18/08/2026
Copy
*ME YASA SAI DAN'UWA YA MUTU SANNAN YAKE ZAMA MAI DARAJA A IDON MU?*
Wallahi muna rayuwa ne a zamanin da *"Gawa"* ta fi "Mai *Rai"* daraja.
Wannan gaskiya ce mai daci wacce kusan dukanmu muna da laifi a ciki:
1. *Lissafin Kudi:*
Yana raye, ya tambaye ka *₦2,000* na *Magani* ko na *Abinci,* ka ce: "Gaskiya babu kudi, abubuwa sun sha kai."
Amma ranar da ya mutu... Zaka fidda *₦50,000* ayi *Cefane* ayi abincin sadaka, a sayi *Likkafani* mai tsada.
*Tambaya* ta: Me yasa baka ciyar da cikin da yake jin yunwa ba, sai cikin da ya riga ya daina aiki ka ke son ciyar wa?
3. *Lissafin Lokaci:*
Yana raye, yana kiran ka a waya, kana kallo kaki dauka. Ko ka ce zan kira shi anjima har shekara ta zagayo.
Amma ranar da aka ce ya mutu zaaka kashe Data ta *₦5,000* wajen dora hotunan sa a *Status, *Facebook*, da *Instagram* kana rubuta dogon bayani: *"My friend,my brother you left me too soon 😭".*
*Maganar Gaskiya,* Mamaci baya hawa WhatsApp Status. Mamaci baya Karanta Facebook Comment. lokacin da yake bukatar jin muryarka, ka yi shiru.
3. *Lissafin Yabo:*
Yana raye, baka taba gaya masa ina alfahari da kai ba.
Amma a wajen jana'izarsa, kowa yana bada labarin Shi mutumin kirki ne.
Me zai hana mu kyautata masu suna raye don su ji dadi?
*Dan Allah*, mu daina *Soyayyar Kabari.*
Idan kana son mutum, gaya masa yanzu.
Idan kana da abin da zaka taimaka masa, bashi yanzu yana raye.
*Buhu guda daya na shinkafa* da zaka bashi yaci yaji dadi yau, Wallahi yafi *Shanu 5* da zaka yanka ranar *Mutuwarsa.*
Kada ka jira sai sun zama *"Hoton Status"* Mai dauke da *RIP* sannan ka gane muhimmancinsu.
*Yaa Allah Ka yafe mana kurakuranmu ka bamu ikon kyautatawa* *yan'uwanmu da abokanmu suna raye.*
*Kada sai mun rasa su sannan mu gane darajarsu.