Jaridar Yaren Gida

  • Home
  • Jaridar Yaren Gida

Jaridar Yaren Gida Jaridar Yaren Gida, Jaridar Al'umma!!
(3)

Ku cigaba da kasancewa damu domin samun ingantattun labarai da rahotanni acikin harshen hausa

Domin tallar hajojinku da yada manufofinku ku tuntube mu ta wannan lambar 08144153244 ta hanyar kiran waya ko whatsApp.

Sabuwar Amaryar Adam A Zango Ta Magantu
17/08/2025

Sabuwar Amaryar Adam A Zango Ta Magantu

MASHA ALLAH: Tsaleliyar Sabuwar Amaryar Jarumi Adam A Zango Maisuna MainunaDaga Real Buroshi Mawaka Sokoto
17/08/2025

MASHA ALLAH: Tsaleliyar Sabuwar Amaryar Jarumi Adam A Zango Maisuna Mainuna

Daga Real Buroshi Mawaka Sokoto

YANZU-YANZU: An Daura Auren Jarumi Adam A Zango Da Maimuna Musa A Safiyar Yau LahadiDaga Real Buroshi Mawaka Sokoto
17/08/2025

YANZU-YANZU: An Daura Auren Jarumi Adam A Zango Da Maimuna Musa A Safiyar Yau Lahadi

Daga Real Buroshi Mawaka Sokoto

Tsohon Shugaban Kasa, Janar Babangida Ya Cika Shekaru 84 A Yau LahadiGa wasu daga cikin ayyukan cigaban da ya kawowa Nij...
17/08/2025

Tsohon Shugaban Kasa, Janar Babangida Ya Cika Shekaru 84 A Yau Lahadi

Ga wasu daga cikin ayyukan cigaban da ya kawowa Nijeriya;

Shi ya kirkiri Jihar Yobe

Shi ya kirkiri Jihar Katsina

Shi ya kirkiri Jihar Taraba

Shi ya kirkiri Jihar Jigawa

Shi ya kirkiri Jihar Kebbi

Shi ya kirkiri Jihar Enugu

Shi ya kirkiri Jihar Edo

Shi ya kirkiri Jihar Delta

Shi ya kirkiri Jihar Osun

Shi ya kirkiri Jihar Akwa Ibom

Shi ya kafa FRSC

Shi ya kafa SSS

Shi ya kafa NIA

Shi ya kafa DIA

Shi ya gina A*o Rock Villa

Shi ya gina Third Mainland Bridge

Ya kammala Shiroro Power Station

Ya gina Toja Bridge Kebbi

Ya ƙirƙiri Jibia Water Plant

Ya gina Challawa Cenga Dam Kano

Hanyar Kano–Abuja dual carriageway

Madatsar ruwa a Kano

Sauran ayyuka sun haɗa da:
1.Hedkwatar ECOWAS Abuja
2.Cibiyar taro ta kasa da kasa Abuja
3.Gidajen FHA a duk faɗin ƙasa
4.Kotunan koli a jihohi
5.Ma’aikatar Tarayya a jihohi 36/Abuja
6.Ofisoshin jam’iyya 2 a jihohi 36
7.Hedkwatar rassa 4 na sojojin ƙasa
8.Barikin sojoji Abuja
9.Makarantar Sojojin Tanki Bauchi
10.Makarantar Sojojin Ruwa Calabar
11.Gidaje ga GOCs 4
12.Navy Dockyard
13.Dockyard Snake Island
14.Gidaje ga ma’aikatan ayyuka da gidaje
15.Gwagwalada/Isheri/Prototype housing
16.Hedkwatar FEPA Abuja
17.Ofisoshin FEPA da lab. Yaba
18.National Eye Centre Kaduna
19.Aluminium Smelter Ikot Abasi
20.Kotun Koli Abuja
21.Ajaokuta Steel Project
22.Filin jirgin sama Abuja Ph1&2
23.Majalisar Tarayya Abuja
24.Fadar Shugaba Abuja
25.Hedkwatar NIA
26.Hedkwatar SSS Abuja
27.Bankin Lamuni FMBN Lagos
28.Rassa FMBN ƙasa baki ɗaya
29.CBN Hqrts Abuja
30.Minting/Security Abuja
31.Jabi District Abuja
32.Central Area Ph1&2
33.A*okoro Area
34.Garki Ph1,2,3
35.Gudu District
36.A*okoro SW Extension1&2
37.Maaikatu jihohi 1991
38.Majalisar dokoki jihohi 1991
39.Shari’a Buildings jihohi 1991
40.Asibitin Maitama Abuja
41.Asibitin Wuse Abuja
42.Asibitin Fadar Shugaba
43.Asibitoci a jihohi
44.Ruwan sha Gusau
45.Ruwan sha A*okoro
46.Ruwan sha Kubwa
47.Ruwan sha Abuja Municipal
48.Ruwan sha Gboko-Yadav
49.Bututun ruwan sha 1004 Housing

Motar Adamawa Express Ta Fāɗa Cikin Kogi A Gadar Namnai, Taraba, Inda Fasinjoji S**a RasùDaga Muhammad Kwairi WaziriWani...
17/08/2025

Motar Adamawa Express Ta Fāɗa Cikin Kogi A Gadar Namnai, Taraba, Inda Fasinjoji S**a Rasù

Daga Muhammad Kwairi Waziri

Wani mummunan lamari ya faru a yau a ƙaramar hukumar Gassol, Jihar Taraba, inda wata motar Adamawa Express ta fāɗa cikin kogi yayin da take ƙoƙarin tsallaka Gadar Namnai.

Gadar, wadda ta karye fiye da shekara guda da ta wuce, har yanzu ba a gyara ta ba duk da alƙawuran da gwamnatocin da s**a gabata na APC da PDP s**a sha yi. Wannan matsala ta ci gaba da zama barazana ga rayuwar al’umma da dukiyoyinsu.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa motar ta rasa daidaito ne sak**akon halin da gadar ke ciki, wanda ya jefa fasinjoji da sauran jama’a cikin firgici da tashin hankali.

Al’umma dai sun soki rashin kulawar gwamnati tare da kira da a gaggauta ɗaukar mataki, don kaucewa sake faruwar irin wannan masifa. Wasu mazauna yankin sun ce gazawar gwamnati wajen gyara gadar ta jawo asarar rayuka da dukiyoyi masu yawa.

A halin yanzu, jama’a na ci gaba da roƙon Allah ya ba su shugabanni nagari masu kishin kasa da jin ƙai ga rayuwar talakawa.

Sarkin Zuru Janar Muhammadu Sani Sami Ya Rasu A Safiyar Yau, Yanada Shekaru 81
17/08/2025

Sarkin Zuru Janar Muhammadu Sani Sami Ya Rasu A Safiyar Yau, Yanada Shekaru 81

DA DUMI-DUMI: Hukumar INEC, ta bayyana Garba Ya'u Gwarmai na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen cike gurbi na...
17/08/2025

DA DUMI-DUMI: Hukumar INEC, ta bayyana Garba Ya'u Gwarmai na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen cike gurbi na mazaɓar Ghari da Tsanyawa a majalisar dokokin jihar Kano.

~ Premier Radio

Matashiya Rukayya Muhammad Tayi Aure
16/08/2025

Matashiya Rukayya Muhammad Tayi Aure

Al'ummar Jihar Sokoto Sun Koka Kan Rashin Kyawon Hanya Daga Gangaren Tashar Illela Zuwa Road BlockWannan hanya ce wacce ...
16/08/2025

Al'ummar Jihar Sokoto Sun Koka Kan Rashin Kyawon Hanya Daga Gangaren Tashar Illela Zuwa Road Block

Wannan hanya ce wacce ta hada kananan hukumomi fiye da 8 hadi da babban birnin jihar Sokoto, wanda mutane suna matukar wahala tareda hasarori da dama na dukiyoyi dama rayuka

Wannan aiki ne da gwamnati mai ci a yanzu ta gada daga tsohuwar gwamnatin Tambuwal, amma babu dalili na wofantar dashi saboda wani abun na daban

Kammala wannan aikin bawai al’ummar wannan yankin ne kawai zai inganta rayuwarsu ba, hatta da ita kanta gwamnatin jiha zai anfanar da ita wurin karuwar samun kudin shiga da dai sauransu

Al’ummar wannan yankin basu chanchanci wannan kuntatawar ba daga gwamnati, kuma kammala wannan aikin cikin lokaci ita gwamnatin ce dai za ta samu yabo daga gare su

Muna fatan kukan mu zai isa a kunnen da ya dace tareda daukar mataki na gyara wannan babbar hanya dama wasu mak**antan su dake ciki da kewayen Sokoto.

Daga: Nura Sulaiman.

DA DUMI-DUMI: Jami'an tsaron farin kaya a jihar Kaduna sun k**a Shehu Aliyu Patangi da tsabar kuɗi kimanin miliyan 30 da...
16/08/2025

DA DUMI-DUMI: Jami'an tsaron farin kaya a jihar Kaduna sun k**a Shehu Aliyu Patangi da tsabar kuɗi kimanin miliyan 30 da niyyar zuwa sayen ƙuri'a yayin zaɓen cike gibi da za'a gudanar yau na ɗan majalisar wakilai mai wakiltar chikun/Kajuru a jihar.

Misalin ƙarfe 3 na daren jiya jami'an s**a damƙe shi a wani sanannen Otel dake cikin garin Kaduna.

Daga Abdulkadir Nafi'u

15/08/2025

YANZU-YANZU: Hukumar shari'a da Malamai ta jihar Kano, ta amince da Naira dubu 20,000 a matsayin mafi karancin Sadaki.

Tsohon Gwamnan Jihar Sokoto Sanata Aminu Tambuwal Yayi Zafafan Martani Ga Gwamnatin Tinubu Wacce Yake Zàrgiñ Tana Masa B...
15/08/2025

Tsohon Gwamnan Jihar Sokoto Sanata Aminu Tambuwal Yayi Zafafan Martani Ga Gwamnatin Tinubu Wacce Yake Zàrgiñ Tana Masa Bita Da Kulli Ba Tareda Sanin Mak**ar Aiki Ba

Inda Ya Bayyana Cewa " Nayi Gwagwarmaya Da Gwamnatin Goodluck Jonathan Da Ta Taba Watsa Min Tiyagas Ba Tareda Na Nuna Alamun Tsoro Ba, Ballantana Gwamnatin Tinubu Da Bai Yiwa 'Yan Kasa Aikin Komai Ba Zanji Tsoron Sa"

Zuwa Yanzu Al'ummar Najeriya Suna Cigaba Da Tofa Albarkacin Bakin Su Gameda Kamun Da Hukumar EFCC Ta Yiwa Aminu Tambuwal

Me zaku ce?

Address


Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Jaridar Yaren Gida posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Jaridar Yaren Gida:

Shortcuts

  • Address
  • Alerts
  • Contact The Business
  • Claim ownership or report listing
  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share