01/07/2025
GWANIN BIRGEWA:-Wata ƙaramar yarinya ‘yar shekara 3 ta haddace Hizbi biyu na Al-Qur’ani mai girma, tare da samun matsayi na farko a gasar karatun Al-Qur’ani da makarantar su Miftahu Academy Funtua ta shirya, a matakin Hizbi 2.
Wani abin burgewa, duka iyalinta na cikin masu riko da Al-Qur’ani ne — mahaifinta, mahaifiyarta, kakanta da kakarta, dukkaninsu mahaddata ne.
Lallai wannan babban alfahari ne ga iyali da al'umma.
Allah ya albarkaci rayuwarta da tamu baki ɗaya.
Hoto Daga: Nasir Sulaiman, Funtua