18/12/2024
🔴 DA ƊUMI–ƊUMI: Ƙungiyar Matasa Masu Kishin Najeriya (PAYOBEN) ta yi kira da a gaggauta sakin Alhaji Bello Abdullahi Badejo ba tare da wani sharaɗi ba, inda ta yi Allah-wadai da ci gaba da tsare shi da sojoji ke yi, tana mai cewa sake k**ashi kuskure ne kuma take hakkin kundin tsarin mulkin ƙasa ne.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, Shugaban PAYOBEN, Moses Adasu Makurdi, ya bayyana halin da Badejo ke ciki a matsayin abin tsoro da ke barazana ga dimokuradiyyar Najeriya. Ya yi tambaya kan dalilin sake k**a Badejo, yana mai jaddada cewa an taɓa tsare shi har na tsawon watanni shida ba tare da wata tuhuma ba, kafin daga bisani a sake shi tare da ayyana shi a matsayin mara laifi.
Makurdi ya kuma nuna damuwa kan lafiyar Badejo, inda ya bayyana cewa lafiyarsa ta yi tsanani yayin tsarewar farko, lamarin da ya sa dole ya je ƙasashen waje neman magani. Ya zargi sojojin da rashin imani bisa sake k**awa duk da sanin cewa lafiyarsa ba ta da kyau.
Kungiyar matasan ta kuma nuna damuwarta kan yadda lamarin ke shafar iyalin Badejo ta fuskar ruɗani da damuwa ta tunani, tana mai jan hankali cewa lamarin na iya ɓata sunan sojojin Najeriya da ma ƙasar baki ɗaya.
(PAYOBEN) ta yi kira ga masu ruwa da tsaki, ƙungiyoyin farar hula, da hukumomin da abin ya shafa, da su shiga tsakani, tana mai jaddada cewa sojoji dole ne su mutunta dokar ƙasa. Kungiyar ta yi barazanar jawo hankalin ƙasa da duniya baki ɗaya idan har ba a saki Bello Badejo ba.
Sai dai har yanzu Sojojin ba su yi martani kan kamun ba.
Sarauniya Radio