Hausa News paper

Hausa News paper Gaskiya ita ce Jigo Hausa Newspaper A Nigeria Komai Sai ya tabbata gaskiya sannan zakuji Daga garimu

15/09/2026

lissafin siyasar Nigeriya 2027

Gwabnatin jihar Kaduna tana keta alfarma da cin mutumcin ƴan adawa; wanda ba haka dokan Nigeria ta tanazar ba! A yau ken...
15/09/2026

Gwabnatin jihar Kaduna tana keta alfarma da cin mutumcin ƴan adawa; wanda ba haka dokan Nigeria ta tanazar ba!

A yau kenan inda aka farmaki ƴan jam'iyar ADC a jihar Kaduna. Dandazon mutane sun fito don nuna goyon baya dayin maraba ga ɗan takaran gwabna Rt. Hon. Isa Ashiru Kudan na dawowan sa daga ƙasar Saudia.

Abin takai har ake turo ƴan daba suna wasa da rayuwar ƴan ƙasa; lallai wannan abu baiyi k**a da siyasa ba, amma jahilci!

Dokar ƙasa taba kowa daman yin jam'iyar dayaso a koda yaushe, wanda hakan yabamu daman kasancewa a jam'iyar adawa ta ADC.

Gwabnatin jihar Kaduna tana keta alfarma da cin mutumcin ƴan adawa; wanda ba haka dokan Nigeria ta tanazar ba! A yau ken...
15/09/2026

Gwabnatin jihar Kaduna tana keta alfarma da cin mutumcin ƴan adawa; wanda ba haka dokan Nigeria ta tanazar ba!

A yau kenan inda aka farmaki ƴan jam'iyar ADC a jihar Kaduna. Dandazon mutane sun fito don nuna goyon baya dayin maraba ga ɗan takaran gwabna Rt. Hon. Isa Ashiru Kudan na dawowan sa daga ƙasar Saudia.

Abin takai har ake turo ƴan daba suna wasa da rayuwar ƴan ƙasa; lallai wannan abu baiyi k**a da siyasa ba, amma jahilci!

Dokar ƙasa taba kowa daman yin jam'iyar dayaso a koda yaushe, wanda hakan yabamu daman kasancewa a jam'iyar adawa ta ADC.

Kaduna FALLE daye ce  Cewar Hon. Saleem tahir Abba  matashin Dan shiyasa Kuma Mataimakin na masamman na Dan takaran Gwam...
14/09/2026

Kaduna FALLE daye ce Cewar Hon. Saleem tahir Abba matashin Dan shiyasa Kuma Mataimakin na masamman na Dan takaran Gwamnan Jahar Kaduna A Jam'iyyar ADC Isa Ashiru Kudan 2027 ya kara da cewa mutane su fito su Zabi ADC daga sama har kasa Dan samun Nasara da cigaban Al'umma Saleem Tahir Abba Isa Ashiru Kudan

Matatar ta Ɗangote tana tayin sama da hannun jari biliyan huɗu a ƙarƙashin wata yarjejeniya da ake sa ran za ta samar da...
14/09/2026

Matatar ta Ɗangote tana tayin sama da hannun jari biliyan huɗu a ƙarƙashin wata yarjejeniya da ake sa ran za ta samar da kusan dala biliyan 1.6.

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC a Zaɓen 2027, Atiku Abubakar, ya yi kira...
14/09/2026

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC a Zaɓen 2027, Atiku Abubakar, ya yi kira da a ƙara bai wa mata dama a harkokin siyasar Najeriya.

Atiku ya bayyana hakan ne yayin da yake magana kan muhimmancin shigar mata cikin harkokin siyasa da shugabanci gabanin Zaɓen 2027.

Ya ce mata na da muhimmiyar rawa wajen ci gaban ƙasa, don haka bai k**ata a bar su a baya wajen yanke shawarar da ta shafi makomar Najeriya ba.

Ya kuma jaddada buƙatar samar da yanayi mai kyau da zai bai wa mata damar yin takara da kuma riƙe muƙaman siyasa.

Mai bai wa Shugaba Bola Tinubu shawara kan yaɗa labarai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ya ce dawo da tallafin zai kaw...
13/09/2026

Mai bai wa Shugaba Bola Tinubu shawara kan yaɗa labarai da dabarun sadarwa, Bayo Onanuga, ya ce dawo da tallafin zai kawo tasgaro ga sauye-sauyen da aka yi a ɓangaren man fetur.

An binne Bamanga Tukur a Yola
An sace malamai 6 bayan halartar taron siyasa a Zamfara
Ya kuma ce hakan na iya rage sha’awar masu zuba jari a matatun mai na cikin gida, ciki har da matatar Dangote da sauran ƙananan matatun mai.

Onanuga, ya bayyana shirin Atiku ba zai ɗore ba.

Ya ce harkar man fetur a Najeriya ta samu sauyi sosai tun bayan da Shugaba Tinubu ya cire tallafin mai a watan Mayun 2023.

Ministan Kuɗi kuma Mai Kula da Tattalin Arziƙi, Taiwo Oyedele, ya ce cire tallafin mai ya samar da Naira tiriliyan 15.8 ga Gwamnatin Tarayya da jihohi da Ƙananan Hukumomi tsakanin Yunin 2023 zuwa Disamban 2025.

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Najeriya (INEC) ta wallafa jerin sunayen ƙarshe na ƴan takarar shugaban ƙasa da mataimak...
13/09/2026

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Najeriya (INEC) ta wallafa jerin sunayen ƙarshe na ƴan takarar shugaban ƙasa da mataimakansu da za su fafata a babban zaɓen watan Janairun 2027.

Jerin sunayen, wanda Sakatariyar Hukumar, Rose Oriaran-Anthony, ta sanya wa hannu, kuma aka fitar da shi ranar Asabar a Abuja, ya ƙunshi ƴan takarar da jam'iyyun siyasa 18 s**a tsayar domin neman kujerar shugaban ƙasa a 2027.

Hukumar ta INEC ta bayyana sunayen'yantakarar 18 da mataimakansu ga dai wasu daga cikinsu

PDP, Sandy Ojang Onor, dan takarar shugaban kasa, Umaru Babangida, mataimaki.

AA, Rufai Adekunle Omo-Aje, dan takarar shugaban kasa da Shehu Hussaini, mataimaki.

ADP, Aliyu Abbas-Bin, dan takarar shugaban kasa da Chinazam Ike, mataimaki.

APP, Kabiru Yusuf, dan takarar shugaban kasa da Peace Egobia Ofordile, mataimaki.

AAC, Omoyele Sowore, dan takarar shugaban kasa da Haruna Garba Magashi, mataimaki.

APM, Oluseyi Abiodun Makinde, takarar shugaban kasa da Musa Lawal Daura, mataimaki.

BP, Sunday Adenuga, takarar shugaban kasa, Usman Turaki Mustapha, mataimaki.

DLA, Moses Olusoji Adebisi, takarar shugaban kasa da Nafisat Usaku Abubakar, mataimakiya.

NDP, Ada Elizabeth Fredrick Okwori, takarar shugabar kasa da Uchenna Anthony Chukwuemeka, mataimaki.

NRM, Nkem Esther Okereke, takarar shugabar kasa da Nasir Muhammed Sulaiman, mataimaki.

PRP, Donald Duke, dan takarar shugaban kasa, Kabiru Rabiu, mataimaki.

SDP, Adewole Ebenezer Adebayo, takarar shugaban kasa da Usman Muhammed Bugaje, mataimaki.

YPP, Peter Ada Agada, takarar shugaban kasa da Patience Ndidi Key, mataimakiya.

ZLP, Daniel Daberechukwu Nwanyanwu, takarar shugaban kasa da Hassan Khalid, mataimaki

Shirin fitar da hannun jarin Matatar Dangote ga jama'a ya sake jawo hankalin ƴan Najeriya zuwa kasuwar hannun jari, musa...
13/09/2026

Shirin fitar da hannun jarin Matatar Dangote ga jama'a ya sake jawo hankalin ƴan Najeriya zuwa kasuwar hannun jari, musamman a daidai lokacin da matasa da dama ke neman hanyoyin gina dukiya da kuma kare kansu daga asarar kuɗi da ke tattare da wasu hanyoyin zuba jari marasa tabbas.

Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya sanar da cewa matatar man fetur ɗinsa za ta fara sayar da hannayen jari ga jama'a ta hanyar Initial Public Offering (IPO), inda aka tsara bai wa kowa damar mallakar kaso a cikin kamfanin ko da da ƙaramin jari ne.

Wannan ci gaba ne da ya buɗe sabuwar tattaunawa kan muhimmancin kasuwar hannun jari da kuma damar da take samarwa ga matasa masu son gina makoma mai ɗorewa.

Da yake sharhi kan wannan dama, Dr Salihu Lukman, Mataimakin Farfesa a University of Hafr Al Batin da ke ƙasar Saudiyya, ya ce kasuwar hannun jari na daga cikin hanyoyin da s**a fi tasiri wajen tara dukiya cikin tsari da kuma dogon lokaci.

 # # # 🚨 *NA HUKUMA: 𝐃OKIN ZAƁEN BALLON D’OR 🌕👨🏼‍⚖️*Wannan sanarwa ce da ke bayanin yadda ake zaɓen *Ballon d’Or* 🗳️*1️⃣...
12/09/2026

# # # 🚨 *NA HUKUMA: 𝐃OKIN ZAƁEN BALLON D’OR 🌕👨🏼‍⚖️*

Wannan sanarwa ce da ke bayanin yadda ake zaɓen *Ballon d’Or* 🗳️

*1️⃣ 𝐀YIKIN MUTUM GUDA*
Muhimman lokuta da s**a canza wasa su ne abin lura. Wato tasirin ɗan wasan a filin.

*2️⃣ 𝐍ASAR ƘUNGWA*
Kofunan da aka lashe da kuma yadda ɗan wasan ya kasance mai matuƙar amfani ga ƙungwarsa.

*3️⃣ 𝐀DALCI / LADABA*
Dabi’ar ɗan wasan. Dole sai ladaba, girmamawa da kyakkyawar halayya a filin wasa.

*𝐖AYE ZABINKA NA LASHE BALLON D’OR NA 2026? 🫵🏽✨*

---

Address

Kaduna State Zaria
Zaria
801222

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Hausa News paper posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share