Palestine Ayau

Palestine Ayau Domin Abinda da ya shafi Falasɗinawa da Fallasa Laifukan Ta'addancin Haramtacciyar ƙasar Isra'ila

Ma'aikatar Lafiya ta falasɗinu ta sanarda cewa:- A cikin sa'o'i 24 da s**a gabata an samu shahidai 100 a Gaza a cikinsu ...
07/08/2025

Ma'aikatar Lafiya ta falasɗinu ta sanarda cewa:- A cikin sa'o'i 24 da s**a gabata an samu shahidai 100 a Gaza a cikinsu akwai 2 waɗanda s**a warke tare da samun ƙarin jikkatattu 603 sakamakon hare-haren haramtacciyar kasar Isra'ila.

Daga 7 ga watan Oktoban shekarar 2023 zuwa yau haramtacciyar kasar Isra'ila ta shahadatar da Falasɗinawa 61,258 tare da jikakkatu 152,045.

-Taekwond Ameen
Al-ummar Palestine Ayau | ABS Radio

Akwai adadin sojojin Haramtacicyar kasar Isra'ila dubu 80 da s**a jikkata sakamakon farmaki da kwanton ɓaunar da dakarun...
06/08/2025

Akwai adadin sojojin Haramtacicyar kasar Isra'ila dubu 80 da s**a jikkata sakamakon farmaki da kwanton ɓaunar da dakarun gwagwarmayar Falasɗinu ke yi musu a Gaza.

A cikinsu akwai kimanin dubu 26 da suke da matsalar taɓin ƙwaƙwalwa.

-Taekwond Ameen
-ABS Radio | Palestine Ayau

Sabbin hotunan zirin Gaza, wanda Hare-haren Haramtacciyar Kasar Isra'ila ta maishe su buragutsai a cigaba da kisan kiyas...
04/08/2025

Sabbin hotunan zirin Gaza, wanda Hare-haren Haramtacciyar Kasar Isra'ila ta maishe su buragutsai a cigaba da kisan kiyashin raunana a sama da kwanaki 660.

-Taekwond Ameen

Wata majiyar Labarai ta shaidawa gidan talabijin na AlJazeera cewa:- A Wunin yau Hare-haren Haramtacciyar Kasar Isra'ila...
03/08/2025

Wata majiyar Labarai ta shaidawa gidan talabijin na AlJazeera cewa:- A Wunin yau Hare-haren Haramtacciyar Kasar Isra'ila kan Raunana Falasɗinu ya kashe falasɗinawa 79, a cikinsu akwai adadin 41 da waɗanda kashe a a wajen karɓar kayan agaji.

Palestine Ayau | ABS Radio

A yau Juma'a Miliyoyin Yamanawa sun sake Bayyana a kan tituna a birnin Sana'a kamar kowane sati na nuna goyon bayansu ga...
01/08/2025

A yau Juma'a Miliyoyin Yamanawa sun sake Bayyana a kan tituna a birnin Sana'a kamar kowane sati na nuna goyon bayansu ga raunanan Falasɗinu tare da Allah wadai da kisan kiyashin HKI a Gaza.

-Taekwond Ameen
ABS Radio

Daga watan Mayun da ya gabata, akwai aƙalla sama da Falasɗinawa 1,373 ne hare-haren haramtacciyar kasar Isra'ila ya kash...
01/08/2025

Daga watan Mayun da ya gabata, akwai aƙalla sama da Falasɗinawa 1,373 ne hare-haren haramtacciyar kasar Isra'ila ya kashe a yayin karɓar kayan agaji a Gaza.

-Taekwond Al'ameen
ABS Radio | Palestine Ayau

A cikin Wani bidiyo da Dakarun Gwagwarmayar Falasɗinu s**a wallafa na wani kamammen sojan Haramtacciyar Kasar Isra'ila i...
31/07/2025

A cikin Wani bidiyo da Dakarun Gwagwarmayar Falasɗinu s**a wallafa na wani kamammen sojan Haramtacciyar Kasar Isra'ila inda ya aika saƙo ga Al-umma tare da Gomnatin Haramtacicyar kasar Isra'ila.
Daga cikin Kalaman nasa ya faɗi cewa:-

1. Ba na ci ko sha - ina fama da matsanancin yunwa, wanda zai iya sawa na mutu. Da fatan za a kawo abinci; Ina tsoron na bar Gaza ba tare da rai ba.
2. An hana mu abinci saboda aikin da gwamnatinmu ta kaddamarwa ga Al-ummar Gaza.
3. Netanyahu shike da alhakin tabarbarewar lafiyata da yanayin da nake ciki a yanzu.

-Oppecial Taekwond Al'ameen
ABS Radio • Palestine Ayau

Aƙalla mutane 58 ne hare-haren HKI kan masu karɓa kayan agaji ya kashe a Wunin jiya Laraba a Gaza. Haramtacciyar Kasar I...
31/07/2025

Aƙalla mutane 58 ne hare-haren HKI kan masu karɓa kayan agaji ya kashe a Wunin jiya Laraba a Gaza. Haramtacciyar Kasar Isra'ilan takai hare-haren ne a daidai lokacin da ake raba kayan agaji baya da killace Yankin a cikin matsanancin rashin wadataccen abinci da kwanciyar hankali ga miliyoyin Falasɗinawan dake Gaza.

-Palestine Ayau | ABS Radio

Aƙalla Falasɗinawa 30 s**a mutu tare da jikkata sama da 300 a farmaki jirgin yaƙin HKi kan masu karɓar kayan agaji da ya...
30/07/2025

Aƙalla Falasɗinawa 30 s**a mutu tare da jikkata sama da 300 a farmaki jirgin yaƙin HKi kan masu karɓar kayan agaji da yammacin yau a arewacin Gaza.

-Palestine Ayau | ABS Radio

Yara da mahaifansu na fama da matsananciyar yunwa.A Gaza fiye da kaso daya cikin daya cikin biyar (5) daga cikin yara ya...
30/07/2025

Yara da mahaifansu na fama da matsananciyar yunwa.

A Gaza fiye da kaso daya cikin daya cikin biyar (5) daga cikin yara yan kasa da shekaru biyar na fama da matsananciyar yunwa da rashin abunci mai gina jiki. Wadan da suke raye suna fuskantar tabarbarewar lafiya ta jiki da kwakwalwa saka makon rashin abunci –lamarin dake iya jawo rasa rayukan mutane da yawa a Gaza.

–Mujtaba Muhammad MJ
-ABS–Radio | Palestine Ayau






Wasu Yan fafutukar neman neman yancin falasdinu sun gudanar da zaman dirshan a Poland don nuna goyon baya ga Al'ummar Pa...
30/07/2025

Wasu Yan fafutukar neman neman yancin falasdinu sun gudanar da zaman dirshan a Poland don nuna goyon baya ga Al'ummar Palestine da yin Allah wadai da harin Haramtacciyar kasar Isra'ila a Gaza.

-Mujtaba Muhammad MJ

-ABS Radio | Palestine Ayau




Ma'aikatar Lafiya ta Gaza dake Falasɗinu ta ruwaito cewa:- A cikin sa'o'i 24 da s**a gabata, gamayyar Asibitoci dake Gaz...
28/07/2025

Ma'aikatar Lafiya ta Gaza dake Falasɗinu ta ruwaito cewa:- A cikin sa'o'i 24 da s**a gabata, gamayyar Asibitoci dake Gaza sun bada rahoton jimlar mutuwar mutane 14 saboda matsanancin yunwa da abinci mai gida jiki.

Ya zuwa yanzu adadin Falasdinawa da s**a mutu sakamakon rashin wadataccen abinci yakai 147 cikinsu akwai yara 88.

-Taekwond Ameen
Palestine Ayau | ABS Radio

Address

Ramallah

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Palestine Ayau posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share