
01/05/2025
Ya yi arba da wanda ya yi kidinafin din su a harin jirgin kasa na Kaduna, amma ya kyale shi
In kai ne yaya za ka yi?
Daya daga cikin wadanda aka sace daga jirgin kasa a shekarar 2022, ya bayyana yadda ya yi magana da daya daga cikin 'yan bindigar da s**a sace shi a wani masallaci a jihar Kaduna.
A cikin wata hira da ya yi da Daily Trust, Comrade M. Muhammad, wanda ya ci karo da daya daga cikin wadanda s**a sace shi a masallaci, ya ba da labarin abin da ya faru a tsawon sa’ar da s**a yi suna magana.
“Da gaske ne cewa na ga mutumin nan Abubakar a Masallaci k**ar yadda na buga a shafina na sada zumunta. A gaskiya ya yi mamakin gani na, amma na yi masa murmushi, wanda hakan ya sa ya samu kwanciyar hankali.”
“Muka fita waje, ya gaya mani cewa ya tuba yanzu, kuma yana yin hayan mashin acaba ne. Ya kuma gaya mani cewa sojoji sun kashe daya daga cikin shugabanninsu, sanannen dan ta’addan nan, Baba Adamu, kuma na yi farin cikin jin labarin kisan,” in ji shi.
Kwamared din ya kara da cewa, ya gafarta wa dan bindigar da aka fi sani da Abubakar domin akwai wadanda ba su tsira daga harin ba, amma shi ya tsira.
“Wasu na iya yin mamakin cewa na gafarta masa, na bar shi ya tafi, domin tun kafin in gan shi a ranar, na riga na gafarta musu,” in ji shi.
Muhammad, duk da haka, ya ce ba zai gafarta wa gwamnati ba saboda abin da ya faru da shi a daren 28 ga Maris, 2022, “domin an kai wa jirgin harin ne saboda sakaci na gwamnati.”
Ya ce, gwamnati ta sami gargadin cewa za a iya kai wa jirgin harin, amma ba ta yi wani abu don hana aukuwar harin ba.
Wanda aka azabtar a kidinafin din, ya kuma zargi gwamnati da yin watsi da su bayan sun samu ‘yanci, inda ya ce su ne s**a biya kuɗin jinyar da s**a yi a bayan da s**a kubuta.
“Mun kwana 196, wato watanni 7, a zaman talala, bayan an sake mu, gwamnati ba ta yi mana komai ba face maganin drip da rigakafin zazzabin cizon sauro da ta ba mu.”
“Da yawa daga cikin mu, ciki har da ni, mun sha fama da tashin hankalin firgici, kuma dole ni sai da na je asibitin Neo Psychiatric tsawon watanni don neman magani ba tare da tallafin gwamnati ba.”
In za a iya tunawa a ranar 28 ga Maris, 2022, an kai wa wani jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna hari a Katari, Kaduna, kusan minti 15 kafin ya isa wurin da zai tsaya.
‘Yan bindiga sun sace daruruwan fasinjoji yayin da s**a kashe wasu ko kuma s**a jikkata su, bayan sun tayar da bam a jirgin.
Jirgin ya taso daga tashar Idu ta Abuja da karfe 6 na yamma, kuma ya k**ata ya isa tashar jirgin kasa ta Rigasa a Kaduna da karfe 8 na yamma, amma bai kai inda aka tsara ba.