14/07/2025
BANYI NADAMAR GOYON BAYAN BUHARI BA
Allah Ya sani ni Datti Assalafiy sai da na sadaukar da rayuwata akan Buhari ba don komai ba sai don yakinin da nake dashi a kansa cewa mutumin kirki ne, ga kuma dalilaina
👇
Baya neman matan banza
Baya Luwadi
Baya shan giya
Baya shan sigari
Baya shan miyagun kwayoyi
Baya cultism
Baya karya
Ba mutumin banza bane
Ba dan iska bane
Ba maciyin amana bane
Ba mayaudari bane
Ba azzalumi bane
Ba maha'inci bane
Yana da kirki
Yana da kawaici
Yana da son wasa
Yana da raha
Yana da hakuri
Yana da yafiya
Yana da kawar da kai
Yana da son talakawa
Yana da tausayin talakawa
Yana son zaman lafiya
Yana da tsananin kishin Nigeria
Zai yi wahala mutum yayi aikin Soja ba'a sameshi da wa su miyagun dabi'un da na lissafa a sama ba, amma Buhari ya kubuta daga wannan
Buhari ya mulki Nigeria a Soja da farar hula amma ba'a taba kamashi da laifin satar kobo ba
Idan ka tara dukkan 'yan siyasar Nigeria, kai da dukkan al'ummar Nigeria gaba daya da wahala a samu mai kyawun hali irin na Buhari
Saboda gaskiyarsa har ana masa lakabi da mai gaskiya, sai dai ya hadu da mummunan cin amana daga wasu makarrabansa da s**a tayashi mulki
Kamar kowani dan adam, Buhari yana da nasa ajizancin da kura-kurai wanda muke fatan Allah Ya yafe masa
Yaa Allah Ka tsunduma Shugaba Buhari a cikin Aljannah Madaukakiya don rahamarKa🙏
Datti Assalafiy