Auwal Ahmad Dankode

Auwal Ahmad Dankode Try to be a honest at all times

01/08/2026

JIRGI✈️🛫✈️MAI ABUN MAMAKI.

Mai Shin ka taɓa lura idan jirgin sama yana tafiya, wani farin layuka masu tsawo suna binsa a baya. Mutane da dama suna ɗaukar cewa hayakin jirgi ne, wasu kuma suna cewa wai ROKA ce dake nemo jirgi idan ya ɓace 😄 amma a zahiri ba haka ba ne.

Ana kiran waɗannan fararen layuka da suna Contrails (Condensation Trails), wato layukan da ke samuwa sakamakon iskan jirgi mai zafi da kuma yanayin sanyi mai tsanani a sararin sama.

Ta yaya Contrails ke samuwa?

A duk lokacin da Jet Engines ke aiki, suna fitar da iska mai zafi tare da ɗan tururin ruwa (water v***r) wanda ke fitowa sakamakon ƙonewar man jirgi (Jet Fuel Combustion).

A mafi yawan lokuta, jiragen sama suna tafiya ne a tsakanin 25,000 feet har zuwa 40,000 feet (Flight Level 250 – 400), inda yanayin temperature kan sauka har zuwa -40°C ko ƙasa da haka.

Lokacin da wannan tururin mai zafi ya haɗu da iska mai tsananin sanyi a sararin sama, yana daskarewa cikin sauri ya zama ƙananan ƙwayoyin kankara (Ice Crystals). Waɗannan ƙwayoyin ƙanƙara ne ake gani a matsayin farin layukan da ke bayan jirgi, wato Contrails.

Me yasa wasu Contrails suke ɓacewa da sauri, wasu kuma su daɗe?

Tsawon lokacin da Contrails za su ɗauka a sama yana dogara ne da yanayin iska (Atmospheric Conditions), musamman:

1. Humidity (danshin iska)
2. Temperature (yanayin zafi)
3. Wind Conditions (yanayin iska)

Idan iska yana da danshi sosai, Contrails na iya daɗewa har ma su bazu su zama kamar siraran gizagizzai (Cirrus Clouds). Amma idan iska bai da danshi, sukan ɓace cikin ƴan mintuna.

Shin Contrails suna da haɗari?

A’a. Contrails ba su haifar da wata matsala ga jiragen da ke biye. Su ba kamar Wake Vortex ko Wake Turbulence ba ne, waɗanda suke fitowa daga ƙarshen fikafikan jirgi (Wingtips) kuma su shafi sauran jirage dake bayan su.

A Taƙaice

Contrails ba wata na'ura bace da take nemo jirgi idan ya ɓace, kawai dai wata alama ce ta haɗuwar zafin engines na jiragen sama da yanayin sararin samaniya. Ba hayaki ba ne,

Adress

Kode

Webbplats

Aviseringar

Var den första att veta och låt oss skicka ett mail när Auwal Ahmad Dankode postar nyheter och kampanjer. Din e-postadress kommer inte att användas för något annat ändamål, och du kan när som helst avbryta prenumerationen.

Genvägar

Dela