Arewa A Yau

Arewa A Yau All about Nigeria and beyond in English and Hausa Languages.

Manoma sunyiwa Gwamnatin Tinubu bore a kan shigo da abinci Najeriya. Me zaku ce?
12/10/2025

Manoma sunyiwa Gwamnatin Tinubu bore a kan shigo da abinci Najeriya.

Me zaku ce?

Yanzu-Yanzu: Tinubu Ya Yafewa Maryam Sanda wada ta sheke mijinta shekaru 5 da s**a gabata.Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinub...
11/10/2025

Yanzu-Yanzu: Tinubu Ya Yafewa Maryam Sanda wada ta sheke mijinta shekaru 5 da s**a gabata.

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yafewa Maryam Sanda, wacce kotu ta yanke wa hukuncin kisa a shekarar 2020, bisa samunta da laifin kashe mijinta, Bilyaminu Bello.

Maryam Sanda, mai shekaru 37, ta shafe shekaru 6 da watanni 8 a gidan gyaran hali na Suleja, kafin samun wannan afuwa daga shugaban ƙasa.

Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya bayyana cewa wannan mataki ya fito bayan shawarar kwamitin musamman da ke duba batun yafe wa masu laifi a fadin ƙasar.

Me zaku ce?

Mahaifi ya sayar da jaririnsa kwanaki biyar da haihuwar shi.Rundunar Yansanda a Ebonyi ta k**a wani mutum mai suna Chukw...
11/10/2025

Mahaifi ya sayar da jaririnsa kwanaki biyar da haihuwar shi.

Rundunar Yansanda a Ebonyi ta k**a wani mutum mai suna Chukwuma Onwe, bisa zargin sayar da ɗansa kwanaki biyar da haifar da akan kuɗi Naira miliyan 1.5.

An k**a Onwe, wanda dan asalin kauyen Nwezenyi-Igbeagu ne a Karamar Hukumar Izzi ta jihar, bayan matar da zai aura, Philomena Iroko, ta sanar da makwabciyarta, wadda ita kuma ta kai rahoto ga ƴansanda.

Omar ya sayar da yaron ga wata mata mai suna Chinyere Ugochukwu, wacce ita ma yanzu tana hannun ƴansanda, Daily Nigerian ta wallafa

SP Joshua Ukandu, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN, a yau Asabar a Abakaliki cewa an ƙwato jaririn daga hannun wacce ake zargi da sayensa.

Ukandu ya ce an k**a mahaifin yaron tare da wadda ake zargi da sayen jaririn a jiya Juma’a a unguwar Azugwu da ke Karamar Hukumar Abakaliki ta jihar.

Rariya Online

KAJI KO: Idan Sheikh Lawan Triumph Ya Ci Mutuncin Manzon Allah (SAW), Ba Zamu Goyon Bayansa Ba” — Inji Alhassan Mai Lafi...
11/10/2025

KAJI KO: Idan Sheikh Lawan Triumph Ya Ci Mutuncin Manzon Allah (SAW), Ba Zamu Goyon Bayansa Ba” — Inji Alhassan Mai Lafiya

Wani daga cikin matasa a cikin ƙungiyar Izalah, Alhassan Mai Lafiya, ya bayyana cewa ƙungiyar ba za ta goyi bayan kowa ba idan har an tabbatar da cewa ya ci mutuncin Manzon Allah (SAW), ko da kuwa mutum ne da suke ƙauna da girmamawa.

A cewarsa “Billahillazi, duk yadda muke son Sheikh Lawan Triumph, idan ya ci mutuncin Manzon Allah (SAW) k**ar yadda Malam Abduljabbar ya aikata, ba zamu goyamasa baya ba. Kuma zamu jagoranci hukuma da gwamnati domin a hukuntashi.”

Ya ƙara da cewa adalci shi ne ginshiƙin ƙungiyar Izalah, kuma suna goyon bayan gaskiya a kowane lokaci, ba tare da nuna son kai ko bambanci ba.

“Idan Malam Abduljabbar ne ya aikata abin da Malam Lawan ya aikata, da zamu goyamasa baya tare da bashi kariya saboda yana kan gaskiya. Ƙungiyar Izalah da yayanta ƙungiyar adalci ce da goyon bayan gaskiya. Idan muka aikata sharri, me zamu tsinta a rayuwar duniya?” in ji Alhassan Mai Lafiya.

Wannan furuci na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da muhawara kan zargin cin mutuncin Manzon Allah (SAW) da ake yi wa Sheikh Lawan Triumph a kafafen sada zumunta.

Leadership Hausa Online

KU JI RABO: Addinin Musulunci ya samu karuwa wata Matashiya Ƴar kasar Finland ta Musulunta ta karbi addinin Musulunci - ...
11/10/2025

KU JI RABO: Addinin Musulunci ya samu karuwa wata Matashiya Ƴar kasar Finland ta Musulunta ta karbi addinin Musulunci - Allah ya kara a cusa mana son Manzon Allah (S.A.W).

Cc; Albishir Hausa

11/10/2025

Da me kuke amfana a yankunanku a mulkin Tinubu?

11/10/2025

Mu yiwa Annabi Salati.
S.A.W

Sponsored.DA ƊUMI-ƊUMI: Dan Majalisa Nalaraba ya Raba Tallafin Karatu ga Matasa 500 a Jihar Nasarawa.Kamar yadda masu iy...
28/09/2025

Sponsored.

DA ƊUMI-ƊUMI: Dan Majalisa Nalaraba ya Raba Tallafin Karatu ga Matasa 500 a Jihar Nasarawa.

Kamar yadda masu iya magana ke cewa gina matasa shine gina ƙasa, ɗan siyasa Nalaraba ya sake nuna ƙoƙarinsa da bajintarsa wajen bunƙasa ilimi da ci gaban al’ummar Mazaɓarsa na jihar Nasarawa.

Dan Majalisa Nalaraba, wanda ya zage dantse ganin ya kawo Federal College of Education zuwa jiharsa, yanzu ya raba tallafin karatu ga ɗalibai 500 daga sassa daban-daban na jihar Nasarawa, Kowane ɗalibi ya samu ₦100,000 domin tallafa musu wajen ci gaba da karatu.

Ya bayyana cewa, manufarsa ba ta ta’allaka kan ƙabila ko jam’iyyar siyasa ba, domin ɗaliban da s**a ci gajiyar tallafin sun fito ne daga kowane yanki na jihar.

Nalaraba ya jaddada cewa, bai k**ata matasa su ci gaba da zama kayan aikin Yan siyasa ba, inda ya ce: "Ilimi shi ne makamin ci gaba da ya k**ata dukkan matasa su riƙe, Gina matasa shi ne gina ƙasa." in ji shi.

Manazarta kan lamarin siyasa na ganin cewa irin wannan aiki na aikin bajinta na da Alaƙa da jagoranci na gaskiya. A cewarsu, mulki ba wai kawai ayi alkawura ba ne, Cika alkawari shine ginshiƙin jagorancin k**ar yanda Nalaraba yake yi ma jama'a.

How x Nigerian Army Adamu Ashaka concentrated on Islamic Preaching across the northern part of the country.
19/09/2025

How x Nigerian Army Adamu Ashaka concentrated on Islamic Preaching across the northern part of the country.

19/09/2025

A Magistrates’ Court II sitting in Katsina has ordered the remand of Leadership Online Newspaper editor, Zuhair Ali Ibrahim, following a police request to keep him in custody pending investigations…

Yadda Kansila yayi amfani da Kwamishinan yan Sandan Jahar Katsina domin aika Dan Jarida Magark**a bayan fallasa zambar M...
18/09/2025

Yadda Kansila yayi amfani da Kwamishinan yan Sandan Jahar Katsina domin aika Dan Jarida Magark**a bayan fallasa zambar Miliyan 30.

A yau ne 18 ga watan 9, 2025 kotun majestire mai lamba biyu dake katsina ta aika da Editan jaridar Leadership Hausa Online News Ltd Zuhair Ali Ibrahim gidan yari bisa bukatar yan sanda na ajiye shi har sai an gama binciken wani korafin da kansilan Doro dake karamar hukumar Bindawa Abubakar Nuhu ya shigar akan sa.

Kansilan ya shigar da korafin ne, akan wani labari da Jaridar leadership Hausa Online ta rubuta a ranar 7 ga watan satumba inda wani mai suna Alhaji Ibrahim sa'adu yayi korafi da ikirarin kansilan Doro Abubakar Nuhu ya canye masa wasu kudin sa har naira milyan talatin. (30M)

A labarin da Jaridar ta buga tace Alhaji Ibrahim sa'adu ya bayyana cewa shi Ubangidan kansilan ne,kuma ya sha taimakonshi ya kuma yarda dashi amma yayi amfani da wannan yardar wajen damfarar shi k**ar yadda yayi zargi.

Editan yayi kokarin jin ta bakin kansilan Abubakar Nuhu amma abin yaci tura don haka s**a buga labarinsu a bisa ana zargin kansilan Abubakar Nuhu .

Kansilan Abubakar Nuhu ya kai kara wajen yan sanda inda aka je har zaria aka kamo zuhair a ranar litinin din data gabata zuhair ya fada ma yan sanda duk yadda ya samu labarin shi da kokarin shi na jin ta bakin kansilan amma abin yaci tura.

Wasu mutane a katsina sunyi kokarin shiga maganar don dai daitawa amma kansilan ya rika Saba alkawalin da ya dauka na janye maganar da sasantawa.

Mutanen da s**a shiga maganar don sansantawa sune Mai ba Gwamnan Katsina Dr. Dikko Umaru Radda shawara akan harkokin jam'iyyu Alhaji shafi i Duwan, sai Dan majalisar tarayya mai wakiltar Mani da Bindawa, sai Alhaji yusufu Ibrahim jargaba sai kuma Malam Danjuma katsina .

Kansilan sai ya amsa za a dai daita amma kuma ya Saba alkawalin, Kansilan yana neman tozarta Editan na leadership online newspaper bisa wata bukatar kashin kanshi, ko kuma don ya tsorata marubuta su bar fallasa komai nashi.

Rariya Online

18/09/2025

Ku sheke ra'ayoyinku

Address

Kano

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Arewa A Yau posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Arewa A Yau:

Share