Salim Aliyu Sunnah

Salim Aliyu Sunnah Alhmdllh

Inna lillahi wa'inna ilaihi rajiuna.Allah ya yiwa Shugaban majalisar malamai na Zuru local government ta JIBWIS Nat HQ J...
17/04/2026

Inna lillahi wa'inna ilaihi rajiuna.
Allah ya yiwa Shugaban majalisar malamai na Zuru local government ta JIBWIS Nat HQ Jos rasuwa, za'a yi jana'izar sa bayan sallar juma'a a masallacin juma'a na daya in sha Allah a yau juma'a 17/4/2026.
Muna rokon Allah ya jikan sa da rahama in ta mu ta zo Allah ya sa mu cika da cikakken imani.

JADAWALIN MUSABAƘA NA SHEKARA TA 1447AH/2026CEJami'in Kula da Gasar Karatun Alkur'ani Mai Girma (Coordinator) Karkashin ...
28/03/2026

JADAWALIN MUSABAƘA NA SHEKARA TA 1447AH/2026CE

Jami'in Kula da Gasar Karatun Alkur'ani Mai Girma (Coordinator) Karkashin Ƙungiyar Jama'atu Izaltil Bid'ah Wa Iƙamatis Sunnah ta Ƙaramar Hukumar Mulki ta Zuru Jahar Kebbi wato Ustaz Kabiru Aliyu , yana Farin cikin Shaida wa Al'umma Musamman Shugabannin Rassa, Alƙalan Musabaƙa, Ƴan Takara da kuma sauran Jama'a cewa, an Fitar da Tsarin Jadawali (Time Table) na Gasar Karatun Al-Qur'ani Mai Girma ta Rassa na wannan Shekara ta 1447AH/2026CE.
A wannan Shekara ta Bana, Kimanin Rassa Goma Sha Tara (19) ne za su Gudanar da Musabaƙar, wadda za a Fara daga Ranar 31/03/ 2026 zuwa 30/05/2026.

Allah Ya ba da ikon Gudanar da wannan Aiki cikin Nasara, amin.

SANARWAR📢📢📢📢 A MADADIN SHUGABAN KWAMITIN WA'AZIN MATASA NA KUNGIYAR JIBWIS JOS RESHEN JIHAR SOKOTO MAL. MUKHTAR ALIYU YA...
28/02/2026

SANARWAR
📢📢📢📢

A MADADIN SHUGABAN KWAMITIN WA'AZIN MATASA NA KUNGIYAR JIBWIS JOS RESHEN JIHAR SOKOTO MAL. MUKHTAR ALIYU YABO, NA FARIN CIKIN GAYYATAR AL'UMMAR MUSULMI NA CIKI DA WAJEN SOKOTO ZUWA WAJEN GAGARUMAR MUHADARA TA JIHA WADDA SHEIKH ABUBAKAR USMAN MABERA SHUGABAN MAJALISAR MALAMAI NA JIHAR SOKOTO KUMA WAKILIN SHEIKH MUHD SANI YAHAYA JINGIR A JIHAR SOKOTO ZAI GABATAR.

ZATA KASANCE KAMAR HAKA:-

RANA:-LAHADI 29-2-2026

WURI:-MASALLACIN JUMUA NA MUAZU BIN JABAL DAKE ANGUWAR NAKASARI A NAN CIKIN BIRNIN SOKOTO.

LOKACI:-11:00 NA SAFE

ALLAH YA BADA IKON ZUWA AMEEEEEN

JIMC SOKOTO STATE

MALJAUS SUNNAH ABDULLAHI IBINI ABBAS LITTAH FIZUL QUR ANIL KARIM ZANGO ZURU KEBBI STATE wannan makaranta mai adreshi Sam...
14/02/2026

MALJAUS SUNNAH ABDULLAHI IBINI ABBAS LITTAH FIZUL QUR ANIL KARIM ZANGO ZURU KEBBI STATE

wannan makaranta mai adreshi Sama tana farin cikin gayyatar Yan uwa Al ummar musulmi

zuwa wajen gagarumar walima wadda tashirya
Domin komawa sabuwar makaranta da wani bawan Allah yagina mata

Dakuma masallaci da aka sabunta

Wannan makaranta mai albarka tashare shekaru Masu yawa batada muhallin karatu isasshe

cikin ikon Allah
Saiga wani bawan Allah yadauki nauyin Gina wannan makaranta bayan daya daga cikin manyan jagororin makarantar yabada hili

Wayannan bayun Allah das**ayi wannan aikin Muna rokon Allah yasaka masu da alkhairi

Abun mamaki abun ban sha,awa game da wannan lamarin shine

Shi Wanda yadauki nauyin Gina wannan makaranta har yanzu Bai bayyana kanshi ba illa kawai jagoririnsa akasani akan wannan aikin

Wannan abun yakamata Masu kudinmu dama talakawa muyi koyi da wannan bawan Allah
Domin wannan sadaka tafi kowace sadaka lada a wujin Allah

Yadauki nauyin Gina wannan makaranta tundaga condition har izuwa rupping kwano tareda sa gate Kai kace gidan wani attajireni ga soler yasa a cikin wannan makaranta dakuma yin wayarin na zamani na wutar lantarki

Kai maddalla da irin wayannan mutane Masu zuciyar yi don Allah

Walimar zata kasance kamar haka

RANA
ASSABAR_15/02/2026

LOKACI_ DA MISALIN KARFE 9:00 NA SAFE

WURI_HARABAR MASALLACIN MAKARANTAR KUSA DA GIDAN MLM ALIYU S FENTER BEHIND DANGA PRIMARY SCHOOL

Allah yabada ikon zuwa ameen
✍️ ABU SUMAYYA

09/02/2026

All Invited 🤝 Masarautar Zuru Kebbi State

INNALILLAHI WA'INNA ILAIHIRRAJI'UN INNALILLAHI WA'INNA ILAIHIRRAJI'UN INNALILLAHI WA'INNA ILAIHIRRAJI'UN😭😭😭Allah Yayiwa ...
10/01/2026

INNALILLAHI WA'INNA ILAIHIRRAJI'UN INNALILLAHI WA'INNA ILAIHIRRAJI'UN INNALILLAHI WA'INNA ILAIHIRRAJI'UN😭😭😭

Allah Yayiwa dan takarar Musabaqa na Jihar Bauchi wanda Yayi Izu 60 da Ruwayat

Allah Ubangiji Muke Roko Yayimasa Rahama yasa Aljannace Makomarsa damu baki daya

Hotunan Juma'a Daga Jibwis Nhqts Jo's Mosque 002 Zuru Kebbi State Nigeria
09/01/2026

Hotunan Juma'a Daga Jibwis Nhqts Jo's Mosque 002 Zuru Kebbi State Nigeria

•Sheikh Jingir Ya Sake Taron Laraba, Ya Jagoranci Tsara Sabbin Ayyuka na Ci Gaban Kungiya•A yau Laraba, kamar yadda aka ...
07/01/2026

•Sheikh Jingir Ya Sake Taron Laraba, Ya Jagoranci Tsara Sabbin Ayyuka na Ci Gaban Kungiya

•A yau Laraba, kamar yadda aka saba a ko wane sati, Khalipha Ash-Sheikh Muhammadu Sani Yahaya Jingir ya sake tara jama'arsa a babban zauren tattaunawa domin ji daga gare su da kuma tsara sabbin ayyuka na ci gaban ƙungiyar.

•Taron, wanda ya gudana cike da natsuwa da nutsuwar malamai da almajirai, ya kasance wata dama ta musayar ra'ayi, nazari kan ayyukan da s**a gabata da kuma fitar da sabbin dabaru da zasu ƙara ƙarfafa tafiyar Ahlussunnah a faɗin ƙasa.

•Taron na yau ya kuma ƙunshi gabatar da bayanai daga manyan shugabanni da masu ruwa da tsaki, inda aka tattauna batutuwan da s**a shafi tsare-tsare, shirye-shiryen agaji, da kuma sabbin matakan wanzar da ilimi da tarbiyya tsakanin mambobi.

•Kamar yadda ya saba faruwa a kowace Laraba, taron ya kasance cike da albarka, fahimtar juna, da kuma kyakkyawar mu’amala tsakanin jagora da mabiyansa.

•A ƙarshe, Sheikh Jingir ya yi addu’ar Allah ya ƙara ɗaukaka aikin, ya sa alkhairi ya yawaita .

SURAJ JOURNALISt ✍️

Sanarwa! 📢📢📢📢📢📢 *WA'AZIN  JIHA TARE DA MUHADARA TA KWAMITIN WA'AZIN MATASA A MATAKI NA JIHA A CIKIN BIRNIN SOKOTO* Kungi...
07/01/2026

Sanarwa!
📢📢📢📢📢📢

*WA'AZIN JIHA TARE DA MUHADARA TA KWAMITIN WA'AZIN MATASA A MATAKI NA JIHA A CIKIN BIRNIN SOKOTO*

Kungiyar Jama'atu Izalatil Bid'ah Wa'ikamatis sunnah Reshen Jihar Sakkwato, mai hedikwata ta kasa a birnin Jos.

Wadda Take Karkashin Jagorancin
Shugaban Majalisar Malamai Na Jiha, *Sheikh Abubakar usman mabera* da shugaban kwamitin Wa'azin matasa na jiha

Na Farin Cikin Gayyatar Shugabannin malamai, shugabannin gudanarwa na dukkanin Kananan Hukumomi, Rundunar aikin agaji, shugabannin matasa da dukkanin Kwamitoci Na Kungiyar da ilahirin al'ummar musulmi na ciki da wajen sokoto, zuwa Wajen Gagarumin Wa'azin jiha tare da muhadara ta kwamitin waazin matasa a mataki na jiha wanda zai kasance Kamar Haka:-

*WA'AZI*

Rana: *Jumu'a* 9/1/2026.

Wuri:- masallacin Alhaji Bashiru Mai albasa dake shiyar gidan igwai a cikin karamar hukumar mulkin Sokoto ta arewa.

Lokaci :- 9:00pm

*MUHADARA*

Rana:- Assabar 10-1-2026

Wuri:- Babban masallacin Jumu'a na malam Buhari dan shehu dake cikin karamar hukumar mulkin Sokoto ta kudu

Lokaci:- 10:00 am

*Malamai masu Wa'azi ranar Jumu'a sun hada da* :-

Sheikh Abubakar Usman mabera

Sheikh Muhd Yusuf kaura mai Shafi

Sheikh Khamisu Shuaibu Ungushi

Prof. Mansur Saeed

Prof. C.U Aliyu

Imam Yusuf Yahaya Alibawa

Ustaz Bello Dan galadima Tambuwal

Ustaz Bakir Abubakar Gulma

Ustaz yahuza Gidan Auta

Ustaz Usman muhd Giyawa

Ustaz Abdulkarim Maliki

Ustaz Umar Buhari Koyo

Ustaz Umar Muhd Darhela

Ustaz Adamu Gidan Buwai

Ustaz Abubakar Abubakar Jabo

Ustaz Ahmad Bayaro gwadabawa

Ustaz lauwali yar didi

Dr. Murtala Ibrahim Gudun

Ustaz Aminu Muhd Kilgori

Ustaz Saminu Bello

Ustaz Badamasi Gidan bedu

Ustaz Abubakar A Manigi

Ustaz Nafi'u Abdullahi

Ustaz Abubakar Aliyu Tambuwal

Ustaz Aliyu Bello Kalambaina

Ustaz Malami Ibrahim Tambuwal

Alarammomi sun hada da :-

Hafiz Abdullahi Sulaiman Shinkafi

Hafiz Shuaibu Umar

Hafiz Chika Altine Tambuwal

Hafiz Khadi dan Jega

Hafiz zaidu Umar Alkanci

Hafiz Zakariya'u Muhd Giron masa

Hafiz Bashar yahaya Sarda

Hafiz Haruna Gidan Buwai

Hafiz Fodio Saeed

Hafiz Ilyasu Abubakar

Hafiz Yusuf Umar

Da sauransu Alarammomi

Allah ya bada ikon zuwa, ameeeeen.

JIMC SOKOTO STATE

26/12/2025

Address

Zango Area Zuru Local Government
Zuru
021

Telephone

+2348148246560

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Salim Aliyu Sunnah posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Salim Aliyu Sunnah:

Share