ADAMU I ABBA

ADAMU I ABBA A meaningful silence is more better than meaningless words.

13/08/2025
06/08/2025

Many people slept at night, but many were not lucky enough to see the morning. You and I are alive. Alhamdulillah.

06/08/2025

Thank you Allah for everything Alhamdolillah ya Rab

05/08/2025

🤍🤍🤍

11/09/2023

HABA MATASHI WAI SHIN? MAI YAKE BURGEKA HAR KAKE ASKI DA YA SABAWA UMARNIN ANNABIN MU, ANNABIN RAHMA ANNABI MUHAMMADU SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM 🙏?

"Wa kake burgewa idan kayi askin banza?
"Wacce riba kake samu idan kayi askin banza?

(1) Askin banza wata mummunar ɗabi'a ce wacce matasa suke aske wani sashi na gashin kansu su kyale wani ɓangare domin tsammanin wayewa da buɗewar ido Askin banza yaci karo da tsarin addinin Musulunci domin Manzon Allah (SAW) yayi hani ga aikata hakan, sannan yaci karo da al'adar Malam bahaushe daɗin da ɗawa yaci karo da lafiyayyen hankali to amma abin tambayar me yasa matasan mu suke yi ba tare da shayi ko kunyar kowa ba? Ya zama wajibi mai askin banza yasan da waɗannan batutuwa masu zuwa a ƙasa koba komai yasan matsayinshi a idon kowa, baka da ƙima da mutunci a idanuwan rukunonin al'ummar da zan lissafo_

(2) IYAYE! Burin kowane uba ko uwa bai wuce su ga ɗan su ya zama mutumin kirki ba👌, wannan dalilin yasa zuciyar iyaye take ƙuntata yayin da s**a ga ɗansu da askin banza wani lokacin ma har ka samu wani uban yayi baran-baran da ɗanshi saboda wannan mummunar ɗabi'a domin iyaye sun gamsu harka ce ta mutanen banza,👌

(3) ƳAN'UWA/DANGI. Duk wanda ke yin irin wannan askin na banza, to wallahi bashi da kwarjini ko acikin ƴan'uwanshi Hasalima wani lokacin ware shi su keyi cikin duk kanin abinda ya shafi mutuntaka👌

(4) MANYAN UNGUWA. Duk mutumin kirki a unguwa/layi baya yiwa mai askin banza kyaky-kyawan zato kuma baya burge shi hasalima kallon mutumin banza ake mar duk wani babban mutum yake yiwa mai askin banza kuma duk wanda ya ganshi da ɗan shi👌 sai yayi duk mai yiwuwa don ganin ya raba alakarsu.

(5) ƳAN MATA. Mafi yawancin matasa masu askin banza sunayi ne domin su birge ƴan mata, sai dai basu san basa birge su ba Hasalima kallon cikakkun ƴan iska su keyi musu domin sau tari waɗanda ake kamawa da laifin fyaɗe mafi yawanci irin masu wannan siffar ne. Allah ka shiryar damu bisa tafarki madaidaici 🙏

(6) AL'UMMA BAKI ƊAYA: Al'um

Ba rabo da gwani ba...
05/06/2023

Ba rabo da gwani ba...

TUNA BAYA FURUCIN SARKI ADO A KAN GINA COCIKo Jonathan Be Isa Ya Gina Coci A Jamai'ar Bayero ba- Inji marigayi Tsohon  S...
05/06/2023

TUNA BAYA FURUCIN SARKI ADO A KAN GINA COCI

Ko Jonathan Be Isa Ya Gina Coci A Jamai'ar Bayero ba- Inji marigayi Tsohon Sarkin Kano
Ado Bayero

Zaman babbar kotun Shari'ah (Federal High Court) dake babban birnin tarayya
Abuja, akan karar da kungiyar Kiristoci ta
kasa CAN ta kai Masarautar Kano,
saboda Mai Martaba Sarkin Kano Alh. Dr
Ado Bayero yasa an rushe wata Coci da
ake ginawa a cikin tsohuwar Jami'ar Bayero Kano (BUK).

A zaman kotun da akayi a ranar Litinin 3
Feb, 2014, kotu ta nemi Mataimakin
Shugaban Jami'ar Bayero Prof Rasheed,
da wakilin kungiyar Kiristoci ta kasa, da
kuma Mai Martaba Sarkin Kano da su bayyana a gabanta, a zaman kotun, anga
Prof Rasheed da mataimakin shugaban
CAN sun mike tare da Lauyoyinsu amma
ba a ga Mai Martaba Sarki ba.

Daga nan sai jagoran Alkalan kotun
Justice Alakola Nweri yace da yake muna da sauran mintuna 10 kafin fara Shari'ar
zamu jira zuwan Mai Martaba Sarkin
kafin wadannan mintoci.
Daga nan sai Justice ya dubi Prof
Rasheed yace a baya Kotu ta baku
umarnin Gina Coci a Jami'ar Bayero, ko kunbi umarnin kotu?

Prof Rasheed ya ce kwarai kuwa munbi
umarnin Kotu, dan sai da ginin Cocin ya
kai linta sannan Mai Martaba Sarkin
Kano ya bamu umarnin tsayar da aikin,
daga baya kuma sai ga Mai Girma Galadiman Kano Alh. Tijjani Hashim ya
jagoranci Rushe ginin gaba daya.
Justice yace, kuna nufin kenan kunyi
watsi da umarnin kotu kunbi na Sarki?
Prof Rasheed ya ce kwarai kuwa saboda
Sarki Ubanmu ne, kuma shine Sarki mai daraja ta daya a kasar nan bayan Sarkin
Musulmi saboda haka, bazamu iya kin yi
masa biyayya ba.

Daga nan sai Justice ya umarci Prof
Rasheed da ya zauna. Justice ya ce da
wakilin CAN kaji abinda ya fada kana da abin cewa?
Sai yace Eh, wakilin CAN yace gaskiya
ne hukumar Makarantar Jami'ar Bayero
ta fara gina Cocin aka Hanasu saboda
haka muke rokon wannan kotu da ta
hukunta Sarkin Kano bisa shiga hurumin da ba nasa ba. Daga nan shima akace ya
zauna.

Sannan kotu ta nemi Sarkin daya
bayyana a gabanta, ana haka sai ga
Sakatare

05/06/2023

*ZIKIRORIN SAFE DA YAMMA*

Yin sakaci da Azkar din safe da Yamma kamar yin sakaci ne ka bar wata ƙofa da sharri ko cutarwa za su iya isowa gareka!

Ki/Ka yi Azkar din ka kuwa???

💠Ayatul kursiyyu (1).
💠Qul huwaLLahu Ahad (3×).
💠Qul a'udhu bi Rabbil falaq (3×).
💠Qul a'udhu bi Rabbin naas (3×).

💠Asbahnaa wa asbahal mulku Lillah (Idan da yamma ne kuma: Amsainaa wa amsal mulku Lillah), walhamdu Lillahi, laa ilaaha illaLLahu wahdahu laa shareeka lahu, lahul mulku wa lahul hamdu, wahuwa alaa kulli shay'in k'adeer, Rabbi as'aluka khaira maa fi hazal yaumi wa khaira maa ba'adahu, wa a'udhu bika min sharri ma fi hazal yaumi wa sharri maa ba'adahu (da yamma kuma: Rabbi as'aluka khaira ma fi hazihil lailah wa khairi ma ba'adahu, wa a'udhu bika min sharri ma fi hazihil lailati wa sharri ma ba'adahu), Rabbi a'udhu bika minal kasal, wa suu'il kibar, Rabbi a'udhu bika min azabin fin naari, wa azabin fil ƙabar.

💠Allahumma bika asbahna wa bika amsainaa, wa bika nahyaa, wa bika namuutu wa ilaakan nushuur.
Idan kuma da Yamma ne:
Allahumma bika amsaina wa bika asbahnaa, wa bika nahyaa wabika namuutu wa ilaikal maseer.

💠Allahumma Anta Rabbiy laa ilaaha illa Anta, khalaƙtaniy wa ana abduka, wa ana alaa ahdika wa wa'dika mastaɗa'atu, a'udhu bika min sharri ma sana'atu, abuu'u laka bini'matika alayya, wa abuu'u bidhambiy fagfirliy fa'innahu laa yagfiruz dhunuba illa anta.

💠Allahumma inniy asbahtu (Idan kuma da yamma ne: Amsaitu) ushhiduka wa ushhidu hamalata Arshika, wa malaa'ikatika wa jamee'i khalƙika, annaka AntaLLaahu laa ilaaha illa Anta wahdaka laa shareeka laka, wa anna Muhammadan abduka wa rasuuluka.

💠Hasbiyallahu laa ilaaha illa huwa alaihi tawakkaltu wa huwa Rabbul Arshil azeem (Sau 7).

💠Allahumma inniy as'alukal afwa wal aafiyata fidduniya wal aakhirah, Allahumma inniy as'alukal afwa wal aafiyata fi deeniy wa dunyaya wa ahlee, wa maaliy, Allahummas-tur auraatiy, wa aamin rau'aatiy, Allahummah-fizniy min baini yadayya wa min khalfiy, wa an yameeniy, wa an shimaali

05/06/2023

FALALAR KARANTA SURATUL MULK !!!

Wannan Sura ta shara da suna Suratul Mulk amma ana ƙiranta da wasu sunayen kamar “Suratul Tabaraka” da kuma Suratul Tabarakal lazi Biyadihil Mul]” Suratul Mulk tana ɗaya daga cikin surorin Alƙur'ani Maigirma, ita ce sura ta 67, tana da ayoyi 30, sura ce da ke bada kariya ga azabar kabari ga duk wanda ya lizimci karanta ta, kuma tana ɗaya daga cikin Azkarun naum (zikirorin kwanciyar bacci), sura ce Makiyya a wajen mafi yawan malamai.

An ruwaito hadisai da dama da suke nuna mana cewa wanda duk yake karanta suratul Mulk wato Tabaraka zata kasance masa kariya daga Azaban kabari inshaa ALLAH.

Haƙiƙa wannan Falala ce maigirma daga cikin falalar da ALLAH ke bayarwa ga bayin sa. Malamai da dama sunyi sharhohi akan hadisan da s**a yi magana akan suratul Mulk akan falalar ta da kuma fa'idar karanta ta.

Daga cikin Falalarta da abin da hadisai s**a zo da shi akwai:

1● An karɓo daga Abu-hurayrah (RA) Ya ce: “Manzon ALLAH (ﷺ) Ya ce: “Lalle akwai wata sura a cikin littafin ALLAH mai ayoyi talatin, ta yiwa wani mutum ceto a wurin ALLAH har sai da aka gafarta masa.” [Ahmad: 7975, Abu-dawud: 1400, Tirmidhi: 3111, Ibn Majah: 3786]

2● An Karɓo daga Abdullahi ɗan Mas'ud (RA) Ya ce: “Manzon ALLAH (ﷺ) Ya ce: Suratul Tabaraka ita ce mai hana azabar kabari.” [Assaheeha: 1140]

3● Manzon ALLAH (ﷺ) Ya ce: “Suratul Tabaraka garkuwa ce ga azabar kabari (mai hanawa ce ayiwa bawa azabar kabari).” [Saheeh Al-jami: 3643]

4● Daga Jabir (RA) Ya ce: “Lallai Manzon ALLAH (ﷺ) ya kasance ba ya yin barci har sai ya karanta (suratul Sajada), da (suratul Mulk).” [Tirmidhi: 2892]

5● Daga Ibn Mas'ud (RA) Ya ce: “Duk wanda ya karanta (تبارك الذي بيده الملك) a kowane dare, to ALLAH zai hana masa azabar kabari da ita, mun kasance a zamanin Manzon ALLAH (ﷺ) muna ƙiranta da suna ALMÀNI'A (mai hana azaba), lallai tana cikin littafin ALLAH, sura ce da wanda duk ya karanta ta a kowane dare, haƙiƙa ya yawaita lada, kuma ya sami dacewa” [Assunanul Kubra Linnasá'iy: 10479]

Address

TX

Telephone

+19034991337

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when ADAMU I ABBA posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share