
03/07/2025
DA DUMI-DUMI: Shigarmu Jam’iyyar ADC na wucin gadi ne nan gaba za mu canza jam'iyya –inji Malam Nasir El-Rufai
Daga A Yau
Tsohon Gwamnan Kaduna kuma jigo a tafiyar kawance ta ADC, Malam Nasir El-Rufai ya ce shigarsu jam'iyyar ADC na wucin gadi ne suna kan tattaunawa domin tsayar da jam'iyyar daya kwakkwara.
A Yau ta ruwaito El-Rufai ya ce har yanzu yana Jam'iyyarsa ta SDP hakanan shima Peter Obi har yanzu yana Labour Party (LP) basu fita ba saboda akwai zabuka masu zuwa nan gaba.
El-Rufai ya ce suna zargin Gwamnatin tarayya ta tura sojojinta cikin duka jam'iyyun da suke hadaka da su ciki har da SDP da yake ciki da NNPP da LP da ita kanta ADC, "Kwanan nan za ku ji wasu sun b***e a ADC sun tada rikici kuma Gwamnatin tarayya ce za ta daukar masu Lauyoyi su tada fitina s**e ai su jam'iyyarsu ce don haka muna nan muna neman jam'iyyar da bata da matsala ko kuma mu kirkiri sabuwar jam'iyya" inji El-Rufai
Me zaku ce?