VOA Hausa

VOA Hausa Sashen Hausa na VOA na daya daga cikin manyan majiyoyin labarai daga Najeriya da na duk fadin duniya.

An kafa sashen Hausa na Muryar Amurka ran 21 ga watan Junairu, shekara ta 1979, domin watsa labaran duniya da shirye-shirye zuwa ga Hausawa da masu jin harshen Hausa a duk fadin duniya, musamman ma yammacin Afirka kamar kasashen Nigeria, Ghana, Nijar, Chadi, Libya, Cote d’Ivoire da wasu sassan janhuriyar Benin. Sashen Hausa na watsa sa’oi 13.5 na shirye-shirye a kowace mako, ta radiyo da yanar int

anet. Sashen kuma na buga labaran gida Najeria, da sauran duniya, da bidiyon manyan labaran Afirka daga ran Litinin zuwa Juma’a akan shafinsa na intanet. Shirye-shiryen sashen sun hada da labarai masu zafi , da rahotannin wakilai daga duk fadin duniya, tattaunawa da manyan jami’an gwamnatoci, ganawa da masu fashin baki, fadakarwa daga malamai da manazarta, dauka da watsa ra’ayoyin masu sauraro da suke bayarwa a rubuce, ta waya kai tsaye da kuma ta email.

🎧 TUBALIN TSARO: Shirin na wanan makon ya bibiyi yadda rashin tsaro ke shafar ayyukan kasuwanci tsakanin kasashen Nijar ...
03/14/2025

🎧 TUBALIN TSARO: Shirin na wanan makon ya bibiyi yadda rashin tsaro ke shafar ayyukan kasuwanci tsakanin kasashen Nijar da makwabciyarta Chadi, ganin yadda ‘yan ta'addan Boko Haram, ‘yan fashi da makami, da wasu miyagu ke cin karensu ba babbaka akan Iyakarsu.

Tuni wannan matsalar ta jefa direbobi da ‘yan kasuwa cikin tashin hankali ganin wannan kalubale na rashin tsaro na ci gaba da kawo cikas.

Shiga shafin a saurari cikakken shirin.

Shirin Tubali na wanan makon ya bibiyi yadda rashin tsaro ke shafar ayyukan kasuwanci tsakanin kasashen Nijar da makwabciyarta Chadi, ganin yadda ‘yan ta'addan Boko Haram, ‘yan fashi da makami, da wasu miyagu ke cin karensu ba babbaka akan Iyakarsu. Tuni wannan matsalar ta jefa direbobi da ‘ya...

🗞️ Wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman kan kasar Syria yana kira da a kawo karshen tashin hankali da kare farare...
03/14/2025

🗞️ Wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman kan kasar Syria yana kira da a kawo karshen tashin hankali da kare fararen hula, yayin da kasar ke fama da sabbin tashe-tashen hankula watanni uku bayan hambarar da gwamnatin Bashar al-Assad.

Wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman kan kasar Syria yana kira da a kawo karshen tashin hankali da kare fararen hula, yayin da kasar ke fama da sabbin tashe-tashen hankula watanni uku bayan hambarar da gwamnatin Bashar al-Assad.

🗞️ Bayanai na nuni da cewa, tun a yammacin laraba 12 ga watan maris din 2025 ne Shugaban gwamnatin mulkin sojan Nijer ya...
03/14/2025

🗞️ Bayanai na nuni da cewa, tun a yammacin laraba 12 ga watan maris din 2025 ne Shugaban gwamnatin mulkin sojan Nijer ya baiwa wadanan darektoci ‘yan China sa'oi 48 su fice daga kasar.

Bayanai na nuni da cewa, tun a yammacin laraba 12 ga watan maris din 2025 ne Shugaban gwamnatin mulkin sojan Nijer ya baiwa wadanan darektoci ‘yan China sa'oi 48 su fice daga kasar.

03/14/2025

DUNIYAR AMURKA: Trump ya yi barazanar kakabawa kasashen nahiyar turai harajin kashi 200.

📷 YouTube/White House

Saurari shirin na Manuniya don jin irin kurar da ficewar El Rufa'i daga APC ta tayar a fagen siyasar Najeriya.
03/14/2025

Saurari shirin na Manuniya don jin irin kurar da ficewar El Rufa'i daga APC ta tayar a fagen siyasar Najeriya.

Shirin Manuniya na wannan mako ya maida hankali ne akan halin da siyasar Najeriya ke ciki tun bayan sanar da komawar tsohon gwamnan jahar Kaduna, Nasiru El-rufa'i jam'iyyar SDP.

Hakan na faruwa ne bayan da EU ta sanya abin da Trump ya kira "mummunan harajin kashi 50%" kan barasa da ake sarrafawa a...
03/14/2025

Hakan na faruwa ne bayan da EU ta sanya abin da Trump ya kira "mummunan harajin kashi 50%" kan barasa da ake sarrafawa a Amurka.

"An jima ana kwarar mu tsawon shekaru, ba za mu sake amincewa da haka ba.” Trump ya ce.

“Ni mamba ne a APC kuma ina so a rika kirana a matsayin hakan. Zan yi iya bakin kokarina na ga na tallata APC ta kowacce...
03/14/2025

“Ni mamba ne a APC kuma ina so a rika kirana a matsayin hakan. Zan yi iya bakin kokarina na ga na tallata APC ta kowacce hanya.” Buhari ya ce cikin sanarwar.

Kalaman na Buhari na zuwa ne sa’o’i bayan da tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El Rufa’i ya ce ya fadawa Buhari cewa zai fita a jam’iyyar ta APC kamaryadda rahotanni s**a nuna.

🎧 LAFIYA UWAR JIKI: Shirin Lafiya na wannan makon ya yi magana ne akan yadda ya kamata mutane su kula da kansu musamman ...
03/13/2025

🎧 LAFIYA UWAR JIKI: Shirin Lafiya na wannan makon ya yi magana ne akan yadda ya kamata mutane su kula da kansu musamman yanzu da ake azumi a yanayi na zafi, da kuma yadda masu fama da cututtukan dake da bukatar shan magani kullum zasu kula da kansu domin gudanar da a azuminsu ba tare da fuskantar wani kalubale ba.

Shiga shafin a saurari cikakken shirin.

Shirin Lafiya na wannan makon ya yi magana ne akan yadda ya kamata mutane su kula da kansu musamman yanzu da ake azumi a yanayi na zafi, da kuma yadda masu fama da cututtukan dake da bukatar shan magani kullum zasu kula da kansu domin gudanar da a azuminsu ba tare da fuskantar wani kalubale...

🗞️ Ministocin harkokin wajen manyan kasashen yammacin duniya sun gana a kasar Canada ranar Alhamis bayan shafe makonni b...
03/13/2025

🗞️ Ministocin harkokin wajen manyan kasashen yammacin duniya sun gana a kasar Canada ranar Alhamis bayan shafe makonni bakwai ana takun saka tsakanin kasashe abokan kawancen Amurka da shugaba Donald Trump, akan yadda kwatsam sauya manufofin Amurka kan Ukraine da kuma batun sanya haraji.

Ministocin harkokin wajen manyan kasashen yammacin duniya sun gana a kasar Canada ranar Alhamis bayan shafe makonni bakwai ana takun saka tsakanin kasashe abokan kawancen Amurka da shugaba Donald Trump, akan yadda kwatsam sauya manufofin Amurka kan Ukraine da kuma batun sanya haraji

🗞️ Babban mai taimaka wa Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin kan harkokin ketare ya fada yau Alhamis cewa, ya shaidawa W...
03/13/2025

🗞️ Babban mai taimaka wa Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin kan harkokin ketare ya fada yau Alhamis cewa, ya shaidawa Washington, tsagaita bude wuta na kwanaki 30 da Amurka ta gabatar na dakatar da yakin Ukraine zai baiwa dakarun Kyiv daga kafar da suke bukata a fagen daga ne.

Babban mai taimaka wa Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin kan harkokin ketare ya fada yau Alhamis cewa, ya shaidawa Washington, tsagaita bude wuta na kwanaki 30 da Amurka ta gabatar na dakatar da yakin Ukraine zai baiwa dakarun Kyiv daga kafar da suke bukata a fagen daga ne.

🗞️ A ranar Alhamis manyan jami'an kungiyar Tarayyar EU s**a tattaru a Afirka ta Kudu don halartar wani taron koli da Shu...
03/13/2025

🗞️ A ranar Alhamis manyan jami'an kungiyar Tarayyar EU s**a tattaru a Afirka ta Kudu don halartar wani taron koli da Shugaban kasar Cyril Ramaphosa, taron da zai maida hankali kan karfafa huldar kasuwanci da diflomasiyya yayin da dukkan kasashen ke jin tasirin manufofin harkokin waje na gwamnatin Trump

A ranar Alhamis manyan jami'an kungiyar Tarayyar EU s**a tattaru a Afirka ta Kudu don halartar wani taron koli da Shugaban kasar Cyril Ramaphosa, taron da zai maida hankali kan karfafa huldar kasuwanci da diflomasiyya yayin da dukkan kasashen ke jin tasirin manufofin harkokin waje na gwamnatin Trump

🗞️ Kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL) ya yi kira ga masu zuba jari a duniya da su karkato da hankalinsu ga bangaren ...
03/13/2025

🗞️ Kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL) ya yi kira ga masu zuba jari a duniya da su karkato da hankalinsu ga bangaren mai da iskar gas na Najeriya domin a halin yanzu al’ummar kasar ta zama matattarar masu saka hannun jari saboda sauye-sauye da aka yi da kuma tsare-tsare masu dacewa da masu zuba jari.

Kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL) ya yi kira ga masu zuba jari a duniya da su karkato da hankalinsu ga bangaren mai da iskar gas na Najeriya domin a halin yanzu al’ummar kasar ta zama matattarar masu saka hannun jari saboda sauye-sauye da aka yi da kuma tsare-tsare masu dacewa da masu zuba ja...

Address

330 Independence Avenue, SW
Washington D.c., DC
20237

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when VOA Hausa posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share