
04/08/2025
KYAUTAR MOTA DAGA HANNUN KWAMISHINA DUTSIN MARI, ZUWAGA KADA ZURU...!!!
Kyautar yanzu ma aka soma farawa, kamar yadda zaku gani, da marancen yau Littanin, 04/08/2025, Mai Girma Kwamishinan kananan hukumomi da Masarautu na jihar Kebbi, HON. ABUBAKAR UMAR DUTSIN MARI (MAJEN GWANDU, SAN TURAKIN KOKO), ya sake Gwangwaje KADA ZURU da sabuwar Mota kirar LE COROLLA, albarkacin soyayyar sa da Mai Girma Gwamnan jihar Kebbi, COMRD DR. NASIR IDRIS (KAURAN GWANDU).
Tabbas, jigo kamar, DUTSIN MARI a jihar Kebbi babu shi, duba da kokari irin nasa, tareda fadi tashin sa, don taimakawa al'umma a ko ina cikin fadin jihar Kebbi, kada a bar ko ina a baya, kana don samun nasarar Gwamnatin KAURA a ko ina cikin sauki a jihar Kebbi.
Muna rokon ALLAH ya kara taimakon Kwamishina DUTSIN MARI tareda kara masa lafiya, domin cigaba da taimakon jama'a, Amin. Gwamnatin KAURAN GWANDU, ALLAH ya kara saka hannun sa a cikin ta, Amin 🙏🙏
✍️✍️Ciroman Koko Media Team
04/08/2025