15/08/2026
Mambobin Harkar Musulunci a Najeriya, almajiran Sayyid Ibraheem Yaƙoub El-Zakzaky (H), sun gudanar da bikin daga tutar “Labbaika Ya Rasulillah” domin nuna farin ciki da shigowar watan Rabi’ul Awwal 1448H a birnin Gombe.
An gudanar da taron ne a yammacin Asabar, 15 ga Agusta 2026, wanda ya yi daidai da 2 ga Rabi’ul Awwal 1448H, inda aka gudanar da shirye-shirye daban-daban na tunawa da zagayowar watan da ake danganta shi da haihuwar Annabi Muhammad ﷺ.
An fara taron da misalin ƙarfe 4:00 na yamma, inda aka gabatar da majalisar mawaƙa, addu’o’i da karatun Alƙur’ani mai girma. Haka kuma, an gudanar da kabbara mai taken “Labbaika Ya Rasulillah”, wadda Malam Abdullahi Abubakar ya jagoranta.
Daga nan ne Harisawa s**a gabatar da faretin girmamawa ga Annabi Muhammad ﷺ a wajen taron.
Bayan haka, Sheikh Muhammad Abbari Gombe, tare da wasu mambobin harkar, s**a isa wajen tutar domin gudanar da bikin daga tutar “Labbaika Ya Rasulillah” da kuma sauke tutar Ashura.
Bayan kammala bikin, Sheikh Muhammad Abbari Gombe ya gabatar da jawabi, inda ya taya mahalarta murnar zagayowar watan Rabi’ul Awwal tare da yin godiya ga Allah kan wannan lokaci.
A cikin jawabinsa, Sheikh Abbari ya tabo wasu daga cikin abubuwan da s**a shafi rayuwar Annabi Muhammad ﷺ, yana mai jaddada darussan da Musulmi za su iya koya daga rayuwarsa da koyarwarsa.
Ya kuma yi kira ga mambobin harkar da su ci gaba da riƙo da abin da s**a yi imani da shi, tare da jaddada matsayinsu na bin Sayyid Ibraheem Yaƙoub El-Zakzaky (H) a tafiyarsu.
An kammala taron ne da gabatar da sanarwa da yin addu’a, kafin a sallami mahalarta.
Da’irar Gombe Media Press ce ta fitar da bayanin taron, tare da wasu hotunan da s**a nuna yadda bikin ya gudana.
Domin samun ingantattun labarai shigo shafin👉 DOVE NEWS HAUSA kayi follow.