12/05/2025
*JIBWIS KADUNA TAYI TARON MAJALISAR ZARTARWA*
A yau Lahadi 11/5/2025 dai-dai da 14/zul-Q/1446AH.
Kungiyar jama'atu izalatil bid'a wa ikamatus Sunnah (JIBWIS) Jahar kaduna, ta gudanar da taron majalisar zartarwa kamar yanda ta saba. Taron wada sheikh Abdulhamid Muhammad Mataimakin Shugaban Kungiyar na jahar Kaduna ya jagoranta.
Taron yayi dubine bisaga nasaronin da kwamitocin marayu Dana tattara fatin layya s**a samo abara da kuma yanda Za'ayi karacin Nasara abana.
Taron ya gudana ne ababban masallacin juma'a na kusa da zaria total dake Sabon garin, zaria.
Taron ya samu halartar Alh. Adamu Ibrahim Shugaban Kungiyar ta Jahar kaduna, sheikh Abdullah Aliyu telex, Shugaban majalisar malamai na Jahar kaduna, Mal Auwal Muhammad Daraktan Agaji na jahar kaduna, Alh. Aliyu janfalan sakataren Kungiyar na jahar kaduna shuwagabannin kungiya, Shugabanin majalisar malamai, shuwagabannin majalisar Agaji na kananan hukumomi 23 dake fadin jahar kaduna.
ALLAH ta'ala yasa kowa ya koma gidan sa lafiya.
Mas'ud Bala chikaji. Chairman jibwis social media Sabon garin.