
25/10/2023
Idan muka shiga tsanani da takura na rayuwa sau da dama sai mu rinka gani ko daura laifin hakan akan shuwagabaninmu, sai mu manta da namu laifukan, muna ganinsu kamar wasu kananu ne, ko kuma su namu laifukan kamar ba zasu iya jawo wani irin musiba wacce zata iya zuwa ta damemu ta damu wasun mu ba....!!!
Ban ce shuwagabaninmu basu laifi akan wasu abubuwan dake faruwa damu damu, domin su a karan kansu suna da daman da zasu hana faruwan wasu abubuwan da dama.
Kuma ina nufin shugabaninmu ta kawone irin fuska ne, ya-Allah Ζ΄an siyasa, ko mallaman Addini ko mallaman makarantu, Shuwagabanni a wajen aiki ko wajen Sana'a, Iyaye da sauran duk wanda zai iya amsa sunan Shugaba a kowane irin mataki yake.
Mu duba laifukanmu mu gyara, mu cigaba da addu'a akan Allah ya kawo mana saukin wannan yayin rayuwa da muke, In sha Allahu zamu ga Daidai a cikin kankanin lokaci.
Allah mun tuba.π€²πΌ