31/07/2026
KOTUN KANO TA YANKE WA MATASHIYAR AMARYA MAI SHEKARA 19 HUKUNCIN KISA TA HANYAR RATAYA KAN KISAN MIJINTA KWANA 9 BAYAN AURE
Babbar Kotun Jihar Kano ta yanke wa wata matashiya mai shekara 19, Saudat Jibrin, hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samunta da laifin kashe mijinta, Salisu Idris mai shekara 30, kwanaki tara kacal bayan aurensu.
Da take yanke hukunci a ranar Alhamis, 30 ga Yuli, 2026, Mai Shari'a ta ce masu gabatar da ƙara sun tabbatar da laifin kisan kai ba tare da wata shakka ba.
Ta ce:
"Na yanke miki hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda laifin kisan kai. Kina da kwanaki 90 da za ki ɗaukaka ƙara."
Lauyan gwamnati, Lamido Abba-Sorondinki, ya shaida wa kotu cewa lamarin ya faru ne a ranar 5 ga Mayu, 2025, a unguwar Farawa da ke Kano.
Ya bayyana cewa da misalin ƙarfe 9:00 na dare, Saudat ta sanya wani abu mai guba a cikin abin sha na mijinta mai suna "Zoho", sannan ta yanke masa wuya da wuƙa.
Masu gabatar da ƙara sun gabatar da shaidu biyu a gaban kotu, yayin da wadda ake tuhuma ta musanta aikata laifin.
A nasa ɓangaren, lauyan kare wanda ake tuhuma, Abdulfatah Muhammad, ya roƙi kotun da ta sassauta hukunci, yana mai cewa Saudat ta haddace Alƙur'ani Mai Girma yayin da take tsare, ita ce ɗiya ta fari a gidansu, kuma ƙannenta na dogaro da ita.
Sai dai kotun ta tabbatar da laifin bisa tanadin Sashe na 221(a) na Dokar Penal Code, tare da yanke mata hukuncin kisa ta hanyar rataya.