11/06/2024
Gabadaya bayanin da Hamstar s**ai a kan airdrop criteria nasu za ka iya raba shi gida 3. Na farko sun ce ba za su yi amfani da token balance ba, na biyu sai s**a ce da profit per hour (PPH) za su yi amfani. Amma a tsakiya sai s**a ce "play wisely" wanda shi ne na uku. Saboda haka a ga'ba ta ukun nan kamar sun ce ka je kai tinani ne. Wana irin tinani?
Lokacin da ka fara tinanin a kai, sai ka ajiye maganar token balance a gefe. Saboda qarara wannan sun ba ka amsa a kansa har da yin amfani da emphasis wurin bayanin amsar. Amma idan ka ga dama za ka iya yin gaban-kanka ka je ka tara token balance, idan ta 'bulle ma shi ke nan; idan kuma ta kwa'be ma to dama sun fada ma. Sai ka za'ba, abun da s**a fada ma za ka dauka ko ra'ayinka za ka bi.
Shi kuma abu na biyu da s**ai magana a kai -- profit per hour (PPH) -- idan ka kula gabadaya shi ne cornerstone na ecosystem din nasu. Ma'ana dik wani abu da za ka yi a mining din ya dogara da wannan PPH ne. Misali: 5m daily combo reward da ake claiming ana samun sa ne kadai ta hanyar cards minting, su kuma card minting amfanin su shi ne qarfafa PPH. Idan PPH yai qarfi za kai saurin tara token balance, dik sanda token balance ya taru zuwa wani amount to zai kai ka level na gaba.
Mutane kuma sun ce girman level dinka yana determining card rewards dinka -- idan misali ina level 4 kai kuma kana level 2, to idan muka yi minting wani card iri daya za a iya ba ni 2k PPH kai kuma misali a ba ka 1k PPH. So PPH zai tara maka token balance, token balance ya qara maka level, iya level dinka kuma iya saurin hauhawar PPH dinka. Everything stiched together intricately.
Shi ya sa s**a ce play wisely. Sannan dole akwai buqatar wise decision making wurin sanin wana kalar card ya kamata kai minting dan kai saurin tara PPH, shi kuma ya tara ma token balance, shi kuma ya wulla ka level na gaba. Saboda akwai cards masu tsada amma reward dinsu qarami ne, idan ka matsa musu tin a farko za ka qone token naka ba tare da ka had'a PPH ba b***e level mai nisa.
Sannan daga cikin amfanin play wisely akwai buqatar bibiyar daily combo. Idan ka kula dik sanda kai missing wani daily combo to suna recording din shi. Haka dik wanda ka yi shi ma yana nan recorded! Why? (Will post about this tonight). Saboda haka, ko da ka riga ka yi minting card dinka sun yi nisan da dik sanda za ai daily combo kana qona token fiye da wanda za a ba ka, to qwara ka dinga qonawar anyway. Qwara ka qona 20m token kai attendance na wannan combo saboda riba 3 ce.
Riba ta farko kana da combo attendance, ta biyu ka qara PPH dinka, sannan na uku an ba ka 5m token matsayin kamar an rage ma asarar token da aka caje ka. Sannan already dama kana da babban PPH da yake tara maka token balance mai yawa kullum, therefore tinda ka qara qaro qarfin PPH din again za kai saurin mayar da balance dinka. Wani Combo din idan ka tsallake shi kuma shi ke nan ya zama "expired" ba za ka taba iya minting dinsa ba. 🙄
So, duba da irin wadannan abubuwan, a nawa tinanin qwara mutum ya dauki abun da s**a fada qarara yai amfani da shi. It doesn't make sense to me wai wani babban project zai futo yai clarification kan wani rudani da ake ciki, sannan yai amfani da emphasis wurin clarification din ta hanyar rubutu da babban baqi dika dai dan kowa ya gane, amma still daga baya ya zo yai hukunci da sa'banin wannan abun da yai bayani. Come on! Idan project za su yi mugunta technical language suke amfani da shi.
Gaskiya ni qwara na bi wannan bayanin nasa da yai gwari-gwari, idan daga baya ya yaudare ni kuma wannan qaddara ce, because I can't have control over what they do to me. But I do have total control over what I choose to do, ka ga idan na za'bi qin bin abun da s**a ce to wannan ni na jawowa kaina. Idan na bi abun da s**a ce kuma riba 2 ce, ko dai su cika alqawari nai nasara, ko su saba alqawari su tafi da alakina.
Amma dik da haka, idan kai ba ka samu gamsuwa ba, za ka iya dabara kai boosting PPH din naka, idan yai nisa sosai yana iya tara wa mutum sama da 20m token a rana. Idan kai ma naka yai irin wannan nisan sai ka tara balance din ko sati 1 ne ka bar shi kar ka qona in case ko da za su yi wala-walar, ka ga ke nan ba ka zurma gabadaya ba. Simple!