Kasar Zazzau a Jiya Da Yau

  • Home
  • Kasar Zazzau a Jiya Da Yau

Kasar Zazzau a Jiya Da Yau Domin Sanin Tarihin Sarakunmu, Malamanmu, Manyan Gidajenmu, Yan siyasan mu na da dana yanzu na Arewa

Inalillahi wa ina ilaihi raji'un. Allah ya  yi wa Manama SA'ADATU LAWAL('YA). Da ke gidan goro bakin fadaman sarki kaura...
17/07/2025

Inalillahi wa ina ilaihi raji'un. Allah ya yi wa Manama SA'ADATU LAWAL('YA). Da ke gidan goro bakin fadaman sarki kaura . Mahaifiyan Sarki jaman. Zana'iza karfe 4:30pm in Allah ya kaima. Allah ya jikanta da rahama da dukkan musulmi baki daya.

TARON DUNIYA NA KARIN ILIMI A KWALLEJIN HORAS DA KANANAN HAFSOSHIN SOJA NA NDADA safiyan yau Mai Martaba Sarkin Zazzau, ...
17/07/2025

TARON DUNIYA NA KARIN ILIMI A KWALLEJIN HORAS DA KANANAN HAFSOSHIN SOJA NA NDA

DA safiyan yau Mai Martaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, CFR yana halartan Taro a Kwallejin Horas Da Hafsoshin Soja na NDA a Garin Kaduna. Da isarsa, Mai Martaba Sarkin Zazzau ya duba Faretin da aka gudanar domin karrama shi.

17/07/2025

TARON DUNIYA NA KARIN ILIMI A KWALLEJIN HORAS DA KANANAN HAFSOSHIN SOJA NA NDA

DA safiyan yau Mai Martaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, CFR yana halartan Taro a Kwallejin Horas Da Hafsoshin Soja na NDA a Garin Kaduna. Da isarsa, Mai Martaba Sarkin Zazzau ya duba Faretin da aka gudanar domin karrama shi.

Wannan Shi Ne Marigayi Alh Suleiman (Baban Dada) Gidan Doka Anguwan Karfe Bakin Kasuwa Zaria City. Muna Adu'an Allah Ya ...
17/07/2025

Wannan Shi Ne Marigayi Alh Suleiman (Baban Dada) Gidan Doka Anguwan Karfe Bakin Kasuwa Zaria City. Muna Adu'an Allah Ya Jikan Shi Yayi Mishi Rahama Yasa Yana Kyakyawan Matsayi Ya Gafarta Mishi Ya Kyautata Makwaci Shi Ya Jikan Magabatan Mu Bakidaya.

MAZAN JIYA Marigayi Maimartaba Sarkin Zazzau Alh Dr Shehu Idris CFR Tare Da Marigayi Tsohon Shugaban Kasa Nigerian Muham...
17/07/2025

MAZAN JIYA

Marigayi Maimartaba Sarkin Zazzau Alh Dr Shehu Idris CFR Tare Da Marigayi Tsohon Shugaban Kasa Nigerian Muhammadu Buhari. Muna Adu'an Allah Ya Jikan Magabatan Mu Bakidaya Yayi Musu Rahama.

Innalillahi Wa'inna IlaiHi Raji'unAllah Yayi wa Zainab (Walida) rasuwa. Walida 'Ya ce ga Alhaji Usman Na'ibi (Shehu), na...
17/07/2025

Innalillahi Wa'inna IlaiHi Raji'un
Allah Yayi wa Zainab (Walida) rasuwa. Walida 'Ya ce ga Alhaji Usman Na'ibi (Shehu), na Gidan Na'ibin Zazzau Anguwan Kwarbai. Ta rasu cikin daren jiya, kwana takwas da haihuwar jariri. Za a gudanar da Jana'izan Marigaÿya Zainab da karfe 10:00 na safiyar yau Alhamis, a Rimin Doko, Bayan makaranta, Kaura Zaria.

Allah Ya gafarta mata, Ya yafe laifukanta.

17/07/2025

Aysha Ahmad Mohammad

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM ZANCEN ALLAH MADAUKAKIN SARKI DA SALIHAN BAYINSA A ALJANNAH:Abu Sa'eed Al Khudriy (R.T.A) yac...
17/07/2025

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM

ZANCEN ALLAH MADAUKAKIN SARKI DA SALIHAN BAYINSA A ALJANNAH:

Abu Sa'eed Al Khudriy (R.T.A) yace Manzon Allah (S.A.W) yace :

"Allah madaukakin Sarki zaice wa 'yan Aljannah : "YA KU 'YAN ALJANNAH!".

Zasu ce "Labbaika (Amsawarka) Ya Ubangiji!! kuma dukkan arziki da dacewa suna gareka!!".

Sai yace musu "Shin kun yarda? (da sakamakon da aka baku).

Sai s**e "Meke garemu da bazamu yarda ba! Alhali gashi ka bamu abinda baka ba ma kowa ba, daga cikin halittunka!".

Sai yace "ZAN BAKU ABINDA YAFI WANNAN".

Sai s**e "To wanne bau ne kuwa yafi wannan?".

Sai yace musu "NA BAKU YARDATA, BAZAN TA'BA YIN FUSHI DAKU BA, HAR ABADA".

(Hadisi na 6549 cikin Sahihul Bukhariy).

Allah mai girma nake roko ya sanyani daku da iyayenmu da 'yan uwa da iyalanmu baki daya cikin wadanda zasuyi wannan zancen da Allah (Jalla jalaluhu) Bijahi Rasulillahi (S.A.W)🤲🤲🤲

ZIYARAN FADAKARWATAWAGA daga GIDAUNIYAR CHIGARI tare da Hadin Guiwan abokanin huldansu bisa jagorancin Dokta Abdulsalam ...
16/07/2025

ZIYARAN FADAKARWA

TAWAGA daga GIDAUNIYAR CHIGARI tare da Hadin Guiwan abokanin huldansu bisa jagorancin Dokta Abdulsalam Ahmed s**a gabatar da ziyaran girmamawa tare da gabatar da bayanai ga Mai Martaba Sarkin Zazzau Malam Ahmed Nuhu Bamalli, CFR bisa shirin inganta hanyoyin bayar da rigakafi ga Yara kanana.

SHEKARU 6 DA RASUWAN MAHAIFIN MAKARFI Yau Ne Mahafin Tsohon Gwamnan Jahar Kaduna Sanata Ahmed Muhammad Makarfi Ke Cika S...
16/07/2025

SHEKARU 6 DA RASUWAN MAHAIFIN MAKARFI

Yau Ne Mahafin Tsohon Gwamnan Jahar Kaduna Sanata Ahmed Muhammad Makarfi Ke Cika Shekaru Shida Da Rasuwa. Mai Girma Majidadi Zazzau Muhammad Na'iya. Muna Adu'an Allah Ya Jikan Shi Yayi Mishi Rahama Yasa Yana Kyakyawan Matsayi.

CI GABA DA DAUKAN DARASI KOYON KARATUN AL'KURANI A Cibiyan Nazari da Karrattukan Addinin Musulunci na Usman Danfodiyo wa...
16/07/2025

CI GABA DA DAUKAN DARASI KOYON KARATUN AL'KURANI

A Cibiyan Nazari da Karrattukan Addinin Musulunci na Usman Danfodiyo waṅda ke Fadan Zazzau a yau, Malam Ahmed Tanimu ya ci gaba da Koyar da Yadda ake Karatun Al'kurani Maì Girma.

Wani Gida Wannan A Cikin Garin Zariya Kuma A Wani Anguwan Yake?
16/07/2025

Wani Gida Wannan A Cikin Garin Zariya Kuma A Wani Anguwan Yake?

Address


Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Kasar Zazzau a Jiya Da Yau posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Kasar Zazzau a Jiya Da Yau:

Shortcuts

  • Address
  • Telephone
  • Alerts
  • Contact The Business
  • Claim ownership or report listing
  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share