09/08/2024
GASKIYA AKWAI MATSALA
Akwai wani rikakken dan t@'add@ mai g@rkuw@ da mutane yaron Be||0 Tu yana da account a Tiktok kamar yadda zaku gani a screenshot
Ya saki wani bidiyo a shafinsa na Tiktok ya yaba wa matasan da s**a fita zanga-zanga, sannan a karshe yace a ajiye account number a comment zai tura wa mutane kyautar kudi
Wallahi da na duba comment section mutane kusan dubu uku ne s**a ajiye masa account number, kuma mafi akasarinsu mata ne, Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!
Wannan abin ya bani tsoro, kuma ya sani fargaba sosai, sanin kowane kudaden da wadannan '¥an t@'add@ suke dashi kudin j!ni ne, amma mutanen mu saboda tsabagen kwadayi s**a ajiye account number suna jiran a tura musu kudin j!ni
Duk wanda ya ajiye account number ma wannan dan t@'add@ ba shakka idan s**a masa tayin shiga ayyukansu na t@'add@nci ko bada bayanan sirri zasu yadda, domin duk wanda ya karbi kudin j!ni to zai iya yin aikin masu shan j!nin
Sannan wannan ya kara fitowa da sakacin masu iko da tsaron Nigeria, ta ya zaku kyale dan t@'add@ yana amfani da dandalin sada zumunta a cikin Kasarku har ya tara followers kusan dubu arba'in amma baku sa kamfanin manhajar sun rufe account din ba?
Shin masu iko da tsaron Nigeria bakwa tunanin hakan wata hanyace ta bude, wanda 'yan t@'add@ zasu samu damar gurbata tunanin mutane su shigar dasu ayyukansu na t@'add@nci ko su dinga basu bayanan sirri suna biyansu kudi? sakacin naku yayi yawa
Ina ta tambayar kaina, wai shin bakin talauci ne ko kwadayi, ko jahilci, ko mutuwar zuciya, ko rashin imani, ko rashin tarbiyya, ko kuma masifa ne zai sa mutum ya tura wa dan t@'add@ account number yana jiran ya tura masa wani kaso daga kudin fansa na mutanen da s**ayi garkuwa da su??
Allah Ya sauwake