22/10/2025
📸 YAUSHE ZA MU HANKALTA?
"An zo addininku ma an raba ku, an ce 'yan kaza ma ba Musulmi ne ba ƴan uwanku, in wani abu ya same su ba ruwanku, 'tamaman' kamar yadda suke mana, ko me ya faru sai su ce ai bai dame su ba su, saboda su a wurinsu wasu ya shafa ba su ba. To, ko kuma a zo muku da ɓangaranci; wannan ƴan ɓangare kaza ne, wancan ƴan ɓangare kaza ne, hatta koda addininku ɗaya ne sai ku yi faɗa, saboda wannan yana wannan ɓangaren, wancan yana wannan ɓangaren.
To, irin wannan ka ga an fito da salon yaƙarmu ta kowane hali ba a bar mu mun zauna lafiya ba, to amma mu kuma ana ta ɓaganniya kamar ba a san inda aka sa gaba ba, Mutane sun zama ana kaɗa su, kamar yadda ake cewa ko gawon shanu ne? Ana kaɗa su yadda aka ga dama, ba su san inda s**a sa gaba ba. Har yaushe ne za mu hankalta? Musamman ma su mahukunta da ake basu muƙami ya zama sun zama kayan faɗa da Mutanensu, har da kisa, suna kashe Mutanensu, ko ana kashe Mutanensu kowa ya yi gum da bakinsa ba ya cewa komai.
Su kuma wanda suke haddasawan su ba su ganin kun cancanta ku zama bil'Adam ko ku mallaki wani abu, ko a yi ciniki da ku, ballantana arzikin da su ke gani bizne ƙarƙashin ƙafafunmu, su suna ganin kamar dole ne su zo su ɗiba kawai kayansu ne, suna diɓan dukiya da ya kai miƙidarin 'trillions' na dala amma ko kobo ba su bayarwa, in ma da abin da suke bayarwa zubar da jini su ke, su zubar da jini su ɗebi dukiya, su abinda suke yi kenan."
(H) | 9th Zul-Ƙa'ada, 1446H – 7th July, 2025
https://www.instagram.com/intizarulmahdi