20/11/2025
A ranar Laraba, Ma'aikatar Lafiya a Gaza ta ba da rahoton cewa rundunar sojin Isra'ila ta kashe Falasɗinawa 25 kuma ta raunata 77 a jerin hare-hare kan wasu yankuna da Isra'ila ta riga ta janye daga cikinsu, abin da hukumomin Falasɗinawa s**a ce keta yarjejeniyar tsagaita wuta ce.
Hukumar Tsaron Al'umma ta Falasɗinu a Gaza ta ce an zaƙulo mutum 3 daga iyalai biyu a cikin ɓaraguzai, sannan an jikkata aƙalla wasu mutane 15 a Khan Younis, a kudancin Gaza.