da aka tambayi manzon Allah akan mutun baya wuce shekara 60 zuwa 70 sai yace sauran shekarun zasu fanshi iyayenshi, matarshi, yan uwanshi dama mutanen garinsu.
*YADDA AKEYIN SALLAR:*
Ana yin Raka'a 4 kowace raka'a Fatiha 1 inna Anzalnahu 15 Inna A'daina 15 bayan sallama sai salatin annabi sau 100.
Sannan bayan an kammala ana so ayi wannan Addu'ar dake ƙasa, wanda yayi wannan addu'ar to zai hadu da ɗayan biyu, Kode Allah ya tsawaita rayuwarshi har yakai wata shekarar ko kuma ya gafartamasa in ya mutu. Ga Addu'ar kamar haka:
اللهم لا تجعله أخر العهد من صيامنا إياه، فاءجعلته فاجعلني مرحوما، ولا تجعلني محروما.
Anayin wannar Sallar daga fitowar ranar zuwa zawalinta, dafatan zaku sanyamu cikin Addu'o'inku masu girma.
Sayyid Ashura ne ya fitar Mana shekara uku da s**a wuce, Saifullahi Ningi ya naƙalto.