
13/08/2025
KATSINA STATE HISBAH BOARD.
KATSINA DIVISION 2025.
KWAMANDAN HUKUMAR HISBAH NA KARAMAR HUKUMAR KATSINA YA ZIYARCI GARIN JIBIA TARE DA TAWAGAR SA.
A yau Litinin 12 ga watan Augusta shekara ta 2025 Kwamandan hukumar hisbah na karamar hukumar Katsina DC. Malam Shamsu Kabir ya gudanar da ziyara ta musamman tare da tawagar sa a garin jibia.
A inda ya ziyarci ofishin hukumar hisbah ta karamar hukumar jibia, kwamandan ya basu shawarwari tare da kara basu dabarun aiki.
Kwamandan hukumar hisbah na karamar hukumar jibia ya nuna farin cikin sa matuka bisa ziyarar da aka kawo masu.
San nan daga bisani kwamandan ya wuce family House din su, san nan yayi gaisuwar ta'aziyya tare da ziyartar gidan yan uwa da abokan arziki.
PHOTOS:
MO. Abdurrahman Yaradua, IO. Muhammad Sardauna.
REPORTED BY:
Katsina Local Government Hisbah Board ICT Team Sardauna.