04/23/2026
Haka Shehu Ɗanfodiyo ya zo ya samu dayawan al'ummarmu suna bautar dodo, cikin ikon Allah ya taimake shi ya tsamo su daga bautar dodo. Amma saboda rashin kunya wai yanzu shehun da ya tsamo kakanninsu daga wannan masifa shi ne abin zagi, da ba don Shehu ba da yanzu duka yara masu zagin nan su ma suna can suna bautar tsumburbura da dodo kuma suna shan burkutú.
Yanzu fa kamar haka ne, sai wani jikan tsohon nan ya zo bayan shekaru 100 ya ce Adam Ashaka ya musu rashin mutunci, ya ci galba a kansu kuma ya yàƙe su bai musu adalci ba. Laifin Adam Ashaka shi ne ya yi ɗawainiya ya musuluntar da kakansu. Shi ma Shehu Ɗanfodiyo laifinsa ɗaya shi ne ya hana kakanninsu bautar gunki da dodo da tsumburbura.
Ƙarshen lalacewa shi ne ka ce za ka samo tarihinka wajen maƙiyinka bature, kun yarda malamai su ba ku ilimin sallah da zakka amma ba ku yarda da su ba a kan tarihin addininku da na Ɗanfodiyo ba, akwai hàukar da ta wuce wannan?
Shehu ai kafin Allah ne, ba abin da na ɗauki wannan abin face kawai Allah ne yake son ambaton Shehu ya ci gaba da wanzuwa sai ya ƙaddaro wannan abin. A soke shi ya samu lada sannan bayin Allah na ƙwarai su yi ta masa addu'a suna karanta littattafansa yana ƙara samun lada a kan lada. Wannan shi ne. ❤️
Allah saka wa Shehu da alheri, shi ma Adam Ashaka Allah biya su da aljanna da iyayenmu.