Hasmag TV.

Hasmag TV. Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Hasmag TV., Media/News Company, .

Hasmag Online TV Gidan Talabijin ne da zai dunga Kawo maku Sahihan labarai na gida Najeriya tare da kasashen ƙetare, haɗi da ilimantarwa faɗakarwa nishaɗantarwa ku tuntubemu a 09121774270 Domin bamu labarai kan halin da kuke ciki a yankunan ku

Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Neja Rt. Hon. Abdulmalik Sarkin-Daji, ya fara gina sabuwar cibiyar koyon sana’o’i a gari...
17/08/2025

Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Neja Rt. Hon. Abdulmalik Sarkin-Daji, ya fara gina sabuwar cibiyar koyon sana’o’i a garin Mariga.

Cibiyar za ta koyar da matasa maza da mata sana’o’i k**ar aski, gyaran gashi, dinki, ICT, noma, da sauran sana’o’in zamani.

Wannan aiki zai taimaka wajen rage rashin aikin yi, bunkasa tattalin arziki, da kuma bai wa matasan karamar hukumar Mariga damar dogaro da kansu.

Shin me Zaku ce?

17/08/2025

DA DUMI-DUMI: Jam'iyyar hadaka ta ADC ta lashe zaben 'yar majalisar jiha a Anambra.

MAZAN AURE A KAI ZUCIYA NESAWani magidanci dan shekaru 50 a garin Bama jihar Borno mai suna Modu Isah ya saki matarsa, d...
17/08/2025

MAZAN AURE A KAI ZUCIYA NESA

Wani magidanci dan shekaru 50 a garin Bama jihar Borno mai suna Modu Isah ya saki matarsa, daga bisani ya nemi ta dawo gidansa taki saboda ya mata saki har guda uku, shine ya dauki wu_ka ya dat$e azzakarinsa saboda bacin rai, ya kuma caka wu_kar a cik!nsa

Lamarin ya faru shekaran jiya juma'a, Matar mai suna Bayanze Modu, 'Yan sandan Bama sun dauki mutumin jina-jina s**a kai shi General Hospital Bama, sannan an mayar da case din zuwa State CID Maiduguri

Da ake tambayarsa dalilin aikata haka, yace shi yayi yunkurin ka$he kansa ne saboda yana kishin matar da ya sake domin ta iya kwanciyar aure, ya gwammace ya bar duniya akan ya rayu ya ga wani ya aureta, yace idan bai mutu ba to babu amfanin zaman azzakarinsa a jikinsa ba tare da tsohuwar matarsa da ya sake ba

'Yan uwa Magidanta mu dinga kai zukatan mu nesa, idan ka san zaka auri mace ka saketa daga baya kayi nadamar sakin don Allah kar kayi, Musulunci ma ya hana yin saki a cikin fushi duk saboda gudun nadama irin wannan

Na taba yin case din abokin wani abokina, ya auri wata mata da mijinta ya sake saki uku, sai ta dinga masa karya cewa zataje asibiti, ashe tsohon miji ne yake kiranta a waya tana fita suna haduwa, shine ya bani nambar wayan matar na bincika, na ganoshi har daidai gurin da yake zuwa yana daukarta, da inda yake kaita, aka je aka k**ashi, har gidan yari sai da ya tafi

A takaice wannan shawara ne da kuma darasi ga mazan da suke da ra'ayin sakin matansu na aure su dawo suna nadama

Allah Ya kiyaye

Daga Datti Assalafy

Jarumi Adam A Zango ya angwance da tsaleliyar amaryarsa Maimuna Musa na Shirin GarwashiWanne fata zakuyi garesu...
17/08/2025

Jarumi Adam A Zango ya angwance da tsaleliyar amaryarsa Maimuna Musa na Shirin Garwashi

Wanne fata zakuyi garesu...

Allah yayi wa mai martaba sarkin Zuru, Maj. Gen. Sani Same rasuwa da safen nan. Allah Ya jikan shi da rahama.Ku sanyashi...
17/08/2025

Allah yayi wa mai martaba sarkin Zuru, Maj. Gen. Sani Same rasuwa da safen nan.

Allah Ya jikan shi da rahama.

Ku sanyashi a addu’o’inku

A Yayin da ake gudanar da Zaben Cike Gurbi a Kano,APC ta Koka inda ta bukaci a soke zaben.Me zaku ce?
16/08/2025

A Yayin da ake gudanar da Zaben Cike Gurbi a Kano,APC ta Koka inda ta bukaci a soke zaben.

Me zaku ce?

Hukumomin tsaro sun samu nasarar k**a manyan shugabannin ƙungiyar ƴan ta'adda ta Ansaru mai alaƙa da Al'Qaeda. Mai ba sh...
16/08/2025

Hukumomin tsaro sun samu nasarar k**a manyan shugabannin ƙungiyar ƴan ta'adda ta Ansaru mai alaƙa da Al'Qaeda.

Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro Malam Nuhu Ribadu ya bayyana cafke Mahmud Muhammad Usman (Abu Barra) da Abubakar Abba (Mahmud Al-Nigeri/Malam Mamuda) a yayin wani taron manema labarai da shugabannin tsaro na ƙasa s**a gabatar.

15/08/2025

Wace sura ce mafi tsawon sura a cikin Al-Qur’ani? Kuma aya nawa take ɗauke da ita?

14/08/2025

A FAIFAN BIDIYO: Rabon Tallafi Nera Dubu Dari ga Mata Dubu biyu da Dari Biyar na Cigaba da Gudana Karamar Hukumar Kontagora ....

Izuwa Yanzun dai Mata 1,302 ne S**a Rabauta da Nera Miliyan Daya da Asirin da Takwas da Dubu Dari Tara,128,900,000 a Yankuna Takwas Dake Karamar Hukumar....

Ga yadda ta kaya a Rana na biyu na Rabon Tallafin.....

゚viralシfypシ゚viralシalシ

DSS Ta K**a Shugaban 'Yan Ta'addan Mamuda Da Ta Ɓalle Daga Boko Haram:Hukumar Tsaron farin kaya ta (DSS) ta yi nasarar k...
13/08/2025

DSS Ta K**a Shugaban 'Yan Ta'addan Mamuda Da Ta Ɓalle Daga Boko Haram:

Hukumar Tsaron farin kaya ta (DSS) ta yi nasarar k**a Abubakar Abba, fitaccen shugaban ƙungiyar ta’addanci ta Mahmuda, a garin Wawa dake Jihar Niger. Rahotanni sun bayyana cewar DSS ta shafe makonni tana bin diddiƙin Abba kafin ta kammala wannan samamen cikin nasara. Nasarar k**a shugaban ƴan ta'addan ya faranta rai ga mazauna jihohin Kwara da Neja waɗanda s**a daɗe cikin tsoro da fargaba sak**akon hare-hare da sace-sacen da kungiyar ke yi.

Gwamnan jihar Neja Mohammed Umaru Bago ya jinjinawa DSS kan yadda ta gudanar da aikin cikin nasara, tare da godewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa jajircewarsa wajen magance matsalar tsaro a jihar.

Abubakar Abba, mai shekaru 33 ɗan asalin garin Daura ne dake Jihar Katsina, wanda ya taba yin sana’ar sayar da kasuss**an wa'azojin malamai, ciki har da na marigayi Mohammed Yusuf, wanda ya kafa kungiyar Boko Haram, kafin daga bisani Abban ya shiga ƙungiyar kuma ya kafa Mahmuda.

Kungiyar Mahmuda, wadda ta ɓalle daga Boko Haram, tana da alaƙa da wasu ƙungiyoyin ta’addanci a Mali da Jamhuriyar Nijar, kuma ta shafe lokaci tana kai hare-hare a yankin gandun daji na Kainji National Park.

K**a Abba na nuna babban nasara wurin rage ƙarfin ƙungiyar, tare da isar da sakon gargaɗi ga sauran ƙungiyoyin ta’addanci a yankin. Gwamna Bago ya jaddada buƙatar ci gaba da tattara bayanan sirri da hadin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro domin tabbatar da zaman lafiya.

~Comrade-Zakari Y Adamu Kontagora ✍️

TALLAFIN MILIYAN 250 GA MATA A KARAMAR HUKUMAR KONTAGORA DAGA GWAMNATIN JIHAR NEJA…Gwamnatin Jihar Neja ta kaddamar da s...
12/08/2025

TALLAFIN MILIYAN 250 GA MATA A KARAMAR HUKUMAR KONTAGORA DAGA GWAMNATIN JIHAR NEJA…

Gwamnatin Jihar Neja ta kaddamar da shirin tallafawa mata a Kontagora da jimillar kuɗi Naira miliyan 250 domin fara kasuwanci, inda kowacce mace za ta samu Naira dubu 100.

An fara rabon tallafin da gundumomi biyar cikin 13 da s**a haɗa da Usalle, Nagwamatse, Masuga, da gundumar Kawo, karkashin jagorancin Haj. Hauwa’u Bako da Ɗan Amanan Bago Hon. Kabiru Shehu Bacci, yayin da ake saran sauran gundumomin za su karɓi nasu gobe Laraba.

Wannan dai na daga cikin alkwarin da mai girma gwamnan jihar Neja Umaru Mohammed Bago yayi tallawa mata masu kananan sana'o'i da jari a garin Kontagora a shekara ɗaya daya gabata.

Hasmag TV.

YANZU-YANZU: A wannan daren Shugaban Kasa Bola Tinubu ya gana da Dan Siyasa Daga jihar Jigawa Hon. Faruk Adamu Aliyu a f...
12/08/2025

YANZU-YANZU: A wannan daren Shugaban Kasa Bola Tinubu ya gana da Dan Siyasa Daga jihar Jigawa Hon. Faruk Adamu Aliyu a fadar shugaban kasa.

Address


Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Hasmag TV. posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

  • Address
  • Alerts
  • Claim ownership or report listing
  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share