27/10/2025
YANZU-YANZU: Al’ummar Kebbi Na Ci Gaba Da Marawa Abubakar Malami Baya
Al’ummar Jihar Kebbi na ci gaba da nuna goyon bayansu ga tsohon Ministan Shari’a na Ƙasa, Abubakar Malami (SAN), inda da dama ke ganin ya cancanci maye gurbin Gwamnan jihar yanzu, Nasir Idris Kauran Gwandu, a nan gaba.
Wasu daga cikin mazauna jihar sun bayyana cewa Malami mutum ne mai kishin ƙasa da kwarewa a fannin doka da siyasa, wanda ya nuna bajintarsa a lokacin da yake Ministan Shari’a karkashin gwamnatin tsohon Shugaba Muhammadu Buhari daga 2015 zuwa 2023.
A cewar wasu masu sharhi, Malami yana da gogewa da hangen nesa wajen tafiyar da al’amuran gwamnati, musamman ma a fagen adalcIn shari’a, yaki da rashawa da kuma dawo da kadarorin Najeriya daga ƙasashen waje.
Al’umma da dama a Kebbi suna ganin cewa irin wannan ƙwarewa da jajircewar sa na iya taimaka wa jihar wajen samun ci gaba mai ɗorewa idan aka ba shi damar jagoranci.
A halin yanzu dai, tattaunawa da ra’ayoyi kan yiwuwar tsayawar Abubakar Malami a takarar gwamnan Kebbi na gaba suna ƙara karfi, musamman a tsakanin matasa da tsofaffin ma’aikata, waɗanda ke ganin ya dace da mulki bisa cancanta da kwarewa, ba wai siyasa kawai ba.