Gidan Sarautar Katsinawan Zazzau

Gidan Sarautar Katsinawan Zazzau Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Gidan Sarautar Katsinawan Zazzau, Media/News Company, Zaria.

Mun bude wannan shafine dan hadin kai, sada zumunci, yada kyawawan al'adunmu, Tunawa da iyayanmu da kakanninmu, se kuma kare mutuncin Gidan Sarautar Katsinawan Zazzau.

20/09/2025

***ALLAH YAYIMAKA BAIWA MASU YAWA***

Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah

A kullum muna Kara godema Allah da Ni'imar da yayimana, Muna rokon Allah ya jikan. Magabatanmu, Ya Allah bazamuyima butulciba, Kai ke abinda Kaso a lokacin da Kaso,

Allah ya tashemu da ANNABI MUHAMMADU S.AW da Sauran Iyayanmu baki daya Amin.

#20/09/2025.

***SHEKARA BIYAR DA RASUWARKA***A rana irin ta yau 20/09/2020 Allah yayima Mai Girma SA'IN ZAZZAU Alh. Ibrahim Umar rasu...
20/09/2025

***SHEKARA BIYAR DA RASUWARKA***

A rana irin ta yau 20/09/2020 Allah yayima Mai Girma SA'IN ZAZZAU Alh. Ibrahim Umar rasuwa,

Jikan Kasimu Dan Mallam Sambo Sarkin Zazzau,

Muna rokon Allah ya jikanka yasa kana Jannatul Firdausi da Sauran Iyayanmu baki daya Amin.

#20/09/2025.

***MARTANIN ABDULLAHI ALHASSAN***Nai posting akan Makarantar da Marigayi Mai Martaba Sarkin Zazzau Alh. (Dr) Shehu Idris...
20/09/2025

***MARTANIN ABDULLAHI ALHASSAN***

Nai posting akan Makarantar da Marigayi Mai Martaba Sarkin Zazzau Alh. (Dr) Shehu Idris CFR ya gina,

Sarkin Zazzau Shehu ya gina Makaranta guda biyu na haddan Al-Qur'ani da dayan kuma a Giwa (Mallam Abdulkarimu science secondary school Giwa),

Gashi irin da Sarki ya shuka ta tsira, ta girma har an girbe yanzu Al'umma na Amfana dashi,

Muna rokon Allah Ta'ala ya jikan Sarki da gafara da Sauran Al'ummar Musulmi baki daya Amin.

#20/09/2025.

20/09/2025

***INNALILLAHI WA INNA ILAIHIRRAJI'UN***

Hakika munyi rashin Mutumin kirki Masoyinmu kuma Mai kaunarmu,

Marigayi Mai Martaba Sarkin Zazzau Alh. (Dr) Shehu Idris CFR LLD beda buri da ya wuce yaga Al'ummarsa taci gaba,

Ya taimaki Jama'a kwarai da gaske, Muna rokon Allah ya jikanshi da Sauran Al'ummar Musulmi baki daya Amin.

#20/09/2025.

20/09/2025

***GARMA TA KARYE DA SAURAN AIKI***

Duk wanda ya rayu dakai zemaka shaidan

kunya,
Hakuri,
Amana,
Kawaici,
Gaskiya,
Zurfin tinani,
Hangen nesa,
Karamci da kyauta,

Wadannan kyawawan halayan yasa kasiye zukatan Al'umma,

Muna kara rokamaka rahama da gafara Allah a gareka da Sauran Al'ummar Musulmi baki daya Amin.

#20/09/2025.

***عِشْ مَا شِئْتَ               فَإِنَّكَ مَيِّتْوَأََحْبِبْ مَنْ شِئْتَ               فَإِنَّكَ مُفَارِقُهُ******INDA ...
20/09/2025

***عِشْ مَا شِئْتَ
فَإِنَّكَ مَيِّتْ
وَأََحْبِبْ مَنْ شِئْتَ
فَإِنَّكَ مُفَارِقُهُ***

***INDA DA RAN DA ZATA DAWWAMA DA ANNABI MUHAMMADU YA DAWWAMA***

Sunnan rayuwa itace mutuwa, duk Wanda ajalinsa yayi dole ya rasu,

A kullum Muna Tina irin halayanka da dabi'unka masu kyau ne da karamci, Rashinka Bubban koma bayane a cikin Al'umma,

Ka taimaki Jama'a, Ka taimaki marayu da masu uba, Ka Gina Makaranta biyu don koyon Al-Qur'ani da hadisi (Makarantar Hadda na Idi da na Giwa)

Al'umma sun Amfana da rayuwarka,

Muna rokon Allah Ta'ala yasa Al-Qur'ani ya ceceka da Iyayanmu Kakanninmu da Sauran Al'ummar Musulmi baki daya Amin.

#20/09/2025.

***DUK ABINDA YAYI FARKO ZEYI KARKE***Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un, duk abinda yayi farko zeyi karshe Banda Mulki ...
19/09/2025

***DUK ABINDA YAYI FARKO ZEYI KARKE***

Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un, duk abinda yayi farko zeyi karshe Banda Mulki da Sarautar Allah Ta'ala,

A rana irin ta yau 20/09/2025 muka Sama kanmu cikin razana da firgici na rashin Shugabanmu Adali Mai tausayi da kaunarmu, a koda yaushe mukan tunaka da karamci irin naka, Ka taimakemu, Ka kaunacemu, kaji kanmu, Ka kautata mana,

Muna rokon Allah Ta'ala, ya jikanka, yasa Ka huta, ya shafe kura-kuranka, yasa kana Jannatul Firdausi da Sauran Iyayanmu da Kakanninmu baki daya Amin,

#20/09/2025.

***MAI MARTABA DA WANI HAKIMINSA***Lokacin korona Jama'a ba yanayi, Mai Martaba Sarkin Zazzau bayan ya fito sai yaga Jam...
19/09/2025

***MAI MARTABA DA WANI HAKIMINSA***

Lokacin korona Jama'a ba yanayi, Mai Martaba Sarkin Zazzau bayan ya fito sai yaga Jama'a ba yawa, Sai yace a rubuta sunan duk Wanda ke wurun, Me rubutawan yasama sabani da wani a wurun sai Yaki rubuta sunansa, Bayanda Sarki ya karanta sunaye bega sunan wannan bawan Allan ba,

Sarki: ya banga sunan wane a cikiba?
Me rubuta suna: Ai ban lura dashi bane,
Sarki: a gabankafa ya gaidani,
Me rubuta suna: kaina na kasa ban luraba,
Sarki: kowa yaje a abashi buhun shinkafa 1, masara 1 da dubu 50, Amma wane da ba'a so a bashi Shi a bashi buhun shinkafa 2, masara 2 da dubu 100,

Daga cikin halin Mai Martaba Sarkin Zazzau in yaga kanama wani mugunta to kaimashi hanyar arzikine, don abinda ze bashi da banne,

Muna rokon Allah ya jikan Sarki da gafara Amin.

#19/09/2025.

***JIKOKIN AMINU SARKIN ZAZZAU***Mai Girma DANBARHIM ZAZZAU Alh. Ahmad Bashari Aminu Hakimin gundumar Sabon Gari da Abok...
19/09/2025

***JIKOKIN AMINU SARKIN ZAZZAU***

Mai Girma DANBARHIM ZAZZAU Alh. Ahmad Bashari Aminu Hakimin gundumar Sabon Gari da Abokin wasanshi Mai Girma DANMAJEN ZAZZAU Arch. Nasir Shehu Idris,

Muna rokon Allah ya biyamaku bukata ya jikan magabatanmu da gafara Amin.

#19/09/2025.

***HAKIKA BABU ABINDA YAFI RASHIN MASOYI ZAFI***Idan Ka Rasa masoyi Wanda kakeso kuma yake kaunarka kayi Rashi Mai Girma...
19/09/2025

***HAKIKA BABU ABINDA YAFI RASHIN MASOYI ZAFI***

Idan Ka Rasa masoyi Wanda kakeso kuma yake kaunarka kayi Rashi Mai Girma, Hakika Sarkin Zazzau Alh. (Dr) Shehu Idris ya kaunaci talakawansa, Ya kyautata masu, Ya taimaki marasa karfinsu da marayun cikinsu, Alkhairinsa babu inda be zagaba,

Muna rokon Allah ya jaddada rahama da gafara a gareshi da Iyayanmu, Kakanninmu da Sauran Al'ummar Musulmi baki daya Amin.

#19/09/2025.

***INNALILLAHI WA INNA ILAIHIRRAJI'UN***Allah yayima Alh. Bukar kukun Marigayi Mai Martaba Sarkin Zazzau Alh. (Dr) Shehu...
19/09/2025

***INNALILLAHI WA INNA ILAIHIRRAJI'UN***

Allah yayima Alh. Bukar kukun Marigayi Mai Martaba Sarkin Zazzau Alh. (Dr) Shehu Idris CFR, LLD rasuwa, Za'ayi Janazansa bayan Sallar Juma'ah a Fadan Zazzau.

Muna rokon Allah ya jikanshi yasa ya huta ya shafe kura-kuransa Amin.

#19/09/2025.

***SALLAR JUMA'ARSA NA KARSHE A DUNIYA***A rana irin ta yau 18/09/2020 inda akaga Marigayi Mai Martaba Sarkin Zazzau Alh...
18/09/2025

***SALLAR JUMA'ARSA NA KARSHE A DUNIYA***

A rana irin ta yau 18/09/2020 inda akaga Marigayi Mai Martaba Sarkin Zazzau Alh. (Dr) shehu Idris CFR LLD a Masallacin Juma'ah na karshe a rayuwarsa,

Saboda San Ibada Sarki baze Iya zuwa Sallah ba a kasa sai yace a kawoshi a mota,

Hakika kayi rayuwar Ibada kuma abin koyi, Muna rokon Allah ya jaddada rahama da gafara a gareka da Sauran Al'ummar Musulmi baki daya Amin.

#18/09/2025.

Address

Zaria

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Gidan Sarautar Katsinawan Zazzau posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Gidan Sarautar Katsinawan Zazzau:

Share