04/10/2025
NASARARKA NA GA TSARKINTA (2)...
ME YASA YA ZAMA WAJIBI, MUHIMMANTAR DA TSARKAKE NAFS (RUHI)?...
Abin damuwa a wannan zamanin namu mafi yawan al’umma mun narke cikin gafala mai zurfi, mun jahilci ƙima da muhimmancin tsarkake Nafsu da Rahinmu. A lokacin da wani cikinmu idan ya yi rashin lafiya ya kan garzaya zuwa ga likita, sannan ya muhimmantar da shan magani da kiyaye ƙa’idojin da likitan nan ya gindaya masa dan ganin ya samu lafiya, kuma wannan sa’ayin nasa duka a kan rashin lafiyar jiki ne, ba zai taɓa samun sukuni ba har sai ya ji ya warke sumul.
Amma abin mamaki ita kuma rashin lafiyar Ruhinmu da zukatanmu sai ka ga mun gafala wajan nema masu magani, mun yi ko oho. A lokacin da cutukan ruhinmu ke zamar mana alaƙaƙai da barazana ga makomarmu ta asali, mun manta cewa magance waɗannan cututtukan kuma shi ne zai kai mu ga jin ɗanɗanon haƙiƙar natsuwa wadda za ta sada mu zuwa ga hanyar Allah, a ƙarshe kuma ta kai mu zuwa ga tsira a ranar lahira ta har abada.
ALLAH YA AZURTA MU DA NI’IMOMI BIYU DON SHIRIYARMU...
Lallai hadafin halittar mutum shi ne bauta ga Allah Ta’ala (ibadarsa da gaskiya) domin shi Allah (S.W.T) bai yi wata halitta ba haka kawai ba tare da hadafi ba, shi yasa ma sai ya bayyana hakan a littafinsa mai tsarki cewa:
”وما خلقتُ الجنَّ والإنسَ إلاّ ليعبدون“
“Ban halicci Aljani da Mutum ba, face sai dan bauta.”
Tunda Allah (S.W.T) ya halicci mutum... dan bauta ne, kana tunanin zai bar shi ne kawai sakaka ba tare da mai shiryar da shi zuwa ga wannan bautar ba, wadda aka yi shi dan ita? Amsa shi ne; a’a. To dan haka sai Allah Ta’ala ya ƙago mana abu biyu; su ne: Na (1) Hankali wanda shi ne mai rarrabe tsakanin alkhairi da sharri. Na (2) kuma ya aiko mana Annabawa da Mursalai dan su haska mana su k**a hannayenmu zuwa ga shiriya, su nuna mana ayyukan Shaiɗan da kuma tanajin azabar da aka yi wa wanda ya bishi (dan mu guje masa).
Har wayau Annabawan nan su za su gwada mana haƙiƙanin bautar Allah da kuma tanadinsa na rahama ga waɗanda s**a bi turbarsa. Kenan su Annabawa su ne za su gwada wa mutane ya ake bautar Allah sannan duk wani abu da hankali ya kasa isa gare shi na sanin Allah su ne za su sada mutum zuwa gare shi, inda kuma hankali ya nufa (na ɓata) zuwa ga shaiɗan su ne za su keɓo shi, saboda shi hankali yana da iyaka, amma su Annabawa suna shiryarwa ne ta hanyar Wahayi.
Shi yasa Imam Ja’afar As-sadiq yake cewa: “يا هشام إن للٌه على الناس حجتين: حجة ظاهرة وحجة باطنة، فأما الباطنة فالرسل والأنبياء والأئمة. وأما الباطنة فالعقول”
“Ya Hisham (Sahabin Imam) Lallai Allah yana da hujjoji biyu a kan mutane, Hujja ta Zahiri da Hujja ta baɗini. Ta zahirin ita ce: Annabawa da Mursalai da A’ummatu Ahlulbaiti (A.S). Hujja ta baɗini kuma ita ce: Hankali.
(الكافي؛ ج1، ص16)
DOLE KA NEMI MALAMIN DA ZAI RIƘA SHIRYAR DA KAI...
A Kan shi za mu tashi a rubutu na gaba Insha Allah. Allah Ka yi mana taufiƙi da fatan za mu yi wunin juma’a lafiya.
Daga Khadiminku:
— Ibraheem Bin Yaqub
(Abu Muhseen)