
23/07/2025
Akwai Mutane Da Yawa, Amma Irinsu Murtala Maiyara Kalilan Ne. Mutum Mai Zuciya Mai Tsabta, Jajirtacce, Mai Kishin Al’umma Da Kyakkyawan Fata Ga Kowa.
Oga Mai Yara Bai Tsaya Jiran A Yaba Masa Kafin Ya Taimaka Ba.
Rayuwarsa Cike Take Da Sadaukarwa, Aiki Tukuru Da Ƙoƙarin Ciyar Da Al'umma Gaba – Ko Da Ta Hanyar Sana'a...
Alh Murtala Mutum Ne Da Idan Ka Sadu Da Shi, Ka San Ka Sadu Da Wanda Ya San Darajar Mutane. Bai Ɗauki Kowa A Banza Ba, Kuma Ba Ya Jin Nauyin Tashi Don Ya Ba Da Gudunmawa A Lokacin Da Ya Dace.
Muna Taya Ka Murna Da Fatan Allah Ya Ci Gaba Da Kara Maka Basira, Lafiya, Da Haske A Duk Inda Kake. Irinka Su Ake Bukata A Yau – Masu Faɗa Da Aiki, Ba Faɗa Da Surutu Ba!
Nagode...
Abdullahi Umar Danyale